Sashe 38
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai Ranki ya dad'e mu shaidane akan irin yanda Yarima Hammood yake tattalinki, ko ciwon nan dakikayi waccen uwar mulkin seda suka sab'a da juna, Allah dai yabar k'auna" Tab'e baki tayi
"Ni MOOD bawai ya wani dameni bane, kawai mulkin nake kwad'ayi" Nan suka dinga fadanci itadai ta basu wuri, tana barin wurin ta kira Nigeria, bayan sun gaisa da wacce ta kira tace
"Komai yana tafiya yanda muka tsara, a b'angaren kuyangin khairiyya ma na saye biyu daga ciki, nakuma tsoratar dasu, sedai a tayamu da addu'a Allah ya bamu sa'ar ceto Hammood daga wannan mugwayen mutanen"
"Ameen aka fad'a daga d'ayan b'angaren sannan sukayi sallama.... Hafsat ta wuce zuwa cikin gida tana mamakin sharrin mutane, dukda batada ishashen lafiya sanda suke maganar tona masa asiri amma tanajin su tas, bayan haka wasu abubuwan tana sani take yinsu, ta d'aura niyyan taimakon Hammood dankuwa dabe taimaketa ba da yanzu batasan inda take ba arayuwa. Shikuwa da tun sanda suka fara magana a garden basu san yana nan zaune a cikin manyan itacen banana yana shan islaba, runtse idansa yayi, tabbas shida Hafsat sesunga bayan juna, baze tab'a bari tayi nasara akan saba, su dama wad'an nan yasan da zamansu manya manyan munafukan fada musamman Amina, yajima yana zargin tasan wasu acikin Idan fada, su zuba ita dashi, wato Ita Hafsat aurararsa takeso tayi danta samu dukiya? Shida ita za'aga waye zewa wani kaye, ba boka ba ko shed'an ne akanta seyaga iyakarta.
*Toooh jama'a yanzu littafin tsintar aya ya soma zafi, yanzu ne za'a tsinci iyakar tsakuwar dake cikin ayar, gadai 'yar shara ta d'aura d'amarar taimakawa hammood, amma shi ga abinda yake tunani, shin wazefi shan wahala acikinsu? Shin waye yake baiwa Hafsat information akan su Ameena? Su waye Idan nan na fada? Anya Hammood be d'auka da zafi ba kuwa? Ku biyomu muci gaba da tayasu tsince ayar don ganin inda wannan abun ze kaimu, sonso masoyana kuyi hakuri jiya ban cika alk'awari ba*
*Mom Nu'aiym*
*TSINTAR AYA* FREE BOOK
*BILLY GALADANCHI*
*SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS*
Mik'ewa yae yana zagayar wurin, kanshi ya d'auki zafi sosai, shin a ina Idan fada suka samo wannan yarinyar? Anya kuwa wannan mutum mace kuwa, gaba d'aya be fahimci zuwanta a rayuwar saba a baibai, ta hanasu fad'n abinda suka gani to kenan shiri take akan ta gaya musu da kanta amma se yaushe? Mesa zata hanasu magana akan hakan? Ba yau aka fara zuwa ace yana magana ba, ba yau aka soma ba'a gansa ba aje ace an gansa sabida kawai anaso a tabbatar da zargi, babban abinda yafi damunsa shine besan su waye idan fada ba, amma gashi Hafsat tace tasan su ita, idan har so take tayi wasa da hankalin sa akan idan fada, idan so take ta kwashe sirrin sa ta gayawa Idan fada to yanada maganin ta, zeyi amfani da ita shima, ze wasa k'walwar ta, dama burinsa yasan su waye idan fada, togashi tace ta sansu bara ya barta sesu buga wasan bari ya gani shida ita waye zeyi kaye.
*************
Shiru d'akin taron ya d'auka ana jiran isowar shugaban k'ungiyar, mutane sunkai su ashirin kowa yayi tsit aciki talatainin dare, se k'arfe biyu daidai sannan shugaban ya shigo ya nemi kukera ya zauna kowa ya mik'e seda ya zauna sannan auka zauna suka gayar dashi tammar yanda suke gayar da sarkin Daulatur Dinar, bayan yayi gyaran murya seya fara magana kamar haka
"Anyi sanya sosai da aikin da aka baiwa yarinyar nan, ance shekarunta 17 anya batayi k'ank'anta ba? Shiru shiru babu wani k'wak'waran bayani daga wurinta yanzu watannin su nawa kenan a k'asar, tahau jirgin banza taje tanashan sanyi a turai ana bata kudad'e amma aikinta sam baya gudu mekenan muke zaune wangale da baki muna jira? Bazata iyaba a datse mata hanyoyin sadarwa inaga yafi" Seda yayi shiru sannan wani daga cikin su yace
"Inaga ba haka zamuyi ba, zaburar da ita zamuyi, a firgitar da tunaninta yanda aka saba, kada muzo ya samu wani ci gaban amma bamu sani ba" Bece komai ba wani daga ciki ya kuma cewa
"Shugaba inaga a matsayin mu da manya masu kaifin tunani sanadi kawai zamuyi masa daze dawo Nigeria, sanda yake kusa damu ai munyi nasarar shiga tsakanin sa da mahaifinsa,kokuma mu kasheshi kamar yanda tun farko mukaso, a wannan karon semu kashe har sarkin sannan mu namu sarkin seya maye gurbin su, danmu har duniya ta nad'e kaine sarkin mu, kuma da izinin Allah kaine zaka zamto jagoran talakawa nanda lokaci k'ank'ani, ko babu komai mahaifinka shine da sarautar nan bashida wani magaji kuwa sekai" Murmushi yayi najin dad'i kafin yace
"Tabbas lokaci yayi dazan nunawa mutumin nan iyakar sa, nayita kallon hankalin sa akan ya bani sarautar nan tunda gadon ubanace amma shi ta kansa kawai yakeyi se d'an cikinsa, nikuma ya mayar dani ko oho, zargina akan tabbas Hammood yana magana yak'i ya tabbata tunda be tab'ayi agaban kowa na, ansha a bisa masallaci ko shago ko dai wani wurin daba gidaba amma sam baya magana, yanzu akwai mutanen mu a U.S takanas nayi sponsoring nasu suke bibiyar sa amma narasa gano kan yaran nan sunce har acen baya magana, sabida haka kasheshi kawai zamuyi, dama naso ace yana magana ne sena tabbatar sena kashe sa, yanzu kuwa kurman gaskene to kuma uban bashida niyyan hanashi sarautar dukda cutar kurumtar daya gada awurin uwarsa, gwanda baya doron k'asar, gwanda ya mutu in huta da zullumi, amma shin anan zamu kashesa kokuwa?" Wani daga cikin su ne yace
"Shi wannan mutumen dasuke kira sarki bashisa adalci kuma be cancanci ayi masa sassauci ba, mahaifinka rik'on k'warya kawai ya bashi se Allah yamai rasuwa shin base ya mayar maka ba?, A'a sabida zalunci seyayi tazarce yace kai yarone a wancen lokacin yanzu ka hayyafa kayi gemu harya fara zama fari amma yana ihun cewar d'ansa ne magajin sa wannan ai mugun xalincine dan haka jininsa dana d'ansa ya halasta, dama duk wanda yakeso ya gifta maka bayan su" Gyaran murya ya kumayi sannan yace
"A shirya masa mugunta, a shirya masa makirci, a lafta masa k'aya ayi duk yanda za'ayi ya dawo Nigeria shida iyalin sa da ajayi masa auren gata yana kurma, ita gaggawa aikine dake b'ata dukkanin shiri sabida haka bazamu aiki da gaggawa ba, amma iyalansa dayake aure zasu shiga cikin sahihin shirin salwantar mana da tunanin sa zuwa tafiya me gangara" Dariya sukayi dan kuwa duk sun gane yaren seda suka tsahirta yaci gaba
"Munada labarin uwarta, muna kuma da labarin ita kanta duk a wurin wani saurayi me suna Bilal,yaran da yakeda video na komai daya shafi lalacin uwarta da ita kanta wanda yayi da ita, ayi amfani da wannan a girgiza duniyar ta, lallai koda k'arfin tuwo ne semun k'wato mulkin dayake mallakin mu munci gaba da wanzar da adalci a wannan masarautar" Nan surutai sukaci gaba na yanda za'ayi tilas Hammood da iyalansa su dawo Nigeria!
**************
*Shin ina labarin Bilal?*
Tun bayan da Bilal ya dawo garin seya samu kansa da bak'in cikin rashin cimma burinsa akan khairiyya, gabaki d'aya hankalin Bilal be kwanta ba musamman saya samu labarin aurenta da d'an sarkin garin dayake zaune, daganan seya k'ulla alak'a da wani yaro me suna Sabir wanda a masarautar yake zaune yana d'aya daga cikin 'yaran kuyangin gidan wanda baya aiki sedai yakanje shago a kasuwa, kuma babu laifi yanada abun hannun sa daidai gwargwado. Bilal ya bashi dukkan dama, hadda kyautar dubu d'ari uku akan ya k'ara jari, Sabir kuwa wannan batu ya masa dad'i yaji a duk fad'in duniyar nan babu wanda yakeso sama da Bilal...... lokacin da tafiya tayi tafiya a tsakanin su wata rana suna zaune agidan Bilal ya gayyato Sabir suna tsakiya dacin abinci se Bilal ya dire cokalin hannun sa ya kallesa yana murmushi yace
"Sabir ina inama nine kai? Ina matuk'ar k'aunar rayuwar sarauta koda kuwa daga sama ne kawai ace gani acikin babban masarauta bad'an kuyanga dake da matsayi ba, kod'an baiwa zanzo danayi farin ciki" Murmushi Sabir yayiwa uban gidan sa yace yana kallon sa
"Ranka ya dad'e rayuwar fada dakake ganinta gaba d'aya ba rayuwa bace me dad'i, banda k'iyayya hasada da kuma bin juna da sharri babu abinda yake cikin sarauta, bamawai awurin wanda sukeda sarautar ba ko magadan sarautar a'a wlh hatta wurin mu 'ya'yan bayi da kuyangi kowa hassada, kowama ji yake tamkar ya kashe d'an uwansa kaga yanxu akan sarautar gidan nan gaba d'aya akwai wata kafaffiyar k'ungiya anrasa waye shugaban ta, sannan koda kai member ne bazaka tab'a sanin wani member ba a k'ungiyar dan kuwa ance se cikin dare suke meeting kuma acikin duhu sukeyinsa sannan kowa da lullub'i a fuskar sa, shugaban k'ungiyar shishi kad'ai yasan kowa, kuma amma zakakeyin waya dasu da sauransu, kamar a film fa, su burinsu kawai su hallakar da sarki da d'an sarki kai ayanda naji ma sune suka kurumtar dashi, kuma baka sani ba ba akan gaskiyarsu suke so suga bayan bayin Allah nan ba wlh, sharri ne kawai irin na d'an adam, anace da k'ungiyar aci duhu amma mu dabamu sansu ba munace dasu idon fada, komai sun sani kuma idan kashiga kace zaka fita bazasu hanaka amma baka isa kayi awa ba'a lahira ba" kallon sa sosai Bilal yayi yace
"To yanxu kai duk ina kasan wannan labarin idan ba cikinsu kake ba" k'urawa juna ido akayi tsakanin Bilal da Sabir na wani lokaci kafin Sabir yace
"Ina d'aya daga cikinsu, sedai kuma aduk duniya kai kad'ai kasan wannan maganar, mahaifiyata ta hanani shiga k'ungiyar amma dolece ta saka na shiga sabida sharrin da akayiwa mahaifiyata, kuma sune suka nemeni akan in k'watar mata hakk'inta" kallon sa Bilal yayi yana wata shak'iyiyar dariya seda ya lafa sannan yace
"Amma kai Sabir wane sharrine zekaika k'ungiyar dasuke iya kashe mutum" Nisawa yayi kafin yace
"Bansan da sharad'in ba seda na shiga kaga ba zancen fita, bayaga haka kuma suna mana albashi duk wata dubu d'ari sabida basu information" kallon tsanaki Bilal ya masa sannan yace.