← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 71

Sashe 54

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****************
    Hannu ya sanya ya share zufar data tsatsafo masa sannan yace "Menene amfanin wannan aikin dana sakakaku, ina amfanin kud'ad'en dana baku idan har bazakuyi amfani dashiba yanda ya dace, kun d'auki hayar makasa wanda bazasu iyaba basu k'ware ba, asirin mu yana nema ya tonu, k'aramar yarinya ace itama kasheta ya gagareku, gaba d'aya a binciki wa dawa take huld'ar sirri dasu a kashesu ma abun ya gagara,sannan ku zauna anan kuna gayamun maganar banza da cewar wai in kwantar da hankalina, inama naga hankalin bare na kwantar dashi, wlh kunji na rantse na baku awa ashirin da hud'u ku nemo mun prince da matarsa wannan hafsatun ku kashesu, banaso su wuce wannan lokacin a duniya, sarautar wannan garin ko anaso ko ba'aso tawace, wannan daula ce data kafa tarihin ruwan daham, ruwan d'anyen gwal daulace me arziki da tun kahuwar tarihin k'asar hausa ba'ayi daula me arzikin taba, yaya zan rayu jinina yana yawo dana wannan daular in mutu ban mulke taba, ko Masarautar Daular Dahamiyya wacce tafi dukkan masarautun dasuka gabaci wadannan arziki bazata kara da wannan ba ko'a duniyar da, dukda yake sunci kakan kakanmu da yak'i, wlh summa tallahi billahi bazan saurara ba senaga bayan wad'an nan abokan hamayyar nawa kamar yanda Marwan na masarautar Daular dahamiyya yaga bayan nasa abokan hamayyar kamar yanda yazo a tarihi!!!( Meson jin labarin Daulatul Dahamiyya, ya neki littafina na gaba inshaa Allah domin jin wannan labarin me cikeda abubuwan ban mamaki tsoro da kuma al'ajabi, bazan sauke saba seya zama complete yanda zakufijin dadin siyensa, don haka a shirya a bude bakin aljihu a kwashi garab'asa.).

"Ranka ya dad'e Allah yaja zamanin ka, wannan sarautar takace, kai d'an na gada ne ba taka haye ba, nasara a hannun ka take ka kwantar da hankalin ka, yau bazan rufe idonaba, ruhina bazeje rangaji ba harsena tabbatar Yarima Hammood da wannan tsintacciyar magen basa numfashi, zan kashesu zan lalata gawarsu yanda bazasu samu damar a gane suba, zan tabbatar inshaa Allahu jama'ar musulmi bazasu sallace su ba, sena tabbatar ayau basu runtsa ba, majita me tushe ta tabbatar mana agidan detective Sufyan suka kwana na intelligence agency, idan tak'ama yake yana aiki da kwamputa zan nuna masa yanda ake aiki da k'walwa, yana cikin gidan sa zan had'a harshi tunda ya nemi shiga hakk'in mu" Mik'ewa yae

"Kowa yana murna na zuwansa duniya a zamanin wayewa, nayi matuk'ar bak'in cikin daban ziyarci daulata a duniyar data gabaci wannan ba, na tabbatar da hakan ta kasance bazan tab'a shan wahala akan neman mulki ba"

"Hakane sarkin sarakuna, ko yanzu kaine da sarautar bazamu sauraraba semunga bayan wannan azzalumin gawa k'ink'i ramun, dama ya gama komad'ewa" Shidai a fusace yabar wurin su kuwa suka zauna meeting na musamman akan yanda zasuyi dasu hafsah.

**************
      Sanda suka shigo itada Laurah gaba d'aya hankalin Hammood ya karkata ne akan Hafsat, zuba mata ido yayi bayako k'iftawa har sanda suka zauna, dafe kansa yayi sannan ya sake ya d'ago ya kalli Laura adaidai sanda suka zauna yace

"Anty Laurah kindaiga abinda Hafsa tamun ko, ta tilastani na rabu da ita akan abinda ni bawai ya shafeni bane, ga Uncle ya kafe akan dole haka zanyi, hankalina ya tashi sosai, ba yanda na iya amma inaso na ceci al'umma ta da mahaifina, dole na mata yanda takeso ga takardar nan hannun Uncle sufyan Allah ya kyauta" Kallon sa tayi dukda tasan basonta yake ba amma ta tausaya masa yanda yayi maganar

"Hak'uri zakayi Hakan shine tsarin Allah" Gyaran murya Data yayi ya warware takardar dake hannun sa sannan ya soma karatun takardar kamar haka

-Assalamu Alaikum-

-Ni Hammood na saki matata Hafsa saki uku bisaga wani babban dalilin damuka barwa kanmu sani, idan ta gama idda inta samu miji tayi aure.- ya k'arashe yana nannad'e takardar ya kalli Hafsa yace

"To kindai ji kamar yanda kika buk'ata an sakeki d'in, seki bamu abinda muke buk'ata" Tunda dama ya soma karanta wannan takardar take kallon Hammood as easy as that ya saketa, shi bayako tausayin rayuwar ta, koda ita ta nema aida seyayi koda d'ayane ko biyu haka zatafi ganin ya kwatanta mata adalci amma har uku, hawayen datake k'ok'arin tarewa ne ya silalo mata tana sharewa tace

"Sunan sa Ayatullahi amma mutane suna kiransa da suna Masscom 2, akwai Masscom 1 amma dashi nayi basaja, naje wurin Ayatullahi yakemun aiki sabida ogansa ne, duka lambobin wayar shi Ayatullahi suna kaina, a hannun sa akwai dik wani record na meeting da ake gudanarwa na idan fada me taken aci duhu, bansan fuskokin suba amma tabbas muryoyin su sunyi nuni da fuskokin su wannan shine kuskurensu na farko, aciki akwai kawunka Uncle Jay wanda yana daga cikin planners dasuke tsara yanda za'a kasheka akowace safiya, nasha bashi k'afa ma, hatta me keke napep daya d'aukeni a ranar da aka saceni Uncle Jay ne yayi hayar sa, kuma akwai muryar sa acikin bayanai na na sirri masu yawa, abinda ya faru harya fallasa shine...A ranar danaje hotel bani kad'ai nake ba, kafin na shiga keke napep spyies dina sun d'auki plate number sa, kafin nayi komai ina zama ajikin keke napep ba d'ana tracker sabida ban yarda da kowa ba wacce Ayatullahi yake bibiyarta koda bakaje shi dama zeje lokation harma yaje ya gama tsara yanda ze fito dani seka rigashi, ina zama sanda wani ya rufamun k'yalle na gama afka masa tracker a zoben hannunsa sanda nake k'ok'arin kare kaina daga gareshi na rike hannun sa, UncleJay yana yawan murd'eni baibai, bansan dalilin sa na aikata abubuwa da yawa ba, acikin fada zan iya yarda kowa ze cutar da Mood amma Jay, amma me bansan mesa duk inda zan buga seya bayyana ba. A hannun Ayatullahi akwai recording na umarnin da aka bayar akasheku, wanda Uncle Jay ne ya baiwa makasan wannan umarnin cewar suyi harbi! Kullum tunani na shin wanene Incle Jay wai? Menene ainahin zuwansa duniyar ka? Anya antab'a masoyi kuma b'oyayyen mak'iyi? Ina zanbi na harbo bakin zaren? Bazan iya ci gaba da magana ba amma ku nemi Ayatullahi kubi komai a sannu, ku saurari komai, komai yanzu na kirawo shi nan yazo da komai" Nisawa Mood yayi zufa tana tsatsafo masa tin yaushe ake gargad'in sa akan Jay! Tun yaushe Muhseen yake yawan son ankarar dashi akan Jay! Menene wannan yarinyar take magana akan sa akan Jay? Yaya ze rayu idan wannan tambarin ya daki k'irji ya tabbatar cewar Jay ne matsalar sa!!!!

"Ki gayyato mana Ayatullahi anan, bazamu iya fita waje ba a wannan yanayin ko medications na prince daga waje aka siyo za'a kawo mun, nan shine tsaronmu ko ina camera ne, suspicious person ma yana tinkarar bangon gidan nan zanji alert na tinkarowar sa ta hanyar waya ko agogon hannuna koma duka gidan xe d'auki sauti me ratsi. Runtse ido Hammood yayi sannan yace yana kallon Hafsa

"Banaji Jay zemun haka Hafsa mecece hujjarki ta kafewa akan hakan? Murmushin takaici tayi

"Ka rigada ka sayi duk wani information dake bakina ta hanyar manna mun saki har uku sabida haka anan ko Bahar ce batada gaskia zan tona ta bare duk wanda yayi saura, ku bani waya zan kira masscom" kallon ta yake ya gaza gane inda akalar zancen ta yake dosa, komenene dalilin dayasa gaba d'aya wannan take a baud'e? Bece mata komai ba ya zaro wayar sa alamun number yake jira, kai tsaye ta zube masa lambar ya kira ya mik'a mata anan tace da Masscome

"Bansan yanda za'ayi dattijan taka ya bayyana a jikinka ba, ban saniba ko zaka iya zuwarmun a siffa irinta dattijo me neman gadi a layin gada biyu ba, layin dake bayan shiyar fada a zaurawa road gida me bugun lamba sha bakwai harafin dake bin bayan A a rubutu acikin sa'a d'aya ko k'asa ga hakan ba" Wata magana akayi a d'ayan b'angaren daya sakata yin murmushi tace

"Kaine kakeda basirar baniba Ayatullahi, idanda baka fahimta gaba d'aya da banga amfanin sauyawa rawar kid'aba" Godiya tayi kafin ta ajiye wayar inda Data ya kafeta da ido yana mamakin irin baiwar dake kanta, komai itace take tsarashi gaskia tana k'ok'ari sosai.

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*Sak'on gaisuwa zuwa gareku mutanen Daraja kuma nagartattu, Lallai na aminta ita darajar gaskia ta Allah ce, Allah ya saka muku da alkhairi masu alk'alamin daraja, Nu'aiym yana matuk'ar godiya da addu'o'inku da kulawarku da kuma jajircewa, bazamu manta dakuba Sister Batul Mamman, Ant Mejidda musa, antyna Zuwaira maman ja'afar, Ayusher muh'd, Maman khady da sauran wanda ban ambata ba, Allah ya karrama darajar ku ya d'aukaka darajar alk'alumanku, ya saka da alkhairi.*

*Sak'on gaisuwa na musamman zuwaga d'aukacin mutanen duniyar kafar sadarwa ta whatsapp, ubangiji yanda kuka hana wayata sakat da kira domin jin labarin lafiyar Nu'aiym ya hanaku bak'in ciki duniyar sa da lahirar sa,Allah ya saka da alkhairi yabar zumunci, tabbas kun nunamun halacci kun tabbatar mun da cewar ina zagaye ne cikin nagartattun mutane, Allah ya biyaku da aljanna mad'aukakiya.*

*Anty Ramla @ mai dambu, inji Nu'aiym yace a gaisheki da k'ok'ari.*

*SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS*

    28.

Yanayin shigar sa irinta mutanen Niger, yanayin sa gaba d'aya tamkar wani bak'in buzu, gaba d'aya kayan tarkacen sanduna ne ajikin sa, d'auke da kaya tare da matar sa d'aya wacce itama kallo d'aya zaka mata ka tabbatar cewar wannan wata yankice daga cikin bak'ak'en buzayen Niger,adaidai k'ofar gidan ya zauna saman wani banci inda matar sama ta zauna, Detective ne yazo yana fara'a ya tarbesa da cewar ya hanya, dama shi yake jira yau me gadinsa zebar gari yayi tafiya inda me gadin ya fito da kayansa shi kuwa har yana musu sallama iya securities kawai ya bari dama basa zama seda me gadi dayake buzu! Kai tsaye ciki Data ya shiga dashi har zuwa cikin parlor, daga waje kuwa yana d'aga murya akan cewa Maharazu me gadin sazeyi tafiya

"Kayi rana a wannan tafiyar, nizan nuna masa komai karka damu ka tafi abunka kawai,maharazu me gadi se godiya yake kafin yabar wurin.

  Gaba d'aya Hafsa bata cikin walwala amma hakan be hanata shek'ewa da dariya ba ganin Ayatullahi a yanayin sa, zama tayi kusa da Laura sannan tace
Chapter 54 · 0% Book details