← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 71

Sashe 45

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Momy nice baki gane ba dududu kwana nawa? Rungumarta momy ma tayi kafin tace

"Allah sarki 'yata, nayi kewar rashinki, naje garin kuma labarin danaji bemun dad'i ba, acen naji sharrin da Bilal ya miki abin ya d'auren kaina sosai, na gaya musu gaskiyar niba haka ya faru ba, kece ya rage na nemi gafararki hafsat, muje gida, dama kekam ina shirin sanar dake dukmanin abinda ya faru tun daga farko har k'arshe" Murmushi Hafsat tayi kafin tace

"Idan na dad'e banje gidaba zasu nemeni momy, ki bari gobe zanzo" rik'o hannunta tayi to muje mota zan baki labarin duk abinda ya faru acikin minti uku zuwa biyar" Hafsat bazata iya yiwa momy musuba dan haka ta bita har mota, anan taji labarin daya girgiza ta kuma ta tabbatar khairiyya itace kishiyarta a yanzu dama tayi imanin akwai inda tasan khairiyya, kenan Bilal fyad'e yayiwa khairiyya? Kuka kam atare suka shashi itada momy daga k'arshe suka rabu bayan exchnaging number waya suna yiwa juna alk'awarin sake had'uwa, dan hafsat ta nunawa momy cewar bazata iya bata labarin taba a yanzu sesun sake had'uwa sabida tana sauri, dan kuwa momy tace tanaso hafsat ta dawo gidanta da zama gaba d'aya.... Aran Hafsat tace Momy wannan bame yiyuwa bane yanzu.

Ko wannan karon a k'ofar shiga Fadar Sarauni sukayi karo da Hammood,kallon juna sukayi sannan tayi gaba abinda batare datace masa ci kanka ba, a fusace yabi bayanta zuciyar sa tana harbawa, yayi sa'a Bahar bata parlor dan haka yabita har cen cikin d'akinta, kallon juna suka tsayayi tace tana zare abayar dake jikinta da dankwali ta dawo iya riga da wandone a jikinta

"Malam lafiya"

"Daga ina kike ? Ya tambayeta yana muzurai murmushi tayi

"Mesa kakeso ka sani ? Dakabi bayana bakaga inda naje bane dakake tambaya na" kallon ta yayi yarasa wace irin mara kunyace Hafsat

"Kinsan dai daga fitarki har dawowarki kina tare ne da tsinuwar Allah da mala'ikunsa ko? Kina matar aure kike fita babu izinin fita, daga yanxu ban yarda kije konan dacen batare da izinina ba" Wata dariyar raini ta masa

"Ban gane me kake nufi ba ? Tun yaushe ka bani izinin fita tunda har kai kayi kwance? Yazan biye maka mu lalace?

"Me kike nufi da kalamanki?

"Oho a tambaye ka" Rugowa yayi se damk'e ta ta kauce masa ta arce aguje zuwa waje yabiyo bayanta, a parlor ta zagaye bayan bahar shikuwa segashi aguje

"Nashiga Uku Ni Bahar Sarauni, yau naga d'ebar albarka la'ada wuri, kai yanzu dan bakada mutunci shine bazaka dena bibiyar yarinyar nan ba, Allahu bazakamun abinda kakeso agidaba, gobe zan kaima ka matarka" Mak'e kafad'a hafsat tayi cikin muryan sangarta tace

"Mugune Bahar, karki kaini wurinsa dan Allah, ya dinga jamun suma na idan banyi abinda yake so ba"

"Aikuwa idan ya kuma ja miki suma senaja mai la'anta yaseen, kwanakin nan rashin Daraja Hammude keji, ita waccen matar taka bazata iyaba bane ba? Kake bibiyarmun jikata da sabon dalon d'angwalar yaji, banason renin hammatan me shayi kamaji na gaya maka" A harzuk'e yabar gidan bayaso yayi magana amma tabbas seyaci kaniyar hafsat.

*************
Dukkansu su uku atare sukayi shirin fita, Hammood, khairiyya da kuma Hafsat, khairiyya da Hafsat munsan destination d'insu mararraba hotel zasuje, hammood ne bamusan inda zashiba, ga kuma idan fada dasuma suka d'auki destination d'aya dasu khairiyya..........

*Sorry na muku kad'an, ba charge a phone d'ina, gashi naso sosai inga yau ko Hafsat zata tsira......to mu had'u gobe dai inshaa Allah.*

*Mom Nu'aiym*

  *TSINTAR AYA*  FREE BOOK

         *BILLY GALADANCHI*

     *SHAFI NA ASHIRIN DA UKU*

23.
Tunda wad'annan mutanen suka fara shigowa se gaba d'aya hammood yabar reception sabida shima bawai ya fito haka kawai bane, tsaf acikin motar sa seda ya sauya kaya zuwa wata matacciyar yadi da hula kayan daud'ar jikinsu kad'ai ta ishe su, gaba d'aya yayi dressing irin na me garin k'auye da wani karkataccen madubi bayau ya saba basaja irin haka ba, dan kuwa gaba d'aya motar dayake kanta ba wacce aka sanshi da ita bace, wata iriyar starlet ce me sanya ciwon jiki, gaba d'aya rawanin dake kansa ya wani cukurkud'e wuri d'aya gashi a karkace, wannan shirin ba k'aramin b'atar da kamanin sa yayi ba fiyeda yanda ya kawar da kamanin Hafsat, shi kanshi shirin barin wurin yake dan haka kusan atare suka shiga abun hawa, ita tahau napep shikuwa ya shiga wannan kwarab'abbiyar starlet danake da tak'inin ta girmewa shekarun haihuwar sa, kallon matar yake data shiga keke napep d'in, tun d'azu me napep d'in yake wurin bayan ammasa bayanin wani abu an nuna masa waya, kuma wanda yabi bayan matar yashiga napep d'in bawai tare suke da matar ba, sannan kuma yaga yana wata magana dame napep d'in kafin fitowar ta, kenan parking d'in natane dama ita ake jira? Dama motarsa a kunne take hakan yasa yayi azamar zuwa domin yayi overtaking nasu amma me seyaga matar ciki wuyanta  ya tafi baya tamkar matacciya har mayafinta ya zame baya, seda wata mota ta tashi bugun nashi sannan ya saisaita kansa, me napep kuwa zuwa yayi da azama ya wuceshi sunata sauri tamkar zasu tashi sama wannan ne ya k'arawa abun k'aimi a zuciyar sa yace lallai seyaga inda suka dosa!

      Sanda yabi ta d'ayan layin daya ajiye motarsa yayi parking wannan motar sannan yashiga tsakanin gutter's ya tsallaka ya b'ulla ta wannan layin dayayi parking acikin motarsa ta alfarma ya sauya kayan jikin sa nanma, seda yayi branching guest house nashi yashiga ya ajiye wannan motar sannan yafita da wata motar ta k'ofar baya ya nufi masarautar sa a sukwane tamkar zakin daya shekara beci namaba! Kai tsaye part d'in khairiyya ya nufa acen ya tarar ta dawo, kallon ta yayi sosai sannan ya haska mata wayar sa, sesa ta karanta abinda yake nuna mata sannan ta kawar dakai tare da cewa

"Anguwa naje" Cikin fusata ya kuma rubuta

"Yaushe kika isa kije unguwa batare da izinina ba? Kuma unguwar wurin wa? Wa kika sani a garin? Tana gama karantawa ta kallesa

"Ajiyeni kayi ne? Kokuma kaine raina yake hannunka kaga Hammood dan Allah ka shafawa lafiya ta lafiya, abinda ya isheni ya isheni" Fusata yanzu kam yayi ya matso kusa da ita a harzuk'e ita kanta tayi mamakin yanayin sa, tunda suke yaune rana ta farko data hango masifa haka a idansa, matseta yayi har jikin bango amma bece mata ci kanki ba kawai ya tsatsareta da manya manyan idanuwan sane dasuka sauya launi, runtse idanta tayi cike da tsoro, she really need a shoulder to cry on, mesa yake mata fad'a, gaba d'aya mahaifiyarta ta janyo mata mummunan tabon daze illata rayuwarta, menene amfanin wannan mugun aikin data aikata, akan me Bilal zeje wannan matakin a tonawa mahaifiyarta a siri, zuwa wannan lokacin gaba d'aya kukan datakeso tayi tun d'azu bezoba se yanzu ya wanke fuskarta dukda idanta a rufe yake, duk yanda taso ta had'iye kukan nata seda yazo da iyakacin k'arfin sa, kukan ta saka sosai wanda ya sanya yayi kasake kawai yana kallon ta cikin mamaki, maganar sace ta b'ata mata rai kome? Metakeyi tare dasu Baba Usman? Me suka ce mata? Is she alright? Janyota yayi zuwa jikinsa ya soma patting bayanta a hankali ziciyar sa tana harbawa ya tabbatar akwai wani abun dasuke shiryawa tare da khairiyya kuma yanzu ne suke so suyi trapping nata tun ita batasan asalin halayyar suba, meke shirin tasowa kuma, be hanata kukanba seda tayi me isarta sannan ya kwantar da ita kawa yabar d'akin dan kuwa hankalin sa yanakan waccen yarinyar dayabi bayan 'yan keke napep yaga sun kaita unguwar Shiyar fada cikin tsohon guest house d'in me martaba dayake k'ark'ashin kulawar Baba Usman a yanxu, mecece alak'ar dake tsakanin Baba Usman da khairiyya, mesa kuma ya sanya aka d'auke matar mutane zuwa shiyar fada danya tabbatar cewar shine ya sanya aka d'auketa, to Amma ina hafsa taje? Metajeyi a wannan gidan? Kai tsaye part d'in Bahar ya nufa dan yasan a k'a'ida yau akace zata tare agidan ta, koda yaje ya binciki bahar batanan, driver dasuka fita atare ya tambaya ita inda ya tabbatar masa da cewar ga unguwan daya kaita kuma tace k'arfe shida ya koma ya d'auketa, yaje ance tafita tin yamma bata dawo ba, yajira har bayan magrib bata dawo ba wannan ya sanya ya taho a tunanin sa ta koma gida! Kai tsaye gidan Hammood ya nufa inda yaje ya tarar da Baba me gadi dan tuni ya dawowa aikin sa agidan, seda ya waiga baya yaga ba kowa sannan yace

"Ka shiga ciki Baba dan Allah ka sanar wai Hafsat ta fito inji mijinta zasuje gida" Jin wannan sak'on ya tilastawa Momy fotowa daga cikin gidan tazo suka gaisa da Hammood inda kallo d'aya yayi mata k'irjinsa ya doka da kamanceceniyar dake tsakanin ta da khairiyya, gayar da ita yayi sannan ya sake maimita abinda ya sanarwa Baba me gadi, da mamaki tace tana kallon sa

"Hafsa a charge tabar wayarta kuma k'arfe shida tacemun zata dawo,bansan inda ta tafi ba bankuma san meya tsareta a inda taje ba, ni kaina na shiga damuwa sosai" Nisawa yayi sannan yace

"Ba damuwa nagode sosai, inaga tayi yamma ne ta wuce gida" Cikin rashin kuzari tace

"Ze iya yiyuwa hakan ne, zekuma iya yiyuwa wani abin ne, koma menene dai i will keep u updated idan tazo idan ma batazo d'inba" Godiya yamata amma be karbi lambar wayarta ba a hanzarce ya juya shitar fada batare da wani tunani na biyu ba, ko shakka bayayi wannan matar Hafsa ce, she can go to any extend akan abinda takeso, yayi iyakar tunanin dazeyi akanta ya gagara gane wa tskewa aiki akansa, kome menene wannan al'amarin tabbas babbane a wurinta indai har zata iya amfani da wannan hanyar me cike da hatsarin gaske wurin cimma burin ta! Yana shiga gate ya kira masu gadin gaba d'aya da masu kula da shuke shuken furannin gidan gaba d'ayansu wayoyin hannunsu yanfara karb'a sannan yace yana kallon me gadin

"Its been long i cm here show me in" Ranka ya dad'e duk datti ga k'ura ba shiga ake ba" kallon masifa ya wurga masa kafin yace
Chapter 45 · 0% Book details