← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 71

Sashe 43

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rad'e rad'in magana nakeji da kuma k'ananun maganu daketa tashi ana gaya mun wai saura sati biyu muzo garin nan aka d'aurawa Hafsat aure da Mijina, nikuma na tabbatar duk fad'in masarautar nan ke kad'aice bazaki gayamun maganar daba gaskiya bace ba, shiyasa nazo inji daga majiya me tushe" kallon ta Bahar tayi sannan ta kawar da kanta tace

"Kafin zuwanki masarautar nan wani al'amari ya faru me d'aure kai wanda shine ma sanadin mik'aki aure da mahaifinki yayi awurin hammude, to al'amarin ya faru ne akan wannan Hafsat dakike gani, kuma an rigada anshirya yi musu aure atare tun kafin naki dan haka shine yanzu aka cika alk'awarin" kallon mamaki khairii ta mata sannan tace

"Auu wai dama Wannan itace karuwar tasa da akace yayiwa fyad'e ko yayiwa cikine kuketa kare kare, shine tsabar ci baya kuka aura masa ita dan kutuwar zuciya, shine sabida ni banida daraja aka had'ani da karuwa zuwa U.S aka mayar dani wawiya dabatasan me takeyi ba? Lallai ma kuncika" B'ata fuska Bahar tayi sannan tace

"Ke idan rashin Daraja kikeji kisan dawa kike magana kinji dan ninan bansan komai ba se darajata,duk wata hatsabibiya la'ananniya bata isa ta tako k'afarta har nan tace zata gayamun la'anata ko rashin daraja ba, idan bakinki ya kuma bud'ewa kika k'ara tunanin aika muggan kalamai akan Hafsat d'ina wlh zan d'ebe darajar dake kanki in wurgar a bola" Cikeda rashin kunya ta mik'e

"Yarinyar batada wani suna daya wuce karuwa, dan kina uwar sarki ko kakar yarima se akace a gagara gaya miki gaskia? Kun zalinceni nima inada yanci ai" Mik'ewa Bahar tayi sannan tace

"Rashin darajar ta isa haka khairiyya yanxu kinga fita anan, kuma karki kuskura ki kuma tunanin zuwa inda nake daga yanzu har abada, nime daraja duk wanda kikaga yana rab'ata tokuwa tabbas babu la'anta akansa d'an daraja ne, ke kuma bakida darajar dazaki fad'a ni kuma in fad'a dan kuwa nayi sa'a da kakar ki" Fuuuu Khairri ta fita daga d'akin tana k'unk'uni kwashe da alkhaybba me tsananin sauyin tsiya, a k'ofar fita daga d'akin tayi karo da Hammood shikuwa ya baro wurin sarki yazo gun bahar! Wani kallo yabita dashi dashi kad'ai yasan ma'anar sa lallai wannan yarinyar ba saiti a kanta!!
Sheshekar kukan Hafsat ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin dayaje, inda Bahar ma taje ta tsaya a k'ofar d'akin tana kiran hafsat, takawa shima yayi dan tun zuwan khairii yake bayanta yasan kukan me Hafsatun keyi, anan ya sanya hannunsa ya murd'a handle d'in take awurin kuwa k'ofar ya bud'e a hankali ya tura kansa aciki ganinta yashe acikin a saman tile ya sanya ya tura jikinshi duka aciki, wannan ne karonsa na farko dayaga tana kukan gaske, tabbas kalmomin khairii sun mata zafi, Bahar bata bi bayansa ba yanayin sa kad'ai ya isa ya nunar mata cewa yaji komai, sunkuyawa yayi ya d'auketa cak ya d'aurata akan gado sannan ya sunkuya daidai kunnenta yace

"Do not take what she said to your heart, i appologize on behalf of my queen" D'ago jajayen idanuwanta tayi ta sauke a kanshi sannan tace

"Ur repeatedly making thesame mistake all the time, So kake ka tona mana asiri,i told you not to talk ever again amma kaman bakajini ba, ko ina idone akanka ko rogar jikinka kada ka yadda dashi just go to your queen and let me be please"

"Idan.....rufe bakinsa tayi da hannunta sannan tace shhhhhhhh "Dont you dare say a word just leave please" Bece komai ba se yatsansa daya kai ya share mata hawayen idanta sannan ya mike, ya koma gun Bahar, zaman kuka ta saka masa

"Yau naga rashin Daraja Ni Tumba, yanzu kai Hammude dama da wannan mara darajar kake rayuwa, wacce la'ana tayi yawa akanta har bara ganin girman babab" Da hannu yaketa bata hak'uri amma daga k'arshe kukan dai yabarta tana yi seda hafsat ta ajiye nata kukan ta soma ban hak'uri.

******************
Yau a wurin meeting ma Hafsat ce ta shirya zataje a maimaikon Ameena, k'arfe d'aya da rabi na dare ta fito da shirinta mask ne kawai bata saka ba yana hannunta, muryar dataji a gefenta ne ya tilasta mata tsayawa ta lab'e basu ganta ba dankuwa daga gefenta suke, tana kallo suka nufi indabta nufa, itama da sauri ta sanya mask d'inta tabi bayansu cikin sand'a, haka suka taka atare susu biyu ita kuma ita kad'ai! Seda meeting yayi nisa sannan ta tsinkayi muryar da bazata tab'a mantawa da itaba tana cewa

"Wannan video sunada yawa a hannuna, banaji dan ammata barazana wata tsiyace, idan har sak'onninmu basu shigeta ba to wannan shishi kad'ai ne makamin mu" Nisawa wani daga ciki yayi sannaj yace

"Ai sak'on k'arshe ta amsa mana dame mukeso? Kuma na bata adresshing inda zamu had'u gobe, a mararraba hotel room 113rd floor" Babban cikin sune yace

"Ka samu wuri me kyau gaskia, karka bata damar jin tsoro ka gaya mana dukkanin sirrukan Mood dabata sani ba, ga k'ara da wannan abun na cewar uwarsa zalintar sarki tayi shi shege ne, gaba d'aya ka lalata matashi aranta" Murmushi wannan yayi sannan yace

"Allah yaja daran sarki na k'ware sosai a wannan harkar, ka kwantar da hankalinnka" Gyaran zama sarki yayi sannan yace

"Mutane 12 muka gayyata a wannan taron, yaya nake ganin wuri sha hud'u suke aciki lallai a tabbatar da an damk'e masu mana kutse kuma kamar ko yaushe a kashesu anan a binnesu anan, bazasu tsiraba" Cikin Hafsat ne ya bada wani sautiiii k'uuu daya sanya kowa seda yaji dankuwa tabbas Ameen ta sanar mata yau ba'a gayyaceta meeting ba tace ai bazasu gane ba setaje, kenan ta kira mutuwar ta kome? Tana tsakiya da wannan tunanin ta tsinkayi muryar Ogan yana cewa

"Kowa ya fad'i lambar sa muji idan munyi gayyata dashi, kowa da lambar da muka bashi kuma kunsan bama bada lamba a jere kamar ni yanzu nine lamba ta dubu bakwai da casa'in da hud'u" Anan kowa ya fara mikewa yana fad'ar lambar sa har akazo akan wani yana mik'ewa seya sanya hannunsa ya rufe bakin Hafsat da kuma hancinta da hannunsa ya watsa wata powder take ya cizgi hannunta sukabar cikin hall din a guje, itadai Hafsat batasan ko waye ba biye kawai take a guje tayi gujin har ranta ya b'aci, gashi kuma binsu ake da gudun fanfalak'i!!!!

MOM NU'AIYM.

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*ASSLAMU ALAIKUM,KAMAR YANDA NA FAD'A DAGA FARKO DAI HAKANE, BA KULLUM ZANKEYIN POSTING BA, IDAN NAYI YAU BAXANYI GOBE BA, DUK RANAR DAKUKAGA NAYI YAU NAYI GOBE TO NASAMU CHANCE KENAN INA FATAN ZAKUMUN UZURI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA D'AYA*

21.

Wata hanya ya d'auke tare da d'auke hankalin masubin bayansu, hannu ya sanya ya rufe mata baki bayan sun shiga lungun ga duhun dare bazata iya gane waye ba suka k'urawa juna ido acikin duhun dukkaninsu suna iya jiyo yanda sautin bugawar zuciyoyin junansu ke bugawa da k'arfi, zuwa wani lokaci dabaze wuce minti uku ba ya sake ta sannan ya fita daga lungun yana fitar da sautin hakin k'arya daga huhunsa yana tambayar wasu

"Kunyi nasarar ganinsu kuwa? Ni ban same suba" D'ayan yana kallon sa yace

"Bibiyar su a yanzu baze amfanemu da komai ba, shugaba ya suma dan haka mu koma kawai kafin k'ubgiyar kwantacciyar maciji ta ganmu ta gane sirrinmu" Haka suka juya zuwa d'akin taron na sirri zuciyoyin su babu dad'i suna mejin rad'ad'in abinda suka fad'a agaban wad'an nan. Dafe zuciyarta tayi dake k'ok'arin faso k'irjinta ta fito ta soma sauke numfarfashi sama sama tsananin tsoron data shiga, jikinta ba k'aramin rawa ya hauyi ba seda ta denajin takun sawun tafiyarsu da mintuna biyu zuwa biyar sannan ta zare mask ta cire bak'ar rigar dake jikinta, ta zubesu anan sannan ta fito daga cikin wurin tana waiwaye...... gab dazata shiga part d'in Bahar aka rik'o hannunta a zabure ta k'walla k'ara da sauri ya rufe mata baki da hannun sa cikin rad'a a kunnenta yace

"Daga ina kike cikin wannan daren" gano cewar Hammood ne ba k'aramin kwantar mata da hankali yayi ba, tace cikin sauke numfashi

"Alhamdulillah" sannan tayi lamo ta lafe ajikin sa, shikuwa hakan datayi ba k'aramin tasiri yayi ajikin saba, sungumarta gaba d'aya yayi nan d'inma lafewa tayi a k'irjin sa tana sauke gajerun numfashi a wahale, ji takeyi tamkar wani macecin rayuwarta yazo, kai tsaye cikin gidan yashiga dogarawa masu tsaron k'ofar basuce dasu komai ba, har d'akin dayake mallakin ta ya shigar da itabya ajiye ta akan gado, hannu yakai ya janyo mata hular dake kanta ta rufe sumar data lek'o ata gaban kanta, yana nazarin yanayin ta yace

"Daga ina kike yanzu? Kawar da kanta tayi daga dubansa sannan tace

"Kai daga ina kake yanzu? Murmushi yayi kafin yace

"Kinada ban mamaki Hafsat, kina ganin kamar ke kinfi kowa wayau ne kome? Tsammani kike kamar kin samu power dazaki iya kayar dani, ki sani nan masarauta tace kuma duk wani wanda yake k'ulla sharri ko alkhairi akaina inada masaniya akansa, lokaci kawai na baiwa kowa daze yabawa aya zak'inta a hannuna, wlh bakina dana rufe na tsawon shekaru sena fansheshi akan mak'iyna cikin k'asa ga wata watanni shida, idan kikaje ki gayawa manyan ki su shirya, kuma sunyi sake d'an zaki ya girma, a shirye nazo kuma tabbas sena kayar dasu nine da nasara, suna tak'amar suna iya wargazani, nikuma ina tak'amar zan iya wargaza dukkan shirin su, sena zame musu k'arfen k'afa fiye da yanda Takawa me martaba sarkin masarautar hankaka ya wargaza azzaluman masarautar sa. Duba littafin TAFARU TA KARE dan samun yanda ta kaya a wannan masarautar. Sena tabbatar na rugurguza anniyarsu kuma wallahi, summa tallahi billahi ni Hammood nayi alk'awarin koda raina ze zama fansa sena wargaza sirrin mak'iyana sannu a hankali" Mik'ewa tayi zaune sannan tace tana kallonsa ido cikin ido
Chapter 43 · 0% Book details