← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 71

Sashe 60

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban fahimce kaba? Ta furta har lokacin tana k'ok'arin zame jikinta daga nasa, farcensa me d'auke da k'umba me tsayi ya caka sosai a kuncinta seda tayi k'ara wurin atake ya fashe ya soma jini sannan yakai hannunsa kunkurun sa ya sanya yatsunsa ya caka acikinta ya matse seda ta sunkuya, turata yayi ta fad'i ta buga bayanta akan gado nanma k'arar tayi tare da cewa

"Wayyo Bahar" Dariya yayi kafin yace

"Itama na tura a kasheta, matsala ce wannan tsohuwar arayuwata, zanma iya cewa barazana ce arayuwata, na tabbatar zuwa wannan lokacin an gamamun sa ita, bake wai me basira ba, bakewai kin iya wayau ba, halinki wan nene ban saniba, ko cewa akai dake bansan duk bibiyata da kike ba, bakisan komai ba har yanzu jahilar 'yar sarki, ba abinda kika sani tukunna sena kashe duk zuri'arki zakisan koni waye! A firgice tayi hanyar waje ya rik'o hannunta ta k'wace ya kuma kamota ya cillar akan gado

"Bahar data tsufa dukta rukub'e, idan na kasheta ba rage mata hanya nayi ba, watak'il ma wuta zataje amma inna kashe ta taje aljanna, kinyi kuskuren zurfafa bincike akaina dakin barni kawai da kaina zan karb'i mulkin in barki amma yanzu sena gama dasa miki azaba bayan azaba sannan in turaki rami, Bahar kuma na tura a akashe tsohuwa me diddigi" Mari ta sauke akan kuncin sa

"Kai Jay Barratu cefa da Bahar d'inka, kanka d'aya kuwa? Kodai nace wai bakada hankali ne, shaye shaye ka fara? Mari me gigita duniya ya dire mata

"Ubanki da uwarki nasha ba shaye shaye ba, banza me mugun hali, kina tsammanin zan baro masarauta tane haka kawai inzo nan in zauna sabida ku kuyita ci gaba, wabban mission ne daze zama successfull ko bakay so, dan kuwa anfi shekaru Ashirin da shirin sa,danma na saba da sanki ne, danma na saba da cinki ne, danma kinada dad'i ne Barratu naketajan abun da tsayi dan kawai inta cinki amma dabadan haka ba, aikema da tuni kin zama tarihi" A masife tace

"Idanda kana sona bazakantab'a cutar da ahalina ba Jay, mun maka dukkan adalci akan me zaka butulce mana? Akan meye bazaka duba halaccin muba ka tafi ka barmu babu cuta babu cutarwa, idan wani abu ya samu Bahar wlh sena d'auki fansa akanka" Wata mahauciyar dariya yayi

"Barratu gani kike tamkar duk wata hanya da Hafsa ta d'auraki akai me b'ullewa ce wannan shine babban kuskuren ki a rayuwa, ni banida niyyar cutar daku kamar yanda Sarauniya Maryama takeso, nida so nayi wai inna b'atar da Usman, sena k'arasa yayanki wato sarki bayan haka shi dama Hammood is answerable to me as u know, sena d'are kujerar mulki, ita Maryama dake tunanin in gama wahala tazo inhau mulki amma ina matsayin puppet king, tana mulkana senayi shawarar kaita fadar Sarauni ta huta! Bayan nan ke zaki zama Gimbiya Barratu, Zulaihaty zata Zama Sarauniya Zulaiha shi kuwa Hammood tuni na cire masa sarautar a ransa zance dashi danshi nake komai kinga ze barni na huta, Bahar idan taso kawomun wargi ita soma nayi in d'auketa daga kusa damu zuwa bayan masarauta kinga nayiwa kowa adalci kenan ko? Amma ke sabida dak'ik'iyace ke bakida wayau seya zamana kin biyewa waccen Hafsat kunata kawomun wargi gaba d'aya kunbi duk inda nakawo ku toshe, a tsammaninki bansan kina yawon neman duk wani sirri nawa ba, namiki shirune san ayanda nasan kwanyarki bataja nayi tsammanin bazaki gane komai ba se yanzu na fahimci kuskurena, dan kuwa na fahimci Hafsat itace take jujjuya kanki yanzu, ita kuma kaine da ita shegiya tamkar itace ta halicci kanta" Haryakai k'arshen maganar sa idansa na kanta tana hawayen bak'in ciki tace

"Honey dan Allah ka canja, dan Allah honey ka dawo kamar Honey Jay d'ina nada, ka sanar dani bakai bane wannan kace dani komai wasa ne ko mafarki nake kaji? Wayarsa ce tayi k'ara ya dena kallonta ya janyo wayar daga aljihun sa sannan ya kara kunne ya saisaita muryarsa, Bahar ce dan haka cikin girmamawa ya gaisheta tace

"Kuzo Fada kaida Barratu babu lafiya, daga mab'oyar daka kaimu anje harcen an kashe Sarki, nima da k'yar nasha wlh, yanzu haka harsashi seda yabi ta gefen hannuna ya wuce seda akamun dressing, muna cikin matsala Jay, kai kad'ai ka rage mana" Cikin Tashin hankalin k'arya yace

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, me sukawa sarkin Bahar? Tana kuka tace

"Hatsashi suka d'ana masa a k'ahon zuci, gaba d'aya da tsaro me yawa mukazo fada ka kirawo Hammood a waya tin jiya be dawo ba, ni kirashi be d'aga kiranba" yana kuka yace

"Gamunan zuwa Bahar, Allah ya isanmu" Ya katse kiran tare dayin dariya yace yana kallon Barratu

"Hajiya Bahar ta kub'uta amma yayanki ya zama tarihi, abinda nakeso dake shine kokiyi shiru tamkar bakiji bakuma kisan komai ba a kaima kokuma wlh insaka a kashe Bahar, karki Kuskura koda Hamood ne ya gano wai wani halin nawa dabe saniba, ki zab'a rayuwar raggan uwarki ko rufe wannan abin dakika sani, kindai ga ko yanzu yayanki na kasheshi kai tsaye" Tana k'wallah tace

"Koma me zakayi kayi amma abu biyu nake rokon alfarma awurinka, na farko babu ruwanka da mahaifiyata ka barmun ita a raye har lokacin ta yayi, na biyu kuma.babu ruwanka da rayuwar Hammood ka barmunshi a raye, Mulki kuma idan har zaka bani matsayin Sarauniya inhau babban matsayi ka barni in rayu dakai kakuma bani dama in haihu namaka alk'awarin zamma taimakeka ta hanyar d'aurawa Hafsa manyan laifukan dazata barnan araunace yanda bazatayi marmarin waiwayarmu ba har abada,shikuwa Hammood zamu nuna masa be isa mulki ba se zuwa gaba kad'an! Kallonta yake cikin ido sosai yanaso ya gano gaskiyar zancenta a idanta kuma tabbas daga zuciyarta take furta kalaman cikin tsananin mamaki yace

"Bakiji kin tsaneni ba akan kashe yayanki danasa akayi? Share hawayen idanta tayi

"Banso ace kana kisaba Jay ina tsananin sonka bazan iya rayuwa in babu kai ba, amma kuma banaji kaine ka kashe yaya Tahir, gawar daba takaba kawai ka k'arasar amma naji tsananin ciwo jay, mesa zakayi tunanin ashe Bahar bayan duk tsananin son danake maka, da tun farko kace dani Mulkin kakeso.da tuni munyi yadda zamuyi Yaya Tahir ya baka kujerar" kallonta yake tabbas Barratu tana sonsa kuma zata iyayin komai akan sa, amma be zata abun yakai haka ba, cikin jimami yace

"Kiyi hak'uri hak'uri Barratu, banaji bana gani, bazan yafewa koma waye ze hanani isa akan mulki ba ciki kuwa hadda ke, dan haka yanzu ya zakiyiwa Hafsa" Murmushi tayi me ciwo

"Zan d'aura alhakin kashe yaya Tahir awuyan Hafsa, tunda ba'a kama makasan ba, zamu tilastawa d'aya daga cikinsu zuwa yace shine yayi kisan kuma Hafsa ce ta turasa, amma zamuyi arranging yanda zamu kamashi, inyaso semu bashi kamar 5.m seya confessing bayan an kamashi zamu masa dabara ya kub'uta, kaga Hammood tukunna besan komai akanka bare yayi bincike" kallonta yayi

"Amma kina ganin bata fad'a masa ba, sunafa tare tun jiya" B'ata fuska tayi kad'an

"Bazata fad'a ba dan bance ta fad'a ba, tin dama cen nace ta tufawa mijina asiri kaine dai baka sona" Rarrashinta ya somayi akan tayi hak'uri tare da neman yafiyar abinda yayiwa Yayanta Tahir! Nan tayita kukan mutuwar yayanta tace dashi tabbas dabadan shi bane seta tona masa asiri amma girman soyayyar datake masa baze bata damar yin hakan ba" Jay Se murna yake yayi nasara haka suka d'unguma fada...Jay yanata k'ok'arin kiran Hammood ya sanar masa mahaifinsa ya mutu yayi hanzarin zuwa amma wayar bata tafiya.

Gamu gani dai idan tusa zata hura wuta!!!

"Mom Nu'aiym.

   *TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA TALATIN DA UKU*

33.

  Kallon Hammood Bahar tayi yanda yake sauke numfashi sannan tace "kwantar da hankalinka zakayi na musu waya kamar yanda kace, kuma suna kan hanyar zuwa nan, idan yazo base muji daga bakin saba, na fad'a masa Tahir ya mutu kamar yanda  kowa yaji a fada bari yazo muji da wacce zezo kuma gaba d'aya na kasa aminta Jay ze cutar damu, nasan zuciyar sa ta rashin imani tun yana k'arami amma wlh na d'auka cewar Jay ze dena wannan mugun halin, nayi tsammanin irin tarbiyar dana baiwa Jay ta sanya rayuwarsa da tunanin sa komawa irin na mutanen kirki, ban zata cewar shahararren mugu bane ba" Cikin raunin Murya yace

"Banshirya tarbar wannan ranar ba Bahar, ban shiryawa aminta da wannan cin zarafin ba Bahar, gaba d'aya duniyata ta shiga d'imauta, ace wai Jay ne da kansa zeyi hayar mutanen dazasu kasheni Sarki, su kasheni har dake me muka masa? Sumar kansa ta shafa cikin kulawa

"Ka rabu da mutum Hammude, ka dena biyewa salihar zuciyar ka tuni dama cen Jay la'ananne  ninasan halin sa, tsammani nayi ya sanja, sabida daidai gwargwadon tarbiya na baiwa Jay ita, na tsaya tsayin daka seda naga ya dena nuna yawan sonkan nan dayake, dacin zali, yaudarar mu yayi ashe, niya mayar tsohuwar kawai" Runtse Ido Hammude yayi kafin ya bud'esu ahankali akan Hafsa sannan yace

"Ke bazaki ci abincin bane, kizo kusa dani ki zauna" kawar da kanta tayi sannan ta turo baki

"Bazan ciba, gidan momy zan tafi da wancen yazo an kamashi, kaji dai abinda ake shirin musu" Kallonta khairiyya tayi"wace momyn? Ta tambaya a tak'aice

"Momyna mana, tana cikin wani yanayi" Cikin takaici khairiyya tace

"Ke tsintacciyar mage har wata mommy c3 dake, ki dena alak'anta uwata da kanki dab bakuda wani had'i na jini, yarinya kin shigo rayuwata kinbi kin tattare komai kin k'wacemun, mijina mahaifiyata, dangin mijina gaba d'aya farin cikina ya dawo naki wlh senaga bayanki" K'ank'ance ido tayi tana me zubesu akan khairiyya sannan tace

"Baiwar Allah matsalarki ta farko itace mijinki, tuni ya sakeni saki uku sabida haka matsalar farkon ta kau, ta biyun itace dangin mijinki wannan kuma mune danni k'anwar sace ke baki isa ki karkare wannan ba, se matsala ta uku shine Momy kije da kanki ki sanar mata ta dena kirana 'yarta idan kin isa" Bahar ce cikin mamaki ta kalleta

"Kanki d'aya kuwa? Magana kike akan Hammude ya miki saki uku, wannan ai rainin hankali ne, a gidan wane la'anannen akayi haka bana nan? Sosa kai tayi
Chapter 60 · 0% Book details