← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 71

Sashe 62

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Momy dama nace an gyara miki wurin kwanciya da komai a b'angarena naga kuma har yanzu baki zoba, shine nazo inji dare yanata tsalawa" murmushi irin na manya Momy tayi kafin tace "khairiyya kenan, mezanje b'angarenki nayi kuma? Ko k'anwarki gatanan rigimar damuke kenan, ni wurin Bahar zanje na kwana" Harara ta aikawa Hafsat sannan tace "Wannan mayyar momy kike cewa k'anwata, Allah ya tsari gatari da saran shuka" Kallon nutsuwa momy tayi mata, seda ta k'are mata kallo tatas sannan tace "Baby sallami kowa dakenan zamuyi magana dake da Hafsa" Tana k'unk'uni dukta sallami kowa Hafsa taje ta rufo k'ofar ta dawo sannan momy ta kallesu tace "Khairiyya na tabbatar daga ranar da kikaga mummunan Video abinda na aika nida Bilal kikaji kin tsaneni, inama ace bani bace na haifeki? Inama ace nakizo duniya ba hakane?" Ta k'arashe maganar tana kallon Khairii, ita kuwa cikin takaici tace "Ea momy amma wannan maganar be dace kiyita anan ba, Hafsat fa kishiya tace koda tace an saketa amma seta samu abun gorantamun ko?" Murmushi Momy tayi sannan tace "ke Video kika gani Hafsat taga zahiri, tagani da idanta ina aikata masha'a da Bilal amma matsayinta na 'yata bata gujeni ba, sema tattalina datake hartaso ta rabani da aikata abun na koreta, still duk abinda na mata nida Bilal danyasha yagalgala jikinta amma bata fasa yimun kallon uwa ba daga rik'onta da nayi, ta mana rufin asirin da koke iyakar abinda zakimu kenan amma shine kike ganin bekenta akan hakan, kinbi kin rainata akan Namiji kin tsane ta, Hafsa 'yar uwar rufin asirinki ce, duk masife masifen danake shiga itace take tsamoni da taimakon Allah, duk irin abinda mijinku yake ciki itace take cetonsa, amma kishin banza ya rufe miki ido kin kasa gane gaskia, idan zaki rik'e ta a matsayin daya dace ki rik'eta idan bazaki rik'eata a hakan ba ke kika sani, yanzu haka dakika ganni nan dabadan tana bibiyar me nake ciki ba da tuni Bilal yayi Nasarar rabani da kimata dankuwa yan fashi ya had'a za'aje a yak'eni amun fyad'e a k'wacen dukiyata amma tayi ruwa tayi tsaki bamma saniba aka kama Bilal yanzu haka yanacen tasa amai hukunci kuma inagama an zartar fin abinda ya mana, bazan hanata ba sabida inada takaicin Bilal! Yanzu kice baki tsani kowaba se ita akan namiji?" Ta juya ta kalli Hafsa sannan tace

"Ke kuma shashashar banza sakatyar wofi kinawa mijinki zancen saki dan ubanki bakida labarin tsinuwar Allah tana tabbata akan duk wata mace data nemi saki awurin mijinta da kanta? Allah yace ayi saki kuma ya fad'a bayason sakin akan me zaki taka haddi kikai matakin neman saki? To abinda zan fad'a miki shine mijinki da wannan Sufyan da Laurah sunzomun da maganar ankawomin takardar daya rubuta abinda Sufyan ya karanta miki bashi bane abinda ya rubuta, kinga takardar ma a hannuna" Ta zaro takardar ta soma karantawa a sarari

"Matata Hafsat ta nemi in saketa, ni kuma bazan tab'a iya sakin taba har abada, aurenmu na zobene Hafsat dan haka kiyi hak'uri. Nasan bazakiji dad'i ba idan kikaga sab'anin abinda kike tsammani a rubuce amma dan Allah kiyi hak'uri da abinda kikaji. Mijinki har abada Hammood" kallon Momy tayi tana dariya sannan tace "Allah momy k'arya suke so kawai suke suyiwa abun kwaskwarima amma gaba d'aya niba haka aka karanta takardan agaba naba" Tsaki gajera momy taja "Ni sun gayamun yanda akayi, shi Sufyanun bawai abinda yafada ya gani da takardan ba, bayaga haka kuma waya tab'a saki mace na cikin jinin haila? Mijin naki aiba jahili bane dase miki saki har uku, jini nan Hafsa kinsan Allah idan kika k'ara tashin mun zancen sakin nan baniba ko wanine agidanan koshi mijin nakiz wlh sena kakkaryaki mara kunyar banza me rank'walelen kai" Turo baki tayi tana sharar k'wallah

"Tunda ya yaudareni shida Allah" Dundu momy ta dire mata abaya "Rashin ta idan nan yana nan ko Hafsa,mijin naki kike gayawa magana haka gatsai, Allahu yasha gobe a d'akinki zaki kwana idan kinje kya mutu daga cen" Zumb'uro baki tayi tana hawaye, khairiyya kuwa ilahirin jikinta yayi matuk'ar sanyi dajin Hafsa tasan sirrin mahaifiyarta danata gaba d'aya, koda wasa bata tab'a nuna mata ba, kenan wannan shine halacci? Idan hakane tabbas itama zata nuna mata kalar nata halaccin. Komawa tayi a saman gwiyoyinta ta fuskanci mahaifiyar ta sosai sannan tace "Momy dan Allah kiyi hak'uri da duk shirmen dana ringayi, inshaa Allahu zan kiyaye nan gaba bazan kuma kwatanta aikata irin shirmen danayi akan koma meye ba" Jinjina kai momy tayi tana murmushi tanjuya zuwa ga Hafsa cikin k'ask'antar dakai tace "Hafsa dan Allah ki yafeni duk abinda na miki kiyi hak'uri bans.....rungumeta Hafsat tana me k'arawa kukanta k'arfi "Dan Allah kicewa momy tabarni asakaneni, wlh bazan iya wannan auren ba, tayaya zanyi kishi da 'yar uwata ba" Khairiyya da gaba d'aya bata jin kanta a dai-dai ta ce "Hak'uri zakiyi Hafsa, ni bazan rok'i momy ko mijin ki akan wai a sake ki ba, kanki d'aya kuwa? Cewa aka miki aure wasan 'yar tsana ne, kinga kima dena wannan shirmen" Ihu ta k'walla me firgitarwa tamkar wata tab'ararriya "Anty khairiyya baya sona, ya tsaneni, dukana yake ke shaida ce, so yake ya kasheni kuma ni bana so na mutu, dan Allah da manzan sa kisa ya sakeni, keya tab'a dukanki ne? Shiru khairiyya tayi ita kanta tana mamakin yanda Hammood komai k'ank'antar laifi indai akan Hafsa ne se ya nuna fusatar sa da sauri, dafe gefen kuncinta tayi tana share mata hawayen ta sannan tace "Koma waye shi ba sarki ba idan ya kuma dukan ki zan gaya masa kotu ce zata rabani da shi" Hafsa bata sake cewa komai ba se kukan datake ita ko khairii lallab'awa tayi tabar part d'in d'auke sa nauyin zuciya abubuwa da dama suna mata yawo a zuciyar ta.

Kallon tausayi Momy tayiwa Hafsa gaba d'aya ita rayuwar ta a sadau karwa ta k'are, babu abinda take se faranta ran wasu koda na ta baze yi dad'i ba, cikin wani yanayi mara dad'i tace da ita "Hafsa Nayi bincike me zurfi akan dangin mahaifiyar ki kuma nagano wani babban al'amari a tattare dake, abba ba zan gaya miki komai ba zan jingine maganar zuwa nanda kwana biyu idan abubuwan sun tafi, amma dai ki sani keme daraja ce sosai Hafsat, sabida haka ki aikata aiki irin na masu daraja" batace komai ba se kuka datake ta fama dashi.

**************
Gaba d'aya wannan d'ure d'uren da momy ke mata ta gaza gane kanshi, duk anbi an rud'a mata cikin ta, Laura ma datazo mata bata kula taba acewarta da ita aka had'a kai akai sakin zalinci aka yaudare ta, tana yatsina fuska tana wannan tunanin sanda tazo zata wuce kitchen Laura ta rik'o hannun ta ta waigo fuskarta babu walwala, murmushi Laure tayi sannan tace

"Haba k'awata, munfi kusa fa nidake, menene abun fushi kuma dani? Dan Allah kiyi hak'uri" Tsayawa tayi gaba d'aya tana kallonta tare da shagwab'e fuska "kawai hadda ke sesu zalince ni" Janta tayi suka nufi kitchen d'in cikin dabara tace

"K'anwata tayaya zaki nemi saki, ko bayan tsinuwar Allah zakiga sakama ko, ta yiyu ma ki shekara arba'in wani mijin be kuma zuwa ba" kallon ta tayi da mamaki "Akan me? Murmushi Laura tayi "Hakk'in mijinki mana dana Allah, meya miki dazaki tilasta ya sakeki, duk rashin sonki da abu idan musulunci bayaso ki rabu da yinshi ki fahimce ni, shawarar da zan baki ki rik'e mijinki tsakani da Allah komai me wucewa ne, ingaya miki da farko mijina ya tsaneni amma yanzu a duk fad'in duniyar nan banaji akwai mijinta yakewa so irin wanda Sufyan yakemun, kiyi hak'uri irin nawa dannima na tab'a cewa seya sakeni, amma daga baya daba barwa Allah yanzu komai ya zama tarihi" Nisawa tayi sannan tace

"Shikenan Laurah tunda kince mu k'awayene naji shawar warin ki na d'auka kuma inshaa Allah zan kiyaye" Dariya tayi "Ba anty kenan? Tana murmushi tace

"Besty zanke ce miki" Tana dariya tace "Nifa ba 'yar boko bace" kallon tuhuma tabita dashi kafin ta ce "Ban gane ba?" Tana dariya tace

"Allah kuwan zan baki labari akan samun ilimina, amma ni sam banyi makarantar boko ba" Jinjina kai tayi sannan tace "Ba damuwa wata rana zamu tattauna akaina" Shigowar Hammod ne ya katse musu hirar su inda Laura ta gaisa dashi tanufi hanyar barin wurin ita kuwa tabi bayan Laura, bece mata komai ba se hannunta daya kama, cak ta staya amma bata waigo ba, dragginta nata yayi a gabanshi, sannan yakai hannun sa asaman kuncinta inda yayi alamun k'urji yayi ja, kallon ta yayi cikin ido kafin tace

"Meya sameki anan d'in? Zumburo baki tayi "Ina ruwanka" ta bashi amsa a shagwab'e. Murza wurin yayi yana murmushi sannan yace

"Amarya har yanzu fushin kike dani? Tana langwab'ar dakai tace "To meye na tab'ani kuma" ta k'arashe tana kamma hannunsa zata zare a fuskar ta, tace "Abun 'yan iska kakemun" yana murmushi yace "Nima ki cikamun hannuna abun 'yan iska kikemun" da sauri ta sakeshi tana gajeran tsaki "Allah ya kiyaye" ta fad'a a hasale. Kallonta yayi yace "zuwa nayi ince ki had'amun wannan Milk Shake d'in danaga kin had'a ranar a U.S banaji akwai abinda babu a nan part d'in" Kallon kama rainani ta masa "Akan me zan maka wannan d'in, gwanda ma ka rabu dani, ni akwai abinda nake yanzu" kafin yayi magana seya tsinkayo muryan Bahar da alama nan take tinka rowa, da sauri ya manne jikinsa da nata ya shiga laluban bakinta, tana kici kicin k'watar kanta ya rik'eta gagam,jin salatin Bahar ya sanyashi ya saketa ya soma muzuran k'arya
Chapter 62 · 0% Book details