← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 71

Sashe 47

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki dena yawan surutu bakiji muryanki ba,mura ya kamaki da yawa" Wani yanayi yakeji mara misaltuwa, gaba d'aya jikinsa se k'aryata sa yake a wannan yanayin, jan jikinta tafarayi tanaso ta raba jikinta da nasa ta kula so yake ya soma sha'awar zama awurin, da sauri ya ya sake maidata k'irjinsa

"Hafsah please, stay still" Kasa yi masa musu tayi, why is he so cool today?he's acting so wired, is this real or is she dreaming? Ta tambayi kanta, lafewa tayi na wani lokaci seda yagaji dan kansa yace

"Mesa kika zab'i yin wannan aikin sayar daran? Am not even worth it, mesa zakimun irin wannan sadaukarwar" Janye kanta tayi suka kalli juna sannan tace

"Wanne irin aiki kake magana kenan? Ni in sayar daraina akanka? EHM Allah ya kiyaye" Murmushi yayi, she's still rude kodatake fama da kanta

"Sanda Bahar da Mamina suka sakaki mesa ke baki gaya munba" Yanzukam gaba d'aya tureshi tayi daga jikinta

"Ni bansan abinda kake magana akai ba" Allah sarki, wato dai bazata fallasa sirrin data d'aukarwa iyayen saba akan taimakon sa, lallai yanzu ya dace ya shirya ya d'auki d'amarar sanin wacece Hafsat donya saka mata da mafificin abinda tamar dukda bawai 100% zuciyarsa ta gama nutsuwa da itaba, mik'ewa yayi

"Zanje gida a babban masallacin fada nakeso inyi salla tare da sarki" batace masa komai ba harya wuce yabar d'akin, wayarta ta janyo akan gadon asibitin datake kwance bata fasa aikata abinda tasa agababa!!
Ganin ya fita yabar cikin d'akin ya sanya wad'anda dama fitarsa suke jira sukayi hanyar waje domin dawowa tare da wad'ansa ake jiran suzo domin gamawa da rayuwar Hafsat gaba d'aya kafin shima ya koma fad'a ya tarar da ajalinsa, tunda yaji sirrinsu bazasu barshi ya kara rayuwar koda 1 second bane har itama........Abin mamaki yau a babban masallacin fada Hammood ne ya bada sallah dakansa, inda mutane da dama sun ganshi yana bada sallan, be fitoba seda haske ya bud'e ko ina lokacin ya gama azkhar d'insa, tare suka jeru da muhseen daya masa dirar mikiya sabida yanayin dayaji muryan sa jiya dasuke waya wuraren 12 na dare, suna tsakiya da tafiya kawai sautin bindiga sukaji wanda atake suka zube k'asa atare shida muhseen, mutanen dasuke wurin kuwa wasu suma tsere wasu kuwa sukayo kan muhseen da kuma Hammood ciki kuwa hadda sarki, kafin wani yunk'uri se tashin wani harsashi sukaji atake sarki ya zube awurin shima!!!

*Readers kumun uzuri, yara nata fama wlh musamman Nu'aiym, ga kuma yanayin abubuwa, book yana gangarewa zamuce baze wuce mu 40pages dududu to mucigaba da hak'uri, wamda suka kira Nu'aiym da ayaan suna godiya sosai, nima ima godiya Allah yabar zumunci.

*Mom Nu'aiym.*

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA HUD'U*
24.
Lokacin da Hammood ya fita gaba d'aya se hankalin Hafsat yak'i kwanciya, wanda suka mata abinda suka mata bazasu tab'a barin taba, wama ya sani ko dama dakun jiran suke ya tashi a wurin su far mata, da sauri ta nemi abayar ta ta zura ta d'auki jakar ta, k'arewa d'akin kallo tayi kawai taje ta murza key ta rufeshi ata ciki sannan seta fita ta window lokacin banda tari da attishawa babu abinda take, ta jima sosai a wani wuri cikin asibitin seda haske asuba ya soma washewa sannan ta fito titi, batasha wahalar samun abun hawa ba kai tsaye gidan momy ta wuce, Baba me gadi jin kmocking ba k'aramin mamaki ya bashi ba, amma a haka ya taso yazo ya bud'e mata ya kafeta da ido duk ta fita a hayyacin ta

"Hafsou kece da asubar fari, lafiya kuwa? Kafin ta bashi amsa ata bayanta kawai aka rotsa mata wani abu akai dayasa kai tsaye ta fad'o ajikin baba me gadi a sume, da sauri ya ajiyeta a k'asa yabi bayan wanda sukazo, sandar da dama da ita yazo bud'e gate d'in ya saita ya wurgawa wanda ya daketa, sannan cikin azama ya zaro wuk'a saga kunkurunsa ya kuma saitawa ya wurgawa d'ayan a kafad'a segasu zube gaba d'aya a kwance da gudunsa ya k'arasa yaje ya janyosu yazo ya d'auresu acikin gidan sannan ya kira momy

"Baba lafiya dai? Kallon ta yayi

"Wasune suka biyo bayan Hafsou bansan daga ina suke ba da wannan sanyin asubar ba, nayi nasarar saita d'aya da wuk'ar lak'ani, na kuma jefe d'aya da sandar lak'ani" cikin tashin hankalintace

"Inji ita Hafsat ba abinda ya same ta" Da hannu ya nunata a kwance

"Gatacen ya mata sanda akai, amma kizo ki kamata sena mata turare tas zata mik'e" Jiki na rawa momy ta fito tazo ita da masu aikin ta suka kama Hafsat sannan sukayi ciki da ita Baba yazo da garwasu a tray ya bad'ad'e kanta da hayaki take ta soma shak'uwa segashi ta dawo a mutum sak, dukda kanta yana mata ciwo, momy har kuwa seda tayi, idan masifar dake wannan masarautar takai haka akan Hafsat yaya khairiyya take? Inama zata saurareta? Inama zata tarbi uzurinta su tallafi maraicin juna, Bilal ya sakko tun zuwansa Nigeria amma ita sam se k'ara d'aukar zafi take da ita, Hafsat se zazzare ido take tace

"Momy bazan zauna a gidan nan ba, dole zan koma masarauta idan bacen ba babu inda nakeda tsaro, ta raina ake momy kar masifar dana janyowa kaina ta shafeki" Baba me gadi ne yace

"Anan gidan dai, banda k'arfin ikon Allah babu wanda ya isa yazo yace xe tab'aki, wancen yaron ma na zare wuk'ar jikinsa na shafa masa maganin tsayar da jini, seyayi bayani tiryan tiryan waye ya aikoshi dan bazan masa lamuni ba" Jinjina kai momy tayi, dukda haka zanwa Daddyn muhseen magana ya turo mana motar mopol biyu wannan shine kad'ai ze taimakeka Baba, idan kanada maganin k'arfe dana Bindiga Baba mifa? Gwanda dai a samu tsaron semu k'ara da naka, muyita addu'a kuma" Rik'e hannun momy Hafsat tayi

"Momy ki sanya mopol d'in su kaini masarauta, inason sanin halin da hammood yake ciki gaskia"

"Bara in kirawo khairiyya muji kenan" Tana janyo wayarta ta kira khairiya sega kiran Bilal (Yaron momy dakeson Hafsa dasuka had'u a US nake magana,yayan Khairiyya)

"Bilal ya akayi? Gyaran muryarshi yayi sannan yace

"Khairiyya ta kira waya tana kuka yanzu, wai mijinta da abokinsa da me martaba duk an harbesu" kallon Hafsat tayi kafin tace

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, harbi kuma a ina?

"Sun dawo masallaci ne kaman tace da asuba, ya kamata ki shirya zanzo muje yanzu" Da sauri tace

"Mu had'u agidan Bilal ba lokaci" Ajiye wayoyin sukayi sannan momy tana kallim Hafsat tace

"Ku tashi yazama dole muje masarautar ku yanzu" Batace komai ba sebin bayan momy datayi duk suka fita suka bar Baba me gadi da wannan mutanen tare da 'yan aikin gidan.

A k'ofar Gabas dake da babban gate na shiga fadar anan tarone sosai wanda baze baka damar shiga ciki ba kai tsaye seda k'wak'waran bincike, Hafsat ce ta sauka a motar ta soma k'ok'arin kutsawa cikin mutane batasha wahalar wucewa ba sabida saninta da akayi har kusa da ambulance dake wurin ta isa gasu kwance susu uku kamar gawarwaki, hannunsa daya sakko daga kan gadon da aka d'aurashi zuwa bayan ambulance d'in kawai ta kalla ta gano wanne ne shi acikinsu, badai abinda take gudu ne ya faru ba, badai duk wahalar data gama sha akan Hammood ba rayuwar kenan? Ciki hadda takawa da Muhseen bawan Allah bejiba be gani ba? Gabaki d'aya tsayawa tayi ta daskare agun tamkar an dasata!! Duk hada hadar da police da soja keyi awurin tare da sauran mutane batajin muryoyinsu akusa nesa da ita takejin tashin maganganun su, seda aka dafata sannan ta juyo a firgice ganin Bahar ce ya sanya ta fad'a jikinta ta fashe da kuka

"Ammu nashiga uku" rungumarta Bahar tayi tana bubbyga bayanta a hankali

"Addu'a zaki musu ba kuka ba Hafsatu, ki musu addu'a kizo kuma dummanmu zamuje asibiti, tunda suna numfashi dukkansu, ya zama dole muje har muga k'arshen ibtila'in daya afko mana" Batai magana ba tabi bayan Bahar Bahar tana janye da hannunta seda suka kai wurin mota ganin Baba Uthman ya sanya ta tsaya tana kallon sa seda Bahar ta kuma jan hannun ta sannan tace

"Mahaifiyar khairiyya tana waje, banaso mu tafi mu barta" Bahar na sanya jikinta da k'afarta acikin motar tace

"Mu isa waje tukunna" Ita kanta k'arfin hali take amma jikinta se rawa yake, tarihi ne yakeso ya maimaita kansa, haka akayiwa wancen sarkin haka aka kashe mijinta akan sarautar da ayanxu bako wani power sukeda ba se sunada d'aurin gindin 'yan siyasa!!! A waje kuwa Hafsa bataga momy va wannan ya sanya kawai suka wuce tana k'ok'arin kiranta a waya. Gaba d'aya a asibiti anyi cirko cirko, duk sanda Hafsat zata had'a ido da Baba Usman seya sakar mata Murmushhin zaki gane kurenki kokuma ya wurga mata sak'on hararar, shida kanshi shine ya yanke mata hukuncin antayata a freezer a kashe ta, ko shakka batayi mugunta a jininsa take, bayajin tsoro ne wai? Meyasa yake mata murmushi gani yake kamar bazata iya tona masa asiri ba? Dame yake tak'ama meya tink'aho dashi? Lokacin da likita ya fito neman 'yan uwan patient d'in Baba Usman ne yaje, haka kawai hankalinta be kwanta dashi ba tabi bayan sa batare daya sani ba, k'arewa yanayin ofishin kallo tayi a asirce sannan seta dawo jikin k'ofar da aka rufe jakar hannunta dai dake jikinta da bud'e ta d'akko wani karamin abu ta saka masa irin batir na agogon hannu sannan ta sunkuya k'asa k'ofar dabe gama had'ewa da k'asaba ta sanya siririn hannun ta tana addu'ar kar wani ya ganta acen ta sak'ala Atom recoder d'inta ta mik'e a hanzar ce tabar wurin dukda ciwon kan datake bazata tab'a bari a cutar da ahalin dasuka tallafeta ba, bazata tab'a bari aci galaba akansu ba, batada details na abinda ya faru a yau amma taji an ambaci harbi kenan da gaske jiya dasuke cewa they will end every thing today, Allah ya tashi kafad'un bayin nan naka, hadda Muhseen bejiba be gani ba.

Kallon Baba Usman likitan yayi cikin nutsuwa jin abinda yace kafin daga bisani yace yana sauke numfashi
Chapter 47 · 0% Book details