← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 71

Sashe 48

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan aikin aikine me hatsarin gaske yallab'ai, musamman da yake shi Hammood d'in a kafad'a aka same shi, dama ace irin acikine, mara ko wani wurin dakai tsaye mutum ze iya shek'awa lahira, amma magana ta gaskia a yanzu kowama ze iya zargin komai idan akace yau ya mutu, koda ni na yarda da aikinka zan kasheshi amma sauran abokan aikina zasu iya fallasaka koma suk'i amincewa dani anan gaba" Cikin takaici yace

"Kai yanzu a shekaru nawa zaka tara miliyan talatin, bawai harkace ta tsiya bafa, akan rai d'aya ko'a busa kuskure ne ai zaka iya k'arasashi, kawai ni ina ganin bakason yin aikin ne, nikoda ubansa banaso ya mutu a yanzu shine banason rayuwar sa kwata kwata" Cire madubin ido Dr. Yayi "Ranka ya dad'e dama zaka bamu 50.m ne amma meye wani 30.M yayi kad'an gaskia, sannan dama tsohon kakeso a gangarar shida aka sama a ciki sannan ga shekarun tsufa amma dukkansu dakake gani indai ba wani ikon Allah ba zasu rayu gaskia" Cikin k'ufula Baba Usman yace

"Ka had'a dukkansu uku ka kashe zan baka miliyan d'ari" Mik'ewa likitan yayi kafin yace

"In that case zanyi musu alluran wani poison inyaso zan gayawa duniya acikin harsashin da aka harbesu dashi akwai Poison me dafi dan haka duk sun amma seka zube 75% na deal namu a acc na wani k'anina dan bazan bada nawa ba zargi ze shiga bayan nan idan mun kammala seka bayarda sauran kud'in" Hannu ya baiwa likitam yana mik'ewa

"Very nice of you babban likita, idan kayimun haka bawai 100.M ba hadda wani taimako zan maka ka k'ara gaba daga nan asibitin kuma zan baka kyautar gida da mota duk dan ka huta" Likita yana washe baki ya hau godiya sannan ya hau shirin sa na aiwatar da abinda aka sanyashi.

*****************
Aminullah a asibiti ya sameta suka lab'e acen bayan wata itaciya ya bata duk abinda ya samu har videos da kuma Atom recoder daya mak'ale ta kwaso duk abinda suke tattaunawa a wannan lokacin, kai tsaye wurin d'akin Dr taje ta zaro wannan tazo ta shirya komai ta nemi wuri ta nutsu domin saurararsu sedai bata ko kunna na farko ba aka aiko akan tazo an kama wanda sukayi harbi" Tayi sa'a dama ta kira Masscom yana xuwa ta mik'a masa komai akan bata saurara ba tukunna sannan tace ya mata sending duka ta whatsapp zasuyi waya daga baya yanxu hankalinta ba'a kwance yake ba. Suna zaune ita da Aunty Barra suna tattauma matsalar akan har yanzu ba'a shiga aiki dasu Takawa ba acire musu wannan harsashin har sha biyu ya gota an rasa me likitocin da Baba usman suke nufi kawai sega police hadda soja da wasu matasa, abinsa yafi bata mamaki shine hadda Aminullah a yaran da aka gabatar akan cewar wai sune maharban! Ganinnsa ba k'aramin tsoratar da ita yayiba wanda hakan ya sanya ta mugun tsorata har tsoron yafito a sarari bawai tsoron tonuwar asirin tayi wani laifin na tsoron ta baiwa Aminu dama, ido suka had'a da Usman yayi mata wani kyakyawan kallo tare da sakar mata wani malalacin murmushi atake k'irjinta ya kuma dokawa seda Barra ta rik'e hannunta tace murya k'asa k'asa

"Hafsa lafiya dai? Kafin ta bata amsa Baba usman yace

"Munje fada duk kunce babu ita aciki nan kuma fa? Wani daga cikin su ya nuna Hafsat, yace "Wannan ce ta sakamu, kuma itace ta kai mana bundigogi guda biyu" kallon mamaki tayi masa kafin ta kalli Barra datayi hanzarin sakin hannun ta tana k'ank'ance ido akanta, d'ayan ma yana kallonta yace

"Haba Barde, amma kasan mun mata alk'awarin ko za'a kashemu bazamu tab'a tona mata asiri bako? Kan kowa awurin d'aurewa yayi ciki hatta Bahar, baba usman yace

"Ohhh shiyasa gaba d'aya Hammood be yarda da yarinyar nan ba, koda wane lokaci maganar sa d'ayace akan tazone ta cutar dashi, yarinya k'arama se rashin imani shegiya dagani bayin kanta bane wasu ne suka sakata kuma wlh kashinki ya bushe tsinanniya" ya k'arashe maganar yana sauke mata mari, yace yana kallon Barra

"Ai dole daya farfad'o ya saketa, dan bazakije gidan yari ko lahira da igiyar auren wanda kike neman ransa ba, Allah yayiwa wad'an nan jami'an tsaron albarka, shi wannan Allah ne ya kamashi dayazo wurinta har cikin asibitin nan karb'ar balance d'insa ashe police suna kalle damu dakuma wa muke hurd'a dasu, har hotel d'in mararraba taje tayo hayarsa shine yake bibiyar al'amuran Hammood din dan haka badashi akayi harbi ba, kafin muzo nan a CCTV na hotel d'in an gansu a tsaye suna magana a d'aki, munafukar har siffarta take sauyawa in zata k'ulla ta'asa" Bahar jiri ne ya d'ebeta bazata tab'a iya gaskata wannan maganar ba har abada, Barra kuwa seja da baya take yayinda momy ta saka kukan tausayin 'yarta, khairiyya se murna take zata rabu da hafsa na har abada!!! Ita kuwa gaba d'aya komai ya tsaya mata cak! Bata fahimtar komai se kallon kowa takeyi da ido tarasa a ina duniyarta take shirin kaita a wannan mugun mafarkin? Haka aka tasata a gaba se tura k'eyarta akeyi tamkar wata 'yar ta'adda. Baba Usman se masifa takeyi akan iyashegen ta "Duk uban daya turoki wlh sekinyi bayani, nasan wasu mak'iyin d'an uwanane suka turoki, gunduwa gunduwa zanyi da naman jikin ki shegiya me sifar aljanun farkon duniya!

Likita kuwa ya gama tsara duk abinda zeyi harya had'a wasu azzaluman likitoci irin sa, sun gama yanke shawarar su shiga dasu aiki su fara ciro bullet din bayan sun ciro su fara sakawa bullet d'in poison sannan sesu samesu a ward bayan k'afa ta d'auke su k'addamar musu da wannan shawarar suka shiga cire bullet d'in sannan aka mayar dasu ward.

*Kuyi Hak'uri da wannan na cika alk'awarine kawai amma inada patient ga Oga kunsan yau weekends ne, a matse da wannan*

*Mom Nu'aiym.*

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*INA 'YAN KASUWA WANDA SUKA SHAHAR SUKE KUMA SON SU K'ARA SHAHARA TA FANNIN KASUWANCIN SU? TOKU GARZAYO NESA TAZO KUSA,DOMIN MUN SHIRYA TSAF DOMIN TALLATA MUKU HAJAJOJINKU AKAN FARASHI ME SAUK'I TA HANYOYI SADA ZUMUNTA NA YANAR GIZO DABAN DABAN AKAN FARASHI ME SAUK'I, NEMI WANNAN LAMBAR DON K'ARIN BAYANI..07084161619.

*Miss Hindu wannan shafin nakine, nani dad'in yanda kike nuna tsananin k'aunar ki agareni, Allah yabar zumunci*

*SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR*

25.
   Lokacin da likitoci sukazo d'akin da Hammood yake se suka tarar baya nan, abin ya matuk'ar d'aure musu kansu, gaba d'aya sun rasa tunanin ina zeje, har toilet sun duba baya nan, likitan cikin tashin hankali yace

"To ina zeje? Shida yakeda rauni? Yaushe ma allurar baccin ta sake sa? Karmu b'ata lokaci anan mu duba sauran patient d'in, Dr. Anwar kai seka duba mana patient relatives d'in kaji inda yaje" Juyawa yayi sukuma sauran likitocin suka juya d'akin me martaba nanma bayanan, hankali atashe suka juya d'akin Muhseen nanma bayanan, tashin hankali wanda ba'a saka masa rana! Dr. Gaba d'aya jikinsa rawa ya d'auka ya rasa inama ze saka kansa, tomeke shirin faruwa? Idandai ba wani abu sukaji ba tayaya zasu bar asibiti acikin sirri kuma ba tare da kowa ya gansu ba? Kai tsaye office d'insa ya nufa ya d'auki waya ya kira Baba usman bayan sun gaisa yace

"Yallab'ai akwai matsala fa? Cikin tashin hankali Baba Usman yace "Matsala fa, Wacce iri kenan?"

"Gabaki d'aya munje muyi aikin allurar nan kamar yanda muka alk'awaranta dakai amma semuka tarar duk patient basa d'akunan su, kuma patient relatives sunce basusan yaushe suka fita ba, abun akwai matuk'ar d'aure kai" Cikin tashin hankali da d'aure kai  yace

"Wannan wace irin magana ce? Sekace wasu cinnaku ka gayamun duk baka gansu ba wannan maganar ai zancen wofi ne" Zufa Dr. Ya share sannan yace

"Maganar gaskia kazo da kanka ka tuntub'i relatives naku da kuka bari dakuma wannan fadawan da dogarawan, danni gaskia zan iya mayar ma da kud'ad'enka akan in shiga wata fitinar" Cikin masifa yace

"Deal.ya rigada ya k'ullu likita, zanzo inji inda suka tafi dai amma maganar mayar da kud'i batama taso ba, shin ku bakuda CCTV a d'akunan kwananku ne da waje? Cikin k'aguwa likitan yace

"Bamudasu, a main gate ne kawai akwai" Tsaki k'arami yaja kafin yace

"K'aramin asibiti kukeda kenan ba babba ba, bansan mesa me martaba yake zuwa asibitin kuba, koda yake dak'ik'in gaske ne shima" katse kiran likitan yayi kafin yace shi kad'ai

"Wannan mutumin inaga lauye aniyar sa zanyi, ban tab'a kisaba dama, inaga Allah ne ya taimakeni danya tseratar da rayuwarta daga fad'awa halaka, sabida aniyarsa ce zansa tabisa, wanda dik ze iya sanadin jininsa har haka tokuwa tabbas a dubawa rashin imanin sa"

*****************
   A station gaba d'aya hafsat be kawo wuta seda ta shafe kusan awa biyu a cell tana nazari kafin azo interogeting d'inta!!! Mutumin gaba d'aya wani irin mutum ne me tsananin cikar kamala da haiba, kana ganin sa zaka tabbatar wa kanka cewar wannan a k'ware a harkar sa, beyi mata kama da police officer me kaki ba sedai ko d'an sandan ciki ne, cikin dak'ik'a dabefi biyar ba ta gama karantar yanayin sa, katse tunanin ta yayi da cewar

"Sunana Sifeta Sufyan amma anfi sanina da Data, nazone in miki wasu 'yan tak'aitaccin tambayoyi akan wannan al'amarin daya faru, duba da yanayin shekarunki na tabbatar sakaki akayi" Murmushi kad'an tayi sannan tace

"Bazan baka amsa ko d'aya ba a yanzu malam Data, duba da yanayin shekarunka da wayewar ka na tabbatar kaiba jahili bane ba, dagani kuma koban tambaya ba na tabbatar cewar kai d'in nan kasan aikinka fiyeda tunanin me tunani, dan haka anan taimako d'aya zan maka sabida bazanso kasha wahala ba, ba wani taimako bane me wahala, da Farko.zan baka lambar wani wanda xe taimakeka ka samu amsar tambayoyin ka acikin sauk'i, kokuma zan baka dama ka gayyatoshi ayi komai agabana, na biyun sa kuma zan baka wani assighnment idan kaje kayi shima ze taimake ka" Langwab'ar da kansa yayi yana mamakin yarinyar kafin yace

"To Malama Hafsah ina saurarenki" murmushi tayi kafin tace
Chapter 48 · 0% Book details