← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 71

Sashe 46

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"My friend will you do just as i say? Gyaran zaman rigarsa yayi jikinsa yana rawa sannan ya shiga gaba Hammood yabishi a baya ko ina seda suka shiga beganta ba, rik'e bakin sa yayi sannan ya juya da zummar barin gidan amma me freezer dake gefensa seta motsa kallon me gadin yayi daya gama cewa gidan duk datti ne ko ina fesfes yace

"Bani ruwa a wannan freezer nasha" Jikin me gadin yana rawa ya kuma cewa

"Ai basa amfani da ita yallab'ai sedai wancen fridge d'in" Hannu yakai ze bud'e danyaganta a kunne amma me se me gadin yayi azamar rik'o hannunsa d'agowa yayi suka kalli juna jikin me gadin dukda yanda yake mazari hakan be bashi damar sake hannun ba, jijiyar me gadin ta wuya me taken mukwana lafiya Hammood ya kalla sannan yayi wani malalacin murmushi sekuma ya daddage yakai mata wani lafiyayyen sara da gefen hannun sa, take agun me gadin ya zube a sume, shi kuwa ya bud'e deep freezer d'inda har lokacin bata dena motsi ba, da sauri yaja baya ganin mitum ga dakakken yaji a barbad'a ako ina shi kanshi yana bud'ewa sanyin k'ank'arewar datayi tare da tashin hayak'in yaji ya daki hancin sa abinda yayi saurin sanyashi atushawa, seda ya matsa sosai sannan ya kuma dubawa tabbas yaribyar d'azu ce ko mata zece be gane komai ba se kayan jikin ta, da azama ya cicib'ota, ab daire hannunta da k'afafuwanta a had'e ankuma tura mata wani abu a baki, abin bakin nata ya soma zarewa kafin take ta soma atishawa tana ruwan k'walla sannan ya warware hannunta da k'afa be b'ata lokaci ba yabar gidan baya ya sakata a mota, abinda yafi bashi mamaki shine dayawa daga cikin yaran daya wurga wayoyin su a mota basa nan, sun gudu kenan kome? Asibiti ya nufa da ita yana k'are mata kallo, ko shakka bayayi yanayin yanda zuciyar sa ke bugawa akan Hafsat yasan yanxu kam itace, tome ya kaita? Meye nata na zuwa ta wannan matakin, sanda suka asibiti tama fita a hayyacin ta, k'afafunta ya kalla da hannayenta atake ya k'ara tabbatar da zargin sa akan Hafsat ce, dake private hospital kuma sun masa farin sani hakan ya sanya dashi suka shiga bata taimakon gaggawa, gaba d'aya sanyin k'ank'ara ya gama da lafiyar ta, ta kwashe sama da sa'o'i hud'u acikin freezer me azabar sanyi da yattafin yajin barkono, mamaki yake yanda aketa yaga kayan dake jikinta da almakashi se yagawa ake basa k'arewa lallai yarinyar nan batada bankali, meya kaita? Haka har ta dawo iya pant be da bra ajikin ta, kallon likitan yayi yana yamutsa fuska kafin tace

"Dr. Ba wani privacy cover her body please" kallon sa likitan yayi

"Yanzu zamu rufe ta karka damu" yana nan tsaue har suka sanya wani blue zani suka rufe ta, anan suka shiga dudduba ta kayan data tulawa jikinta sun taimaka wurin hanawa sanyin freezer shiga jikinta sosai amma idanta da mak'oshinta da komai ma ya gama shiga azabar sanyin da turirin yajin wannan ya sanya gaba d'aya wata azababbiyar mura ta taso mata ta lokaci guda tasamu taimako dai, an shafa mata mayukan rage azaba sabida zafin d'aurin datasha sannan akayi mata abinda ya dace tukunna sukace bazasu sallameta ba se zuwa safiya idan sunga dacewar hakan shima!

Wayar sa ya zaro ya kira Uncle Jay wanda yana d'auka yace dashi

"Mesa zaka sanya ta irin wannan aikin? Akan me duk a cikin mutane masu wayau da girman shekaru se ita kad'ai" Nisawa Uncle Jay yayi danyaso hana faruwar abinda ya samu hafsat amma besan ya akayi sukayi outsmarting nashi ba akanta

"Hammood magana ce wannan me tsayi bazatayiyu a phone ba ka bari idan mun had'u" Cikin takaici yace

"Your crossing the line Uncle Jay, she's my wife remember? Yaya zaka sakata aikin dani mijinta na kasayi? Kasan me suka mata yanzu? Nisawa Uncle Jay yayi cikin jimami

"I hope she's now safe" Tsaki gajere Hammood yayi kafin yace

"She's not and please count her out of this bullsh****t" Nisawa Jay yayi

"Ka saurareni mana Mood bawai da wani niyyan na sakata ba kawai naga ka d'aura zargi ne akanta shine nakeso nayi diggin meke k'asa ta b'angaren ta, am just trying to proove her innocence"

"What ever" ya furta sannan ya kashe wayar sa ya juya yana kallon ta, kowama indai akace sarauta ne kowa kansa hayak'i yake, meye wannan 'yar tatsutsuwar ta sani, wama yasan kalan shirmen dazata kwab'a idan ba sonkai ba kawai aikin da manya ma basuyi ba se ita taje tayi. Wayar sace ya kuma yin k'ara ya d'akko Uncle jay ne bayaso ya masa rashin kunya dan harga Allah ya shafe shekaru yana masa biyayya, ya gaza gane inda ya dosa akan harkar nan, me suka isa su masa idan sun gane yana maganar daze takurashi ya hanashi yi, lokaci yayi daze yiwa tufkar hanci tunda har aka soma had'awa da Hafsat abin ya zama jin dad'i ma kenan, zama yayi akusa da ita fatar fuskarta dake fara tayi kaman jikin gawa sabida sanyi daya dazk'arar da jini yayi bak'i, yanzu kam bacci take tana sauke numfashi a hankali, wacece Hafsat? Menene ainahin musababbin zuwanta a rayuwar sa, ya sani Hafsat bata kunya ko kad'an tanada tsiwa da sakin magaba yanda duk taso amma she's very honest, sam bata tsoron fad'ar gaskiyar komai d'acin ta, mesa yake zargin ta amma hakan baya rasa nasaba dak'in kareshi datayi da zargin da ake masa akanta tun farko, wayarsace ta kuma k'ara a karo na uku kuma duk Uncle Jay ne, d'aga wayar yayi yanxu kam amma beyi magana ba, Uncle Jay cikin mutuwar jiki yace

"Bani bane na sakata wannan aikin, Bahar ce da Maminka, naso in d'auki wannan blame d'in amma banaso yarda da amincin dake tsakanina dakai ya watse akan hakan, nayi k'ok'arin nusar dasu kuskuren yin hakan amma Mami ta kafe akan Hafsat zata iya tono sirrin b'oye ni me zanyi? Cikin tsananin b'acin rai yace

"Uncle daka sanar dani akan hakan, tasha wuya a hannuna, duka, mari,tsangwama dik akan ina zarginta, dakun sanar dani sena taimake ta" Yana gyaran murya yace "Hammood baka taimaki kanka ba akan mak'iyan ka kake tsammanin zaka taimaki macen dake shirin taimakon ka, kai bazaka iyaba ai" Tunawa yayi da kalmomin ta "Ur a coward!! Tabbas abinda kowa ke kallon sa kenan ciki hadda uncle jay

"But Uncle kaida kake cikin su meka tsinana? All these years ka taimakeni ne? Cikin jin zafin sa yace

"Nida kai duk d'ayane bazamu iya yin komai ba akan wannan abun" Dafe kansa yayi

"Fine then ku barsu su kasheni saime, amma dai wannan 'yar alhakin a zareta a wannan maganar zan gayawa ummi, kuma ka sanar a masarauta a taramun duk manyan fada daduk wanda ya dace ya sani inada magana da dukkansu gobe" cikin sauri yace

"Me kake shirin yi?

"Magana" ya bashi amsa a tak'aice

"Wace iri? A masife yace

"Da baki uncle irin wacce nakeyi dakai yanzu a wayar nan, gobe iwar haka kowa a duniyar Daulatul dinar ze tabbatar wa kansa harshen Hammood ba tattaura bane yana motsawa" Nisawa Jay yayi

"Son please calm down, yanzu gayamun me sukawa Hafsatun" kallon fuskarta yayi sabban yace

"Kasheta sukayi" yana kaiwa nan ya kashe wayar sa ya kira Barra, tana d'agawa yace

"Ki gayawa Bahar Hafsat tana wurina karta nemeta a yau, har mami ma"

"Kawun kane yace ka somayin magana da mutane? So yayi ya gaya mata magana amma kuma seya fasa kawai yace

"Bashi bane kamawa tayi"

"Daka aikon message kawai ai" Bece komai ba ya datse kiran yaje ya kuma rik'e hannun Hafsat yana mata wani kallon dabesan ma'anar saba.

****************
Aminulla kuwa yayita neman wancen layin dasuke waya amma be samu ba, wannan ya sanya gaba d'aya hankalin sa ta tashi, gashi dai komai datace yayi ya kammala amma baya samun wayarta, da wannan ya yanke shawarar kawai ya adana mata sirrinta har sanda tazo wannan itace amana, koda yake har yanzu hoton yarinyar da masu napep suka d'auke a bakin hotel d'in suna masa gizo, seyake ga kamar itace tayi basaja...........

Asaman kujera ya kwana yana rik'e da hannun ta, babu kiran da khairiyya batai masa dole ta hak'ura sabida dama tunda suka dawo basa kwana wuri d'aya sedai yakan zo idan yana buk'atar hakk'in sa daganan ya koma, ta masa magana yace tradition d'in kenan, tarasa gane wanne mahaukacin tradition ne wannan daze nesantata da mijinta, wuraren k'arfe hud'u hafsat ta farka da sambatun ta

"Karku sakani a freezer, sanyi baya bani lafiya kuyi hak'uri" daganan ta tuna sanda aka tura mata wani abu a baki kawai seta mik'e zaune a zabure, da sauri ya farka ya rik'eta dama be kashe fitilan d'akin ba, waige waige ta somayi kafin da azama taja baya a tana rirrike bargon daya rufeta dashi, matsawa yayi har saman gadon ya k'ara rik'ota

"Hafsah" ya furta yaba d'aura kanta asaman k'irjin sa

"Calm down ur safe now, ina tare dake ba abinda ze sameki" kallon sa tayi tana k'ok'arin yin magana attishawa ya taso mata gaba d'aya tayi ajere ajere yakai so goma sannan ta nemi langwab'ar dakai cikeda tsoro

"Wurin Bahar zaka kaini, sunce kasheni zasuyi, kuma ina abubuwana, banga wayana bafa, ina mayafina? Kallon ta yake

"Keda bakida lafiya me zakiyi da wad'annan abubuwan? Rik'o hannun sa tayi

"Wannan ne lokacin danake gaf da cimawa Bahar burinta, ka taimakeni ka baki wayana da mayafina akwai abu me muhimmanci a bayan mayafin nan nawa dan Allah karka hanani" Tausayinta yaji wato shi takeso ta k'watowa 'yancin sa amma yaketa shirme akaron banza, rungumarta sosai yayi sannan yace

"Hafsat calm down naga jakar hannunki a inda na d'akkoki, nakuma d'auka miki, wayarki yana ciki, but banga mayafin kiba nidai" Tana dube dube tace "That is the most important thing ai, shi mayafin sa abayan sa akwai abun amfani ka bani wayar zan kira Aminu" Agogon wayarsa ya kalla

"K'arfe hud'u da kwata na asuba, bazan bari ki kira kowaba a wannan daren, ki bari gari ya waye, kanki yana ciwone? Kokuma kinajin yunwa" kwantar da kanta tayi akan k'irjinsa

"Menake anan to?
Chapter 46 · 0% Book details