← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 71

Sashe 1

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

  *TSINTAR AYA*

*BILLY GALADANCHI*

*Bansaniba ko a wannan lokacin alk'alamin dana d'aga ze samu daidaito a tsakiyar zuciyar makaranta litattafaina tsofaffi da wanda zasu fara a yanzu! Abu d'aya na sani shine tabbas wannan salon daban yake, wannan salone me tsawon tafiya kana kuma salone da ban tab'a zuwar muku dashi ba. Ban shirya siyar muku dashiba, haka kuma bazan sayar d'inba, littafin kyautane babu tantama. Maganar dazan fad'a kai tsaye anan itace Akwai kalmomin dake jingine da nauyi acikin su, musamman awurin yaranmu, salone daze amfani kowa anawa ganin, amma ina roqon alfarma awurin yara su jingine wannan amfanin zuwa lokacin da karanta littafin ze amfane su.*

*Babu batsa aciki, sedai kamar yanda na fad'a kalmomi da abubuwa masu nauyin d'auka, banida hanyar sakaya kalaman masu jingine da nauyi abayansu, sedai inshaa Allahu zanyiwa kalaman kwaskwarima daidai da sakaye zuwaga zallar batsar.*

*Ban saniba ko zakuyi farin ciki da hakan, amma saukar kowane shafin zezone bayan na ajiye wanda ya gabacesa da kwana biyu, ina fatan hakan ze dawwamar da farin ciki a zukatanku masoyana.*

*A nawa b'angaren ra'ayi kuwa strictly matan aure zallah.*

*Tukuici zuwa gareki k'awata Ayusher muh'd, Alkhairin Allah ya kaimiki a duk inda kike, Allah ya d'auka kaki ya raya miki zuri'arki,yakuma albarkace su fiyeda iyawarki. Son so fisabilillah.*

*SHAFI NA D'AYA*

      Duk yawan mutanen dake bayansa suna k'ok'arin ganin sun take gabansa da bayansa hakan yaci tura, sabida yanayin sauri da Hamood keyi, saurin kuwa tamkar ze tashi sama haka yakeji, sabida lokaci zuwa lokaci yakan wurga kallonsa zuwaga agogon hannun sa yana me k'ara sarrafa k'afafunsa zuwa ga d'an sassarfa, tafiya dabata wuce ta mintuna uku ba ya sauya akalar k'afan nashi daga sassarfa zuwa d'an gudu lokaci d'aya yana tattare hannayen rigar sa zuwa sama. Mabiyan nasa ma gudun suka soma tamkar wasu zararraru haka suka dawo acikin fadar kowa se kallon su yake ido k'asa sabida sunsan halin Hamood yanzun nan zece kana kallon sa kai munafiki ne. A sukwane suka k'arasa cikin fadar, a tsaitsaye ya taradda d'aukacin dattawan fadar da kuma  masu babban muk'ami acikin fadar kamar su waziri,sarkin yak'i, Magatakarda da sauransu.Dukkansu sunyi layi gefe da gefe sunbar fili a tsakiyar su inda dagacen zaka hango me martaba a zaune saman wata kujerar mulki ta alfarma wacce aka k'era da zallan ruwan zinariya rubuce a saman ta an rubuta Daulatul Dinar! Be wani b'ata lokaci ba wurin k'arasawa kusa da me martaba lokaci d'aya ya sunkuya yana nuna alamar gaisuwa amma bakinsa be motsa ba babu kuma alamun ze motsa d'in! Kallon k'ur me martaba ke masa na wani lokaci yayinda wasu lafiyayyaun mintuna goma suka wuce amma har lokacin Hammood be gayar da Mahaifin nasa ba! gyaran murya murya Me martaba yayi inda sabo ya saba da halin Hamood d'in, wasu 'yan dak'ik'un seconds suka shud'e kafin yace.

"Hammood Menene dalilinka na kawo 'yan mata acikin fada? kana sani kuwa cewa hakan babban laifine da wannan masarautar bazata iya gafarta maka akanshi ba!Idan kana wajen masarautar kayi abinda kakeso mahaliccinka na kallon ka. Amma anan bazamu lamunta ba, sabida haka daga yau karna kumajin makamanciyar wannan halin a fadar nan" Shiru wurin ya d'auka na wuccin gadi, tsakanin mintuna da dak'ik'u an samu shud'ewar kusan minti talatin amma be motsa ba be d'ago kansa ba bakuma ze motsa d'inba kamar yanda koda ba gaskiya bane baze tab'a iya musawa ba. Shirun dayayi yawa ne ya sanya Me martaba cewa dashi

"You are dismiss" Be jira komai ba a sukwane ya mik'e tare da k'ara sauke kai k'asa alamun girmamawa sannan ya juya a hanzarce kamar yanda yazo yana shirin barin wurin kusa da galadima ya tsaya suka kalli juna, lokaci d'aya galadima ya d'auke kansa shikuwa seda ya gama k'are masa kallo sannan ya wuce cikin hanzari.

     zuwa wannan lokacin gudu yakeyi amma idansa duka biyu a rufe yake, yayinda mabiyansa ke biye dashi cikin tashin hankali. Timing dama yake sabida haka adaidai sanda ya iso inda yakeson tsayawa sekuwa ya tsaya d'in yana mayarda numfarfashi sama sama, Babban cikin mabiyansa ya kalla sannan ya d'aga hannu ya masa nuni da cewar ya bashi biro da paper. Atake jikin su duka ya mutu dan kuwa sunsan an tsokano musu yau, a hanzarce ya rubuta

"Nextweek" ya mik'awa mutumin shikuwa jikinsa har rawa yake ya wurgawa takardan kallon baya ya karb'a sannan yace yana russunawa

"Sun dad'e sosai suna jiranka yallab'ai, dan Allah a dubawa uzurin su" Lumshe idansa yayi sannan ya bud'esu ya zuba tas akan mutumin sannan ya kuma yi masa nuni da biro da paper, da hanzari ya k'ara mik'o masa matsakaiciyar Joter...

"Kainane yake ciwo, kayi musu dukkanin abinda ya dace ka bani bayani a rubuce, kada ka manta ina kallon komai"

"Nagode da wannan karamcin yallab'ai, i will send ur doc right away" Murmushin gefen baki ya sakar masa sannan yad'anje baya da baya da gudu kafin ya juya ya runtuma aguje sekace wanda yake gasan tsere!
   K'ofar part d'in nasa da kanshi ya bud'e ya shiga ciki, ma'aikatan dake gyaran k'asa ya tsaya ya k'urewa kallo sosai dukkanininsu sesuka zube suna kawo gaisuwa dukda yake sun tabbatar da cewar bawai ze tab'a amsa gaisuwar tasu bane, Lumshe idansa yayi sanda standing AC dake parlorn ya watso masa wani had'add'en sanyi da k'amshi sannan ya zube hannayensa duka a aljihun sa ya haura saman batare dayace dasu ci kanku ba. Yara 'yan mata biyu dake k'ok'arin gyaran b'angaren basusan da zuwan saba kwata kwata, wannan ya sanya me 'yan shekarun aciki take nunawa k'aramar wani hoto

"kalli da kyau ki gani Amina, yana magana fa, ba abinda ya iya se tsagwaran iskanci, amma mu sekace ba matan ba ya iya sha mana mur, kalli dai a hoton nan yanda ya rungune wannan macen sekace matarsa, uban kowa kuma yasan cewar be tab'a aure ba, haka zezo da mata da maza acikin gidan nan ayita sowa aci asha amma dazaran ya fito seki nemi koda murmushi a fuskar sa ki rasa tsinanne" k'aramar ciki ce ta karb'a da cewa

"Lallai ma, inatajin labarin mutumin nan, masarautar nan kowa ya bud'i baki prince Mood dai prince Mood, nina zata wani kamilalle ne ashe aminin shed'an ne" Dariya dukkansu sukayi kafin suka tafa suna shewa. Tamkar beji me sukace ba haka ya wuce batare dayace dasu kanzil.ba ya shiga bedroom dayake mallakin sa a part d'in. Sosai ganinsa ya firgita k'aramar harta riga babbar zubewa tana k'ok'arin gayar dashi muryanta yanata faman rawa, For the very first time ya waigo ya k'arewa dukkansu kallo, suna tsugune dazaka saurara a wannan a lokacin dakaji yanda cikin kowaccen su yake bada sauti k'uuuu alamun cewar tabbas k'ir suke jira su b'arke da zawo! batare daya ce dasu kanzil ba ya shiga d'aki abunsa, Babbar ce ta soma mik'ewa

"kurma ne dama kamar yanda akace uwarsa ma kurma ce, ni tunda nake dashi bantab'ajin maganar saba" Kallon ta Amina tayi

"Amma yanajin duk abinda ake cewa, cutar kurumtar ce dai ban saniba ko tabbas ce danko yanzu indai ba kurman bane ya dace yaji me muke cewa akanshi" Dariya siririya Babbar tayi sannan tace

"Ni idan naga ire iren hotunan nan a part d'in san nan se inga kamar tas yakejin komai damuke cewa, amma idan muna zaginsa ya kamamu kuma baice komai ba se inga kamar tabbas bayaji d'in,to amma fa komai a rubuce yake bayar dashi, idan an masa magana seya baka amsa a rubuce kinga dai inhar yana fahimtar maganar ka toko tabbas yana jin magana ba kurma bane" Cigaba da goge gogen da take tayi kafin tace

"Koma dai yanaji ko bayaji kanshi akeji, ni gwarama da naya magana akan wancen D'an galidaman me kafirin girman kan tsiya sarakan iya zagi" haka sukayita tsigarar wanda basaso har xuwa lokacin sa suka kammala ayyukansu tatas.

***************
Chapter 1 · 0% Book details