← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 71

Sashe 16

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Mahaifin Bilal bawai zargin yake momy tana zina da d'ansa ba, A'a yana zargin tana shirin b'ata masa yaronsa da kud'i,wanda yasan bame d'orewa bane ba,kar yaron ya lalace masa anan gaba, amma duk sanda yakeso ya nsanta alak'ar momy da Bilal se Baba lami tace shid'in d'an bak'in cikine dan kawai yaga yaranta ze samu alkhairi inba haka ba yanda Hajiya ta d'aukesu ai yafi k'arfin wulak'anci dan dole yake hak'ura dan haka yaso yakai yaran boading school amma k'ememe Baba lami ta hana wannan zancen tafiya boading!!!!

*************
   *Bayan shekaru biyu*

lokacin da Bilal ya zana jarabawar waec ya gama tanturancewa wurin biyewa hajiya, har wani girma ya taso masa jikinsa ya k'ara zama na isashen namiji alokacin yake 19yrs, be samu admn ba dan haka haryayi shekaru 21 yana nan Hajiya tana yawon hotels dashi, farinsa ya samu hutu yayi luwai,  fatar nan se shek'i take ya tara suma irin buzu bak'u wuluk se gyarata ake da mayuka, hajiya dashi da iyayensa ta mayar dasu 'yan uwanta, ga motar hawa ga kudad'e a acc, a haka ya samu admtn awani garin daban wanda ya tilastawa Bilal barin momyn sa kamar yanda yake kiranta ita kuwa take ce dashi son.

    Zuwa wannan lokacin Baba Lami tasoma fahimtar cewar tabbas akwai wani mara kyau dake shiga tsakanin uwar gijiyarsu da d'ansu amma son abun duniya ya rufe mata ido harta kasa yim magana, kafin zuwa 'yar shara rayuwar su kuwa masu aiki an kori sunkai goma, dan duk suka gani sesun tsegun tawa uwar Bilal amma seta had'asu da hajiyar sabida son duniya, acikin wanda aka kora d'in akwai biyu da Bilal yayiwa ciki, idan hajiya batanan anan yake holewa abunsa dasu sabida ta sabar masa da kanta, ta gama lalata masa rayuwa gaba d'aya hankalin Bilal inba mata ya gani ba baya kwanciya. Ga kud'i da ake zuzuta Bilal dasu har kawo wannan gangarar kuma suna aikata masha'ar su" Cikin tashin hankali Dr. Sunita ta zare glashin idanta, a hautsine take kallon Bintu kafin tace

"Bintu!! Wannan wane irin rashin imani ne, 17yrs fa kikace, yaro yana 25yrs yanzu good 8yrs kina tatse masa ruwan jikinsa, zina kika koyar dashi, harkinsan yanawa 'yan aiki ciki amma seki koresu akan laifin nasune yaya kike tsammanin iyayen su zasuji, Gaskia Bintu am sorry to say bakida hali me kyau, i cant even imagine irin wannan rayuwar akaina, kai not even in my bad dreams, Allah ya kiyaye mana imaninmu amma wlh tallahi its not too late to repent, kiyi maza kiyi taubatun nasuha!!!!!! Nisawa Bintu tayi kafin tace

"Friend say what ever u want to say, call me with any bad name, yea i deserve it i'm a monster, i'm a bad which a big devil friend!!! Sunita cikin jin zafi tace

"What do you really plan with your life now? Tana sosa kunne tace

"I dunno really, but deep down i know i love Bilal, kuma inaso ne ya aureni, abubuwa sunmun yawa Sunita, inajin tsoron rabuwa da Bilal, inajin tsoron in furta masa kalmar aure ya gujeni, Sunita ina sane da cewar Bilal ya samu duniya ta hannu na yanzu, ya gina katafaren gida, yanada shaguna sunkai bakwai a kasuwa, yana shigo da kayan gini na zamani daga waje Bilal duk wannan abubuwan b'oyemun yake, na tabbatar chance kawai yake nema, wasu lokutan ina kallon k'wayar idansa tsanata sosai nake gani manne a idansa, tabbas Bilal yayi wuya ya isa yanke, banida tabbacin ze yarda ya aureni, sunita inaso na tuba, wlh summa tallahi ina nadamar rayuwa ta, nayi danasanin abubuwa da yawa, kinga ada ban gane yarana ana hanasu zuwa guna ba sabida halin danake ciki da Bilal ashe kowa ya sani ni ina kallon na b'oye, shekaruna biyu ban sanya yaran nan a idoba, hawan jinina befi akan Message da Yarona Bilal yamun ba, yace in dena kiransa dan baze tab'a d'aukar wayana ba, yakuma ce dani ai yaga na samu sabon yaro Bilal muna shek'e ayarmu toya bar masa, bayako nigeria fa, ya akayi ya sani" Shiru sukayi na wuccin gadi dukkansu kafin Sunita tace

"Amma kinsan da wahala yaran nan ya aureki ko? shekarunki kusan 50 fa komafi, shi yana tak'ama da kud'i yanzu mezaiyi dake, bayan ma dayake da kwad'ayi da wanine aida tuni yayi ta kansa ya kwahse iyayensa, kuma bari kiji wlh koki yadda ko kada ki yadda bilal yanada target mummuna akanki, koda bansan ko meyeba amma ki shirya wannan" K'wallan idanta ta share

"Dr. Sunita tunda nake kece mutum ta farko dana fayyacewa cikina, sabida kece hankalina ya kwanta dake akan tabbacin zaki d'aurani a madaidaiciyar hanya, dan Allah ki ceceni, banida nutsuwar zuciya koda bazan samu Bilal ba Allah nakeso ya yafemun" Nisawa Sunita tayi, tasan wannan itace mummunar k'addarar da ake cewa mu nemi Allah tsari da ita ta tsakiyar rayuwa shisa taketa bata tausayi

"Ki fara neman yafiyar Allah, ki nemi Bilal shima ki nusar dashi ku tuba, kada kuma kiyi k'asa a gwiwa wurin sanar dashi k'udirinki" Sauke ajiyar zuciya itama tayi

"Zan gwada yin hakan Dr. nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" Harta mik'e takai k'ofa sunita tace

"Fatima" waigowa tayi amma bata amsa taba tace

"When ever u need a shoulder to cry on, just give me a call, lastly ki aikamun number Bilal na wurinki ba wannan farkan naki ba" Murmushin yak'e tayi dukda kalmar farkan ya daketa sannan ta gyad'a mata kai bata iyayin magana ba tafita tabar office d'in!!!

*****************
Jay abubuwa sun masa yawa akan Mood, bayaso yaron ya koma U.S, kuma yace acen zeje ba UK ba, gabaki d'aya shi bayaso ya masa nisa shishi kad'ai, bakuma yason ya auri macen dabayaso, dazebi shawarar sa daya tsaya sun fahimci juna da yaran, amma wannan tsarine mara kyau ya d'auka, inama ace yanzu haka yana tare da Barra, daya d'ebe takaicin abubuwa da yawa, yana cikin wannan tunani Zulaiha ta shigo d'akin tana wak'a, tasha k'aramin mini skirt da riga iya cibiyarta, kannan cike da attachment tasha makeup tamkar wacce zataje partyn dare, zama tayi kusa dashi tace tana kallon sa

"Jay abincinka yana dining yana jiranka"kallonta yayi yana murmushi yace

"To muje mana" Tab'e baki tayi

"Naci nawa kaje kaci naka kawai" Ba musu ya mik'e yaje yayi serving kanshi ya zauna yanacin abincin, ba laifin tuwon garine da miyar egusi yau ansamu kanta, seda ya k'oshi sosai sannan ya mik'e yaje ya wanko bakinsa yayi wanka sannan yayi shirin kwanciya, Zulaiha se rawar kai akeyi ansha kayan mata fin na dubu hamsin, ansha tsumi, ansha tabaje, ansha gumbar sosa gaye, ansha gumbar ungo kama, ansha ruwan wanke ango ba uban tsiyar da ba'a shaba. Lokacin da Jay ya kula matarsa tana buk'atar sa itama seya kalleta yana murmushi yace

"Zulaiha kinsha kyau, matso maza in baki tukwicin wannan wankan" Kamar an jeho sandar sunuka haka ta tashi ta matso bawani kwarkwasa kamar an ajiye masa icce" Kallonta yayi ya hasaso yanda Barra take masa karairaya ji wannan to meye haka? had'iyar yawu yayi sabida yanason matarsa, shine da kansa ya zab'o abarsa ya auro bayan Barra, fuskarta ya kamo ya manna mata kiss a lips nata sannan yace

"Yau wace tsarabar zan samu ne ehn my baby" Murmushi tayi aladole ita me kyau da diri

"Me kakeso" Ta fad'a a tsatsaye, yana shinshinar jikinta yace

"Haba mana baby, kina magana cen bazaki matso kusa dani ba ehn" Wani juyar dakai tayi gefe batace komai ba, duk yanda yake tab'a jikinta tana nan tak'i tayashi se basarwa take gani take tamkar jay baze rayu ba idan babu ita sabida yanda yake nunar mata so da k'auna, haka Jay ya k'araci kid'ansa da rawarsa amma sam kwata kwata bata tayashi komai ba dan haka babu wata cikakkiyar gamsuwa sabida yanayin ta, duk yanda yaso ya nuna jin dad'in sa haka ya kasa sukayi shiru bayan komai ya lafa"

*Note:*
*Wasu acikin mu zasuyita cewa basason hiran gidan Jay, waye waye, to haka zakubi labarin haka yake akwai alk'awarin wayar wa mata da kai akan matsalolin dasuke fuskanta na aure, nan gaba kad'an zaku fahimci dalili yawan sako maganar Jay da ahalinsa acikin labarin nan, inshaa Allahu duk zamu amfana, dukda yake na sanar daku zamuyita cin karo da maganganu masu nauyi a tafiyar nagode*

*******************
Haka aka shirya Hafsat aka kaita fadar sarauni wurin bahar, inda aka shaida mata acen zata zauna, lafiya lau ta kwana d'aya washe gari tunda asuba Bahar ta tasheta tayi sallan asuba, seta sanya bayi suka wadata gaban yarin yar da abun kari iri iri. Anan tashiga ciki domin shiryawa Kamar an juyar dakan ta sekuma ta soma wasa da abincin irin yanda yara sukeyi, atake ta b'ata wurin ta masa kaca kaca, sagaga Bahar ta sake baki sanda tafito kafin ta kama salati

"Na shiga uku ni Salamatu, yanzu yarinyar nan dan la'ancewa akanki ta fara zaki zauna ki b'atamun wuri haka da girmanki da komai, iskancin da ke nan wannan ai, aikuwa wlh sekin gyara, ba hadimar dazata gyara wurin nan dan babu tambad'adden daze d'auki wannan sakarcin tundasu ba la'anannu bane ba" Kallonta Hafsat tayi yanda taga tanata fad'a seta tsorata irin na yara nan danan seta soma kuka kamar wacce aka daka, cikin mamaki Bahar tace

"Yau naga la'ananniyar yarinyar, ni zaki nunawa tambad'ewa, sangarta, sangarta ya'i, Allah ni zaneki zanyi" Mik'ewa Hafsat tayi ta soma bubbuga k'afa daga baya kawai seta shige cikin jikin Bahar tana kuka" Zareta takeyi ita kuwa se manne mata takeyi, ajiki suka soma zagaye a haka

"Yau nashiga uku ankawomun mayya, ke da hankalinki kuwa, kajimun la'ananniyar yarinya, b'alla ni zakiyi" Cikin wannan halin Mood ya shigo, tsayawa yayi yana kallonsu, gaba d'aya ya shagala da yanayin yarinyar, ita kuwa idanta yana sauka akanshi tace dawa Allah ya had'ata bada shiba, nan take ta rugo ta k'ank'ameshi tace

"Yauwa kaga kaka tanamun fad'a ko, ban mata komai ba" zareta yake k'ok'arin yi ajikinsa amma k'ememe tak'i ta sakeshi, nan Bahar tahau salallami
Chapter 16 · 0% Book details