← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 71

Sashe 56

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Asalina ni cikakkiyar bahaushiya ce wacce tarihin jinin rawani yake zagaye dani a k'ark'ashin masarautar Bauran dawa dake mulki b'angaren yankin Baura a wajejen saharar bahaushe dake yankin nan, gaba d'aya ni tuwo ce me lillib'e da miya datasha manshanu wanda aka dafa aka soya da zallan albasa tare da watsa kanwa acikinsa don kashe tsaminsa, domin kuwa iyaye da kakannina a sarauta muka tashi, tun kafin mulki ya zama wata tsiya ahalina suke mulki a k'asar hausa, a yanda tarihi yazo  kakan kakanmu yana daga cikin wanda suka taya shehu yad'a addinin islama a sanda yazo mana dashi.
   Mahaifina yanada 'ya'ya maza guda hud'u seni mace jal da Allah ya bashi wanda kuma duk a cikin matayen sa mahfiyata kad'ai ce da wannan jerin se kuwa kuyanga d'aya data haifi mace itama aka 'yanta ta ta zama me fad'a aji dalilin haihuwar ta, na taso abar so awurin mahaifina ya sanya mun suna Salama tu sabida shine suna awurin uwar haihuwar sa, ya nunan gata sabida nice sanyin idaniyar sa a wannan lokacin, yayinda sarakuna suke tsananin son ganin sun samu magaji se Allah ya jarabi mahaifina da son samun magajiya acewar sa mata rahama ne. Seda nayi shekaru hud'u a duniyar mu sannan aka haifi k'anwata Maryama, a lokacin senayi tsaikon samun mijin aure sabida mahaifina yace baze barni in auri kowane b'eran dawa mara gata ba, haka wata rana bazan manta ba yak'i  ya b'arke atsakanin masarautar mu da yankin arewan daular wannan masarautar danake ciki alokacin inada shekaru sha uku a duniya, haka akazo se akayi rashin sa'a yankinmu sunata fad'uwa ana kashe mana sojojin yak'inmu, dan haka se mahaifina ya nemi sulhu a maimakon ci gaba da zubda jini, a zaman sulhu ne Allah ya kad'oni shaidawa me martaba mahaifiyata tana kakarin mutuwa dan muna tsammanin guba taci, duk yanda akaso a ceto ranta inaa magauta sunyi nasara akanta sun bata guba taci dama tare da sarki takeci takesha, to wannan sha'anin yak'in ya sanya dole takeci ita kad'ai se sukayi amfani da wannan damar suka kashemun uwata abar sona, anan ne d'an sarkin Daular nan na wancen lokacin yace shisam aduniya bega matar aure ba saini, dan haka ana ihun mutuwar uwata suka nemi a aura masa ni kosu tashi yankin mu, mahaifina yana cikin bak'in cikin rashin mata mafi soyuwa agareshi segashi kuma anaso a rabashi da 'yarsa dayafiso ta K'arfin tuwo kuma a irin lokacin dayake cikin d'acin rai! Badan yaso ba ya zab'i zaman lafiyar yankinsa akan soyayyar 'yarsa da farin cikin sa dana 'yarsa wato ni Salamatu. Zuwan da akayi dani wannan Daular sena fahimci a yankina mun gaji mulkine amma tsagwaran mulki ga inda akeyin sa nan. Gaba d'aya komai se ammaka sannan duk inda ka juya hararace, ina zuwa sirikata tashi masifa akan lallai se an aurawa Marwan 'yar k'anwarta dake masarautar Jijiga kamar yanda tun farko aka tsara, dan haka inaji ina gani akamun kishiya da wuri, Marwan yana matuk'ar sona tun bana sakin jikina dashi harnima nazo na cire d'ard'ar muke matuk'ar son junan mu, b'angaren Jaruma kuwa kamar takasheni dan kishi, ban damu ba sirikata bata sona amma se Allah be mata tsawon rai ba dan haka na samu sassaucin azaba nakeji dana Jaruma kawai har Marwan yazo ya karb'i sarautar garin nan wannan itace tushiyar komai!!!

   Bazan iya baki labarin daya gabaci wannan ba dankuwa semu shekara anan bamu tashi ba amma a tak'aice abinda ya faru shine, k'anin sarki wato Baban  sarki Marwan shine ya k'wace sarautar a hannun Marwan bayan Marwan yayi shekaru goma sha shida akan k'arakar mulki, wani yak'i da akayi akacimu da yak'i seyace baze iyaba yana mayarda masarauta baya ya karb'e mulkin, da wannan semuka koma baya akan komai na gidan nan har yanayin isarmu muka dawo wasu al'amarin k'ashin baya ba'a sakawa damu ba'a fitarwa damu agidan nan. Tafiya tayi tafiya akazo yaranmu suka tasa suka girma, wancen sarkin ya fad'i ya mutu, dama kinsan idan aka cire sarki a mulki barin k'asa yake gaba d'aya wannan ya sanya mu bama k'asar se aka gayyacemu akan mu dawo a mayar da Marwan akan mulkin sa hakan yasa muna murna Allah ya karb'i addu'armu muka dawo kwanan mu biyu aka mayardashi anan mukaci gaba dajin dad'in mu, har akazo rana d'aya aka kashe marwan acikin fada da ranar Allah munaji muna gani yaron wancen Baban na marwan daya mutu ya dab'a mar wuk'a kuma ya d'are mulkin, babu wanda ya isa yayi magana dan haka dole akayi shiru badan rai yaso ba, muna nan yaranmu suka girma suka kai abun isa, shi wannan azzalumin sarki seya kwanta ciwo toshima alokacin yashiga tsoron shiga hannun Allah da wannan seya nemi mahaifinku shine babban yarona ya d'aurashi akan wannan mulkin amaimakon shi nashi yaron wato Usman, kuma kafin yaji sauki seyace ga garinku ya fad'i ya mutu wannan shine dalilin shigar wannan masarautar ta zubda jini.

A gefen kwarkwarar mahaifiyarta kuwa 'yarta wato k'anwata tayi aure a wani k'auye dake kusa da yankinmu harta hayayyafa, da wannan k'wark'warar mahaifiyar tamu bata samu nutsuwa ba seda ta d'aura 'yarta akan mugun nufi, nifa Allah ne shaidana harna manta dasu amma me segashi gaba d'aya an turo 'yar k'anwar nan tawa a zuwan sirikata aka nunawa duniya nace banason 'yar k'anwata ta auri yarona, badan nasoba na hak'ura sabida nasan wacece uwarta Maryama, agaba aka tasani ba seda suka tabbatar auren nan an d'aura shi! Tun zuwan ta a duniyar mu banda sharri babu abinda take k'ullawa, lokacin dana kula gaba d'aya hankalin Tahir baya jikinsa sabida bayason Bilkisu sena nemar masa auren Surbajo wata 'yar fulani wacce take 'yar sarkin wani rugar fulani me fad'i a wani k'auye ya aurah, lokaci d'aya kansu ya had'u suke matuk'ar son junan su. Zuwan Surbajo da befi shekara ba ta haifi d'anta Namiji kyakyawa son kowa k'in wanda ya rasa, wannan haihuwar sa seta tashi hankalin Bilkisu itada bata tab'a haihuwa ba, nan danan ta shiga rud'ani, tayita k'unci hadda kwanciya ciwo, yaro yaci sunan kakansa Marwan daganan seda ya shekara biyu uwarsa bata k'ara haihuwa ba, Tahir yanason Marwan sosai yana ce dashi yarima sabida sunan me martaba me rasuwa dayaci rana, dan haka koda Surbajo ta sake haihuwar Namiji se yake tsokanar da bayan tukunya me bak'in jini bameyi dakai, haka yara suka tasa har zuwa sanda babban yayi shekaru 6 k'aramin yanada hud'u, daga nan kuma daga surbajo har maryama kowa haihuwa shiru.
Chapter 56 · 0% Book details