← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 71

Sashe 28

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma koninan yau Hafsatu ta kalla ta kirana Amina aisaina wanka mata mari, wannan ai iskanci ne Ranki ya dad'e, maganar gaskia ta cancanci horo me tsanani" K'ara b'ata fuska khairiyya tayi

"Duk yanda zanyi sena tabbatar tabar k'asar nan zuwa Nigeria i hate seing her face, idiot! nan suka zauna sukayita zigata harta hau daram ta d'are akai tayi kane kane.

kallon Amina Barari tayi cikin mamaki tace "Ke bala'i ce Meena, yanaji gaba d'aya kin sauya labarin, mesa bazaki gaya mata gaskiyar matsayin Hafsat a wurin mijinta ba? Harara ta wurgawa Barira

"Ea tabbas Barira na yarda gulma kad'ai kika k'ware ayi amma sam bakida hankali, kin manta gargad'in Bahar akan b'oye matsayin Hafsat awurin Prince? sannan ai bazamu zira kanmu a ko inaba se inda mukaga zata b'ulle, wannan fa 'yar sarki ce muna k'in gaya mata komai zakiga ta tsanemu, wata k'ilma tayi sanadin da za'a mayar damu Nigeria mu shiga uku,Allah na tuba banda k'udirar Allah ko filin jirgi kyaje?" Dariya suka saka atare sannan Barira tace

"Bari bari, ni wlh makaranta nakeso nakoma, baka mutu a bauta ba" Tsaki taja

"Nifa kurma nake hari, kindai san ba wacce tafini kyau a matansa ko" Tab'e baki Barira tayi "Ba mamaki ta faru, abun Allah budurwa da jika".......

A garden suka had'u da Hafsat wacce sam ta kasa gayawa Bahar abinda ya faru, tunani take sosai akan irin rayuwar data fuskanta tun daga tasowarta har kawo wannan lokacin, agidan momy akwai 'yanci babu takura ba komai, a matsayin 'yar rik'o ta d'auketa wannan ya bata lasisin zama da momy tamkar itace uwarta,momy batada wata matsala amma matsala d'aya agidan momy itace Bilal, ta rasa dalilin daya sanya ta kasa cire momy a ranta har gobe tana mata kallon uwa, meyasa momy ta zab'i rayuwar sab'on Allah akan tagode masa bisa dukkan ni'imomin sa akanta ? tanajin ciwo, tanajin zafi idanda a Nigeria take a halin yanzu babu abinda ze hana ta ziyarci momy ta mata nasiha koda zata kashe ta kuwa? b'angaren zuciyarta kuma yana mata yawo akan tsananin kamanceceniyar Khairiyya da momy, kai bama wannan tanbas a duk inda tasan khairiyya ta santa kamar gidan momy? amma wannan ai 'yar sarkin Baiha ce momy kuwa ta tab'a gaya mata ita mutuniyar sudan ce amma kamar fa ? tabbacin cewar tasan khairiyya ya tsaya a ranta amma a ina ? shine tambayar datake addabar ta amma babu amsa sam! A gabanta khairiyya ta tsaya suka tsaya wurgawa juna kallo cikin isa tace

"Ke baki ita gaisuwa bane ba, waye ubanki tsintacciyar mage? da har ina tsaye zaki zauna" Hafsat waige tashiga yi kamar tana nemann wani abu kafin ta sake kallon khairiyya "Wai dani kike? ta furta tana kallon ta ido cikin ido, cikin takaici khairiyya ta kawar da kanta

"Banngane ba? ni kike kallo kike gayamun dawa nake, dankin samu d'aurin gindi a awurin stohuwar danake da tabbacin takusa kutuwa shine kike d'add'aga ta mutu abarni dake inci uwarki" Yamutsa fuska Hafsa tayi dukda a kumbure take sabisa buguwa gashan mari amma zaka gano kyakyawace ajin farko tace

"Anya kuwa bamu kuskureki da 'yar gidan sarkin Baiha ba ? kodai ba'a gabansa aka raineki ba, koni dana sako k'afa gidan sarauta jiya nasa cewa ba haka mutuncin sarauta yake furta kalamai ba, kamar yar hanyar kawo, U doesnt have a language at all, ur using thug language and that, is not a language, know how and when to talk to me ok" Kallon mamaki khairiyya ta mata tana k'ara mamakin wai 'yar tsintuwa ce kuma yar aiki ce! kafin ta gama tunanin hafsat ta mik'e "Excuse me please" Tana juyawa khairii ta rik'o rigarta tayi dragging nata gabanta

"Are you by anychance taking me for granted? D'age gira d'aya Hafsat tayi

"Take ur hand's off me, as u can see am not in the mood to tolerate ur bullsh***t" Cikin d'aga murya khairiyya tace

"Amma kin iya rik'e rigar mijina ko? tambad'add'iya i can see u really wnt to seduce him" Wata dariya siriri Hafsat tayi sannan ta kallo ta sama da k'asa

"He suppose to be mine first babe, i just let u have him first sabida ni sam baya gabana, after all we r sharing thesame surename with him, ke kikeda lokacin wannan shirmen kuma" Kwad'a mata mari khairii tayi

"Me kike nufi da kalaman ki? Dafe kunci Hafsat tayi cikin mamaki sekace tana jiranta, hawaye ya sakko daga fuskarta tace "Ask ur damn Ass!! sannan ta juya da gudu dafe da kuncin ta, Khairii zuciyarta yana tafasa ta juya zuwa part d'in su tana nanata kalaman Hafsat aranta "He suppose to be mine first beb, i just let u have him first!! what those that mean for goodness sake? is she up to sokething kome? Hafsat da gudu ta wuce cikin gida,tararwa tayi Bahar bata wurin ya sanya ta wuce d'akinta aguje, kan gado ta fad'a ta soma kuka me ban tausayi, me tayiwa mutumin nan yakeso yaga bayanta ne? bata cewa kowa ya mata fyd'e ba yanda ya tsinci maganar nan haka ita ta tsinta me yakeso tayi? wannan tsanar da tushe ta faro babu wata maganar akan abinda ya faru ne, shine yakeso ya cutar da ita, tayi alk'awarin bazata tab'a aurar Hammood ba, amma su zuba itada matar sa seta dasa mata hawan jini sannan tabar mijin, shi kuwa wlh tayi alk'awarin indai har ta amsa sunanta mace seya zube gwiwowinsa a k'asa, ya tuke gemunsa ya dire rawanin sa yana rokon gafarta, a lokacin zata nuna masa iyakar sa wlh, zatayi amfani da sirrin sa data sani ta juya shi son ranta.

Acikin ambaliyan ruwan turaruka Khairii tayi wanka, har yanzu raunukan jikinta da saura dukda ba ciwo ciwon, ta saka abin daya faru aranta har bata sukuni, ita sedaga baya tayi danasanin faruwar komai, upon all people kuma ace Kurma ne ya taimaketa haryasan sirrin ta, momynta batasan illan datayi wa rayuwar taba har wannan lokacin, ko bacci ta kwanta video batsar mahaifiyarta ne yake mata yawo akai, a hankali take murza man ajikinta tafi 40mns da fitowa daga wankan amma she's lost, batamasan tana eban man tanata laftawa jikinta ba, shikuwa yayi tsaye daga jikin k'ofa yana k'are mata kallo sanye take da bathrobe ta d'aure kanta da towel fari kalan bathrobe d'inta, ganin gaba d'aya bata tare da kanta ya sanya ya taka har kusa da ita ya xauna ya rik'o hannun ta suka kalli juna, yana murmushi ya girgiza mata kai" Kallon sa tayi sannan itama ta k'ak'alo murmushin k'arfin hali

"Sannu da zuwa, yaushe ka shigo? kawar da kansa yae gefe sannan ya zaro wayarsa ya rubuta mata

"Meke damunki khairii?" karantawa tayi wani k'ululun bak'in ciki ya kuma tarnak'eta, tace tana kallon sa

"Bazan juri cewar duk sanda zanyi magana dakai ba sedai ka rubuta na karanta, sekace wasu tab'abb'u irin haka aiseka kurumtani nima" Da mamaki ya kalleta, seyayi mata alamar tayi hak'uri da hannunsa sannan ya mik'e ze fita, hannun sa ta rik'o ya dakata amma be waigoba tace cikin sanyi murya

"Baka zama gida bare ka koyar dani yanda kakeyi da Bahar, nikuma zanfison kamun da hannu sena mayar maka da bakina ko, naga kaji haushi maganar ne ban daidaita ba amma ba haka nake nufi ba" Sauke ajiyar zuciya yayi cikin jin dad'in abinda tace sannan ya juyo ya rungumeta gaba d'aya, k'amshin jikinsa ya kusa sumar da ita, gaba d'aya ya mata rumfa acikin faffad'an k'irjin sa, saitin kunnenta yakai bakinsa ya manna mata kiss sannan ya shafi gefen kuma tunta, saketa yayi sannnan da hannu ya nuna mata "Zan koya miki" kallon sa tayi bata gane ba ya rubuta mata yana nuna mata tayi murmushi.

Babban gidane suke acikin sa, b'angaren su shine agaba, se part biyu dasuke baya iri d'aya, part d'in farko na dama shine na Bahar se part na biyu shine na Bayi da kuyangin da akazo dasu gabaki d'aya Bahar ita kad'aice a part d'inta se kuwa Hafsat da wasu susu biyu masu kula dasu, Bahar zaune tana mitar an baro mata miyan kukanta a gida Hafsat se hak'uri take bata wata baiwa tazo tace wai inji khairiyya Hafsat taje, kallon masifa Bahar tayiwa Baiwar

"Ilele kike ko? baiwar ta k'ara k'ask'antar da kanta  "Nice Bahar sarauni" k'wafa tayi

"Me zata mata ne ? la'ana take nema kome? yarinyar nan yanzu take zaunawa tun safe na kula tunda mukazo take yawan aikowa kiranta ke Hafsat aikin me zaki mata ne? Kallon Baiwar Hafsat tayi ssannan tace

"Ba komai Ammu, hira nake tayata" Tsaki taja

"Banta gantalewa tarasa me mata hira seke? ina daga masarautar su an bata kuyanga? Mik'ewa Hafsat tayi

"Nidai Ammu dan Allah ki rage yawan fad'a, cewa akace yana saka hawan jini, idan kika kamu da ciwon hawan jini aina shiga uku ko? duka ta kaimata

"Ke tafi cen danla me neman rigimar tsiya" Tana dariya ta fito zuwa part d'in da sallama ta shiga a parlor ta samesu zaune suna kallo d'an russunawa tayi tace

"Yaa prince barka da yamma" Beko kalleta ba, tace tana kallon khairiyya "Sannu khairiyya gani" A haustine khairiyya ta kalleta

,"Kutmar uba, kina 'yar aikin gidan nan ki kalleni ki kirani khairiyya gatsai, shi kuma sarkin gaba d'aya kike kalla kina wani yaa prince, agidan uwarki ya zama yayanki ko yaya eee? ko motsawa beyi ba bare ta saka ran ze amsa ta, kallon sa Hafsat tayi aranta tace 'yar aiki a sarari kuma seta kalleta tace

"Pardon? shafa sumar kai khairiyya tayi data baje ya sauka a saman kafad'unta kafin tace

"Wai mekenan, zaki durk'usa kiji kiran me nake miki kiyi gaisuwar girmamawa kosena hallakaki tukunna"  Tsaye kawai Hafsat tayi tana kallon ta, ruwan dake gefen side table me asalin sanyi ta janyo cup d'in ta antayawa Hafsat a fuska da jiki gaba d'aya

"Da uwarki nake magana dabazaki yi abinda nace ba" Nan ma tunda Hafsat ta zabura dajin ruwan sanyi ajikinta bata kuma cewa da ita komai ba, kallon Hammood tayi
Chapter 28 · 0% Book details