Sashe 49
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lokacin danaje gidan sarautar Daulatul dinar sena tsinci kaina a wani hali na rashin galihu,amma acikin k'ank'anin lokaci sena fahimci akwai wata kitimurmurar da ake shiryarwa wad'an su en na gada acikin gidan, bayan kwana biyu aka so ayi amfani dani se Allah ya hana ya kuma kare, daganan se aka auramun babban dan sarkin daular, zamana dashi da kakarsa sena fahimci akwai wata matsala, acikin fadar akwai wata b'oyayyiyar k'ungiya me zaman kanta wacce sukeda mummunar manufa akan son k'wace sarautar, daganan sena duk'ufa nida kakarsa akan son neman su waye jagorori acikin wannan tafiyar, nayita lalube acikin duhu, nasha fama na shiga had'arurruka da dama kafin Allah ya bani sa'ar sanin su waye suke neman ran sarki da d'ansa d'a d'aya tilo, daganan sesuka d'auki matakin gaggawa na aikawa a kashe sarki da kuma d'ansa su huta, se sukayi rashin sa'a sarki da d'an nasa basu rigada sun mutuba, nima kuma akayi akayi a kasheni kwanana basu k'areba se kawai suka d'auki matakin rataya laifin akaina ta hanyar kawo shedun k'arya" kallon juna suke suna wani murmushi atare kawar da kanta tayi sannan taci gaba
"Raina fansa ne akan ubana dankuwa Me martaba ya 'yantani a matsayin 'yarsa tuni, Raina fansa ne akan mijina dan kuwa yasha matuk'ar wahala arayuwata kuma shine ya d'akko ni a lokacin da ake neman yagan rigar mutunci yamun sutura, idan na mutu agarin ceton sa ban damu ba, ka k'addara nid'ince na sanya akashe su, amma kuma tare da had'in bakin wasu acikin fadar nan, wannan shine Assighment dazan baka matsayin ka na babban me bincike alaji Data" Gyaran murya yayi har lokacin yana murmushi kafin yace
"Ban fahimci wanne Assighnment ba aduk wannan labarin da kika bani a baud'e" Murmushi tayi kafin tace
"Ka nemo su waye makasan sarki da d'ansa acikin fada bayan ni" Nisawa yayi kafin yace
"Idan ina binciken mutum akan kowane irin laifi ina duba zuciyar sane lolacin dayake magana, bana duba kalamansa, amma narasa yanda akayi kika raba zuciyata kashi biyu a wannan lokacin, na farko kalamanki suka d'auki mafi rinjayen kaso a k'walwata da zuciyata, na biyu kuma harbawar zuciyar ki ya tabbatar mun da cewar keme gaskiya ce hakane?" Murmushi tayi
"Ehm Ehm banda azarb'ab'i bance dakai inada gaskia ba, nadai gaya maka hanya mafi b'ullewa ne amaimakon ka b'ata lokacinka wurin jiran in baka wata amsa danni babu amsar dazaka samu daga gareni a wannan lokacin" Shiru yayi yana nazarin yarinyar be tab'a had'uwa da mutum mara tsoro irinta ba, meke damun kanta haka?
"Idanda zaki bani had'in kai, da munyi wannan tafiyar atare Malama Hafsa, banaso muyita zagaye nida ke, na soma fahimtar kalaman ki dakuma gaskiyar ki" batace masa komai ba yace yana kallonta har lokacin
"Idan zaki bini zan dawo anjima na d'aukeki samuje gidana inada mata hadda yara biyu so karkiyi wani tunanin,akwai muhimman abubuwan danakeso mu tattauna a tare masu buk'atar sirri" Shiru har lokacin batace masa komai ba, seda kusan mintuna uku suka wuce sannan ta sauke nannauyar ajiyan zuciya tace
"Banaso fitana atare dakai ya samu saukar idon polisawan wannan wurin, ka sani idon fada akwaisu a ko'ina na tabbatar anan d'inma akwai mutanen su dan komai zan bikane amma zuciyata batada nutsuwa akan bazaka cutar dani ba sam! Murmushi yayi sannan yace
"Kinada tsananin kaifin basira da k'wazo wannan shine abinda ya ankarar dani akan gaskiyar ki, ya kuma kwad'aitamun son yin tafiya atare dake, idan haka kike tunani zan murd'e kalamai na daga yanzu zuwa yin basaja na wuccin gadi kafin mu samu gaskiyar ke wacece! Murmushi tayi dankuwa tsaf ta gane kalaman sa kafin tace
"Abin ze amfanar da mutane da yawa Detective, kawai inasone ka sani kaima ka shigo wani hannun dayake a rub'e bashida sanayya kota ina tashin wari yake abinsa ka kiyaye" Cikin gano zancen ta yace
"Hakane zan tafi amma ki sani bazan tab'a saurara miki ba idan har ya tabbatar cewar ke mai laifice, dan kuwa kin kasa kawo wasu k'wararan hujjojin dazasu nuna cewar bakida hannu a wannan tafiyar, detective ze baud'e hannunsa yakaiki d'akin horon dayake mallakin humumar su ya azabtar dake cikin k'una" Murmushi tayi
"Ina fatan wannan basajan ya zame maka alkahiri, ina maka tsoro kayi sakacin da santsin miyan yauk'i ze jaka zuwaga gangara" Mik'ewa yayi
"Gwara ki tanadi hujjojin kariya dakai, dan kuwa daga yanxu bazanmiki yare irin wannan ba, had'aki zanyi da horo mafi muni, sarki da d'ansa rayuwar suce a tsakiya"
"Gaba d'aya Allah yana bayana yana dafamun a irin lokutan danake tsananin buk'atar hakan, nayi farin ciki danayi nasarar gano amsa kuwwar d'an mage, ban tab'a sani inada hikimar gano wannan hanyar ba, zan jirayeka zuwa duhuwar ina maka fatan samun nasara" Seda yakai k'ofa sannan yace
"Daga yanzu babu wata magana me kamada dad'i a tsakanina dake, idan baud'e yayi baud'e zaki iya samun tsaraba harta duka kisan wannan, bayaga haka kiyi hankali wurin gayamun magana dan kuwa daga wannan lokacin mun gama tausasa kalamai se saukar horo me tsanani" Bata bashi amsaba ta fahimci da haka yakeso ya rabata da wurin tana fatan police biyu dake tsaye basu fahimci komai ba, dan bata yadda da kowa ba a yanxu!
************
Ranka ya dad'e hak'uri zakayi ka kwanta zuwa lokacin dazaka samu lafiya, kayi hak'uri ko zuwa jibi ne" kallon mitumin yayi a k'ufule ya saba darashin yin magana har yanzu bakinsa nauyin bud'ewa yake masa, idan ba ambaton Allah yake ba seya wuni beyi magana ba
"Yaya zasu mata sharri, akan zasu sauke akan ta, meta musu k'arya sukeyi kuma inaso inga matata yanzu yanzu" Nisawa Uncle Jay yayi kafin yace
"Hammood kokasan ba inda zan barka kaje, kana hauka ne wai, su hukumar aiba mahaukata bane ba dazasu yanke mata hukunci babu wani bincike" kallon mamaki yayiwa Uncle Jay
"Uncle ban gane me kake nufi ba, so kake in barsu suyita dukanta, kokuma so kake sauro da k'udan cizo yayita cizonta, agun kwanciya ake kashi ayi fitsari gaskia zuwa zanyi in dawo da ita" Khairiyya da kishi ke shirin hallakawa tayi gajeran tsaki sannan tace a k'ufule
"Yarinya tana neman ranka, kai kana neman ka ceceta, gaskia Hammood kanada matsala, i will make sure she rot in jail" d'aga ido yayi daga kwancen dayake yace
"Kidena alak'anta hafsat da maganar nan, batada wani alak'a da ita kuma ita ba muguwa bace ba, zargi ne aka jefa a zukatan ku akanta kuma kada ku bari ayi nasara akan hakan" Wani tsakin taja
"Ko shakka banayi asiri ta maka, an jik'a an baka kasha, kasan me kake ciki kuma fita ba inda zakaje da wannan raunin" Mik'eea yayi zaune yana k'walla k'ara yana dafe wurin kafin yace
"Khairiyya idan bazaki fad'a alkhairi ba to kiyi shiru dan Allah, babu i repeat babu wani wanda ya isa a duk fad'in duniyar nan ya hanani fita idan ba Allah ba, yanzu zanje i want to bail her out" zata k'ara magana Uncle Jay yace
"Khairii please, ki rabu dashu, Hammood tunda yamun musu abin yafi k'arfin sa, just let him go" Tashi zaune yayi da ssuri Ummin sa ta rik'esa tana kallon sa, shi d'inma kallonta yayi
"Ummi dan Allah karki hanani, yarinyar nan nini kad'ai nasan abinda nakeji akan halin nan datake ciki, tayi mana sadaukarwa bazan tab'a bari ta shiga wani hali ba akan rashin gaskiya! Zama ta koma tayi sannan da ido tayiwa Uncle Jay alama akan yace masa wani abu
"Ka bamu mintuna goma mu nemo wanda zasu baka tsoro" Tashi yayi tsaye kafin yace
"Abinda banaso kenan, hankali ze dawo akaina, da abun hawa na kasuwa ma zan fita" Damuwa sosai ta bayyana a fuskar ummi ta sadda kanta a k'asa cikin son b'oye damuwar ta, seda yakai k'ofa sannan ya waigo ya kalli mahaifiyarsa
"Ummi kimun addu'a" Murmushi ta sakar masa wanda bekai zuci ba sannan ta gyad'a masa kai" Dawowa yayi ya karb'i kud'i hannun Uncle Jay sannan yabar cikin d'akin da tunani kala kala aranshi.
***************
Koda ya iso station d'in ya tarar da motar Baba Usman da wasu muk'araban sa, fasa shiga ciki yayi ganin akwai yalwar duhu awurin seya lab'e agefen bishiyar da Baba usman yayi parking, yana nan tsaye har aka shafe minti sama da goma sannan segasu sun fito, tsayawa sukayi suda D.P.O. Baba usman ya mik'a masa kud'i ya karb'a sannan yace yana kallon sa
"D.P.O banaso abaiwa yarinyar nan dama ko k'afar dazatayi wani bayani, idanda daganan station d'in zaku turata jail batare da alkhali yabita kanta ba danaji dad'i, amma ko yanzu idan alk'alin naku ne semu siyeshi mu siye lauyeyun su murd'eta, kasani idan asirina ya tonu naka asirin ma ya gama tonuwa" DPO yana 'yar dariya yace
"Ai ka rabu dani da ita kawai, narasa waye ya turo Detective Data akan binciken ta, mutumin dayayi yak'i da mutanen harma da aljanun gidan madubi, dabadan shiba da duni zansan yanda zanyi kawai na hanata xuwa gun shari'a, abin ma dayazo da sauki tunda kace batada galihu batada kowa" Baba usman yana dariya yace
"Ance ba'a siyen Detective data da kud'i, idan nabi ta kansa da nera ya taka ya wuce zan sace matar sa, ko 'yar sa inyanada su inga ta tsiya" Dariyar mugunta DPO yayi kafin yace
"Ranka ya dad'e inama ace nice nakeda irin tunanin ka, dana mori ilimina" Dariya jin dad'i yae kafin yace
"Mu zamu koma, ka tuntub'i detective d'in kaji idan yayi musu zamu karb'e case d'in daga hannun sa" Sallama sukawa juna sannan suka wuce shiya koma, sauke ajiyar zuciya Hammood danya samu wata shaidar akan Baba Usman yayi recording na komai a wayarsa, kai tsaye cikin station d'in yashiga bayan sun gaisa dashi yace
"Office na DP0 nake nema" kallon sosai sukayi masa kafin d'aya daga cikinsu yace malam lafiya?
"Sunana prince hammood daga masarautar Daulatul Dinar" Take suka fara kai masa gaisuwa, yamutsa fuska yayi sabida yanda wurin bullet d'in ke masa ciwo sosai yace yana kallon d'aya daga ciki
"Lead the way" da azama ya shiga gaba shikuwa yabi bayan sa. Bayan sun gaisa yace yana kallon D.P.O