Sashe 53
Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Hammood tun d'azu naso kaje ka kwanta ka huta amma kak'i, ba yanda banso karkayi wasa da lafiyar kaba kabi ka dage" Yamutsa fuska ya kumayi
"Ba haka bane ba, inajin tsoron na mutu ne da hakk'in Hafsa akaina, likita ya gayamun harsashin nan har kusan zuciyata ya lek'a, hafsa ga wasiyya ko bayan raina ki daure ki gabatar da shaidun nan dankuwa an gayamun cewar tabbas niba me tsawon rai bane, kodan ki karewa yaron cikin dake jikin khairii martabar sa da sarautar sa tunda yar uwar kice" Hawaye ta farayi
"Likitan nan k'arya yake maka bazaka mutuba tukunna mawai shine yake da rai a hannun sa? Wannan ma ai mugunta ne, ka kwantar da hankalin ka inshaa Allah bazaka mutu ba" Dafe wurin yayi yakai kwance
"Koda ban mutu akan harsashiba su Baba Usman bazasu barni in rayuba nida me martaba tunda yake banida shaidun dazan karyasu, da wannan bak'in cikin gwanda na mutu na huta" Kukanta ta k'arawa sauti, komai yna wurin masscom, ka kwanta ka huta anan, da sassafe zankai yaa d'an sanda gun Masscom ya bashi komai" Hannunta ya rik'o
"Nidai koda na mutu ki taimakeni, ki ceci yaro ko yarinyar da za'a haifamun kuma kimun takaba, idan bazaki iya yimun talaba ba kuma kawai kawo biro da paper" ya soma laluben k'asa, hannunsa ta rik'e
"Kaida kake fama, tukunna bari ka warke mayi wannan maganar" Lafewa yayi hadda rufe ido irin na karyar nan,Data ya kalli Laure ya kashe mata ido d'aya sannan yace bayan yayi gyaran murya
"Abinda nake gani d'ayan part d'incen zan kaiku, babu security ace ku fita waje kunsan ana farautar rayukan ku, ke Hafsa seki tayashi kwana tunda kinga bazamu bar mara lafiya shishi kad'ai ba ko kuwa? Sororo ta sake baki tana kallon sa
"Intayashi kwana kuma, sekace jinjiri kaidai ka tayashi kwana nizan kwana tare da anty Laurah"
"Nida matata tunda mukayi aure bamu tab'a raba wurin kwanciya ba, akan me zakizo yanzu ki nemi rabamu, ina wannan mijin kine, kinga nifa banason zak'ewa idan be miki ba ki barshi kawai" Mood ne yace
"Ka k'yaleta ta kwana anan, nida zan mutu koda mutuwa nayi nasan banida wani gata a duniya, an barni na mutu ni kad'ai" kallon Mood hafsa tae bafa haka bane ba" Yana kanne dariyar sa yace
"Ka tayani in tashi inje masaukin" Data ma d'agashi yayi ya mik'e da k'yar sannan ta tayashi suka wuce har d'ayan part tana jera masa sannu, a darare ta xauna asaman gadon bayan an kwantar dashi, yana yamutsa fuska yace
"Kinga xafi nakeji, tayani cire rigarnan zakiyi, ni bazan iya d'aga hannuna ba" kallon sa tayi wane zatayi kuka ta langwab'ar da kanta sannan tace
"Yaa Mood dan Allah ka xauna dashi, kaga AC dukda yanzu aka bud'eta amma tana sanyi sosai, nanda anjima kad'an zaka soma jin sanyi ma" Yana meci gaba da yamutsa fuskar sa yace
"Idan tana goga wannan mikin nawa zafi nakeji sosai dukda a rufe yake" Rasa ma me zatace dashi tayi dole badan taso ba ta matsa kusa dashi tayashi mik'ewa zaune tayi sannan tana langwab'e kai tace
"Toka d'aga hannun ka mana" Cije leb'ensa d'aya yayi kafin yace
"Bazan iya d'aga hannuna konan dacen ba, ki taimakamun" kamar yanda akewa majinyaci haka ta cire masa rigar jikinsa, lokaci d'aya faffad'an k'irjin sa ya bayyana, wanda yakeda yalwar kwantacciyar gargasa ko ina ajikinsa, yayiwa fatar sa me haske kyau ainun, kallo d'aya tayi masa ta kawar da kanta aranta tace dama maza suna k'aton nonuwa haka sekace mace, tab'e baki tayi kafin a sarari tace ko meye ruwana oho!! Kallonta yayi
"Meyene? Juyar da kanta tae
"Ba komai, zanje wancen d'akin inkana buk'atar wani abu ka k'wallamun kira, tunda ba waya a hannun na" Kallon ta yayi yana wara ido
"Nan nefa tushen gidan madubi bakida labari? Kallon sa tayi kamar zatayi magana sekuma ta mik'e
"Kai kasan meye wannan" Tana juyawa hartakai k'ofa ya k'walla k'ara, da sauri ta dawo
"Menene kuma? Dafe wurin yayi
"Kwnaciya nazoyi na kasa, hannun nan tamkar an watsomin barkono" Da sauri ta dawo kusa dashi
"Sannu, bara na kwantar dakai" Tayashi kwanciyar tayi sannan seta zauna kusa da dashi
"Menene agidan madubi? Kallonta yayi sannan yace
"In baki labari? Nima uncle Jay ne yaje har U.S ya sameni yake bani labari a wancen lokaci, yace abokin sa ne sosai shi wannan kuma yana daga cikin mutane mafi alkhairi daya sani, amma labarin zuri'arsa tamkar a littafi kokuma a film............(Meson jin labarin da Mood ya baiwa Hafsah akan Gidan madubi ya bemi wannan number domin mallakar littafin Gidan madubi, donjina shin menene acikin wannan gidan?07084161619.*) Gabaki d'aya koda ya gama bata labarin tana jikin sa a mak'ale, banda gumi babu abinda take tana zare ido, kallon ta yayi yana me rik'o hannunta guda
"Ya naga duk kin firgita, ehm Hafsah? K'ara manne masa tayi
"Cewa fa kayi da gaske kake bawai labarin k'arya bane ba, kuma kace har a cikin gidan nan seda akazo da abin tsafin" Murmushi yayi
"Yanzu dai kiyi bacci duka wasa ne" K'ank'ame shi tayi
"Me k'arya dai d'an wuta ne" Yana murmushi ya lumshe idansa batare da yayi magana ba, a yanda suke a gincire haka bacci ya d'auke dukkansu basu suka farka ba se bayan takwas na safiya ya gota inda shi d'inma Hammood ne ya farka jin k'arar wayar sa, yanayin yanda haske ya ratso kawai ya kalla ya tabbatar yau sun sab'awa Allah akan rashin yin sallah cikin lokaci, Data ne yake kiransa, be tsaya amsa kiran ba kawai mik'ewa yayi da zummar zuwa toilet sedai me gaba d'aya jikin sa inda Hafsat ta rab'esa jini ne, cikin tsoro yaja da baya yana k'are mata kallo ita har lokacin bacci take abinta, rabin k'asan jikinta hakane, gajeran tsaki yaja sannan ya bubbugi kafad'arta ta farka a d'an razane, hannayensa duka biyu akan kunkurun sa yace
"Meke damunki haka? Wannan jinin fa? Da sauri ta sauke idanta akan jikinsa sannan ta saukesu a saman shinfid'ar da jikinta, a sarari ta furta
"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un! Gaba d'aya wata iriyar hatsabibiyar kunyace ta kama ta, batayi tsammanin hakan a daren yauba, se nanda kwana biyu meya kawo haka? Haka take fama da uban rushing indai tana period tamkar an yanka k'aramar dabba, kuma baze tashi zuwar mata ba se cikin dare sedai ta farka ta ganta a jik'e, kanta a k'asa tace
"Kayi hak'uri, ni bansan zezo yau ba, kuma banji alamun sa ba, bankuma san yanda akayi ya tab'a jikin kaba" cikin fad'a yace
"Wannan wane irin sakarci ne? Tayaya ma zakiyi sakacin da ranar dakike al'ada ze sub'uce miki, yanzu niba gidanaba banida kaya anan, ban yarda da kowa ba ya kikeso nayi" Batace masa komai ba, batama san me zatace masa ba tukunna, tsaki yaja sannan ya zari wayar sa ya kira d'an me ruwa, gaya masa abinda yake buk'ata yayi sannan ya kashe ya tura masa sakon address. Kiran wayarsa ya sauya akalar sa zuwa ga Data anan yake neman taimakon kayan sakawa dakuma aturo masa Laurah.
Bayan sunyi knocking yaje ya bud'e musu k'ofar ya tsaya yana kallon su, cikin takaici yace
"Waccen abar har yau bata wayau, ki dubata please tayimun shirme a banza" kallon sa Data yayi bayan ya janye jikinsa Laura ta shiga yace
"Meke faruwa kuma? Yamutsa fuska yayi
"Sha'anine irin na mata, ka sauyamun d'aki please zanyi wanka" Janyo hannun sa yayi suka bar wurin sannan yace
"Yallab'ai likitan ka ya tabbatar mun raunin jikinka yana damunka, ance baze warke ba inhar muddin bakashan magungunan ka, mesa bakayin ta lafiyar kane wai, sannan wannan yarinyar a hankali zakake mata, daga kallon yanayinka na tabbatar fad'a ka mata, kakeyin komai a hankali a kanta, sadaukar war datakeso tayi tabbas idan tayishi tayi abinda ake cewa halacci sedai kawai muce aure ba wasan yara bane ba, dan haka zamuyi wasa da hankalin ta acikin ruwan sanyi" Jinjina kansa yayi sannan yace
"Uncle waikasan wawiyar gaskece yarinyar nan, ita khairiyyan datake mawa batada wacce ta tsana sama da ita" Murmushi Data yayi "Ba wawanci bane ba kawai irin nata tunanin ne haka, bakaga yanxu tayi hikima wurin nemo suwaye mugwayen dake binku da sharri, amma ta sanya wawtar daya fallasa ta, ai tanada wayau ne amma batada dabara abinda yake cutar da ita kenan" Sanda suka isa d'aya d'akin ya mik'a masa biro da takarda
"Ka rubuta mata sakinta anan, zata bamu abinda muke buk'ata, tayiwa kanta" kallon tuhuma yayiwa Data kafin yace
"Uncle are you sure? Zama yayi akan gadon
"Sure mana ba abinda take buk'ata ba kenan? Nisawa Hammood yayi sannan ya zauna ya karb'i biro da takardan ya zauna ya soma rubutawa...