← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 71

Sashe 5

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan idar da sallan yajima sosai yana lazimi bayan yayi azkhar d'insa da komai sannan ya mik'e tsaye yana duba message d'in likitan dake tabbatar masa da cewar baya k'asar gaba d'aya, k'aramin tsaki yaja ya fito sekuma yayi karo da Muhseen dake jiransa a k'ofar masallacin dakuwa ko ba'a gaya masa ba ya tabbatar cewar yana masallacin a irin wannan lokacin musabaha sukayi sannan yabi bayanshi zuwa ciki danya tabbatar baze samu amsar komai ba se'a rubuce. Turus Suka tsaya suka kalli jama'ar dake wurin motar Mood ciki kuwa hadda me martaba, k'arasawa yayi shida Muhseen atake muhseen ya zube ya gayar da Me martaba, shikuwa yayi tsaye tamkar an dasashi a wurin ya kafe Me martaba da ido yana jira yaji mezaice wanne kalan labari zezo dashi yau kuma da sanyin safiyar nan, shid'inma shi yake kallo cikeda takaici

"Munaso musan wannan jinin daya fito daga motarka daga ina yake? menene asalin abinda ya faru? munyi tsammanin cewar ai rauni kaji sekaga fess dakai, amma wannan layin jinin dayayita d'iga har zuwa k'ofar d'akinka yake tun daga mota, gashi ana iya hangowa daga motar daka hau jiya aciki akwai jini a sit d'in baya dukda bame yawa bane ba, meke faruwa?" Har wannan lokacin be motsa ba ya daddage ya kafeshi da ido bayako k'iftawa, Muhseen ne ya rik'o hannunsa suka kalli juna yamai magana irinta kurame ma'ana sighn Language yace dashi

"Bro mana meke faruwa? karka bari wani mugun abu ya faru dakai a wannan safiyar, bannason kafiyar nan kakuma sani please talk" Nan d'inma kallon Muhseen kawai yake seda ya gama k'arewa Muhseen kallo sannan yayi amfani da sighn language(Yaren kurame) yace dashi

"Duk Munafukai ne fa! bakaga suna kallona ba, sunsai komai kome zanyi konace bazan wanke kaina ba sun gama shirya komai tsaf so i will not say a word" Dafe kai Muhseen yayi, Me martaba yace da Muhseen

"Ni banna gane wannan yaren na kurame kai Muhseen meyace maka? Wasu yawun takaici ya had'iya sannan yace

"Ni d'inma be bani amsa ba" Gyaran tsayuwa Me martaba yayi sannan yace

"Idon Masarauta sun tabbatar mana da cewar da mace ya shigo rai a hannun Allah tana d'akin sa, mukasan wacece? yau bazan lamuntaba wlh, muje d'akin nasa" Matse hannunsa Muhseen yayi amma seya warce hannun ransa a tsananin b'ace ya juya zuwa d'akin duk suka rufa masa baya ciki kuwa hadda sarki....... Tun a parlor k'asa ya tarar ma'aikata sunyi cirko cirko suna tsegumin jiya ya shigo da mace a hannu kuma maybe rauni taji jini duk a k'asan tile basuma goge wurinba tsabar sonjin mezaije yazo, ganin me martaba ya tilasta musu zubewa a k'asa dukkansu suna kwasar gaisuwa shikuwa cikeda sassarfa ya haura saman inda duk jama'ar suka rufa masa baya. Be b'ata lokaci ba wuri bud'e k'ofar d'akin dayake mallakin sa, duk kuwa suka rutsa aciki ciki kuwa hadda Muhseen dake fatan abunda suke son gani karsu gani d'in sedai kuma turus suka tsaya kallon 'Yarsha dake zube akan gadon zaninta a yafe kawai rigarta ata gaba a yage sumar kanta a hautsine sannan yanayin fuskarta kad'ai ya isa bayyanar maka cewar bata cikin hayyacinta, Me martaba cikin k'araji yace

"Hamood!!! meka aikatawa 'yar mutane wai? wacece wannan kwance a haka, Hammod neman matan naka haryakai kawa 'yar mutane fyad'e ka kawota cikin fada!" Babu alamun tsoro ko fargaba a tattare da Hammod girarsa ta sama ta had'e tas data k'asa fuskarsa babu annuri, beko motsaba amma ya tabbatar wannan shirine, baze tab'a iya kare kansa ba anyi amfani da tsananin tausayin dayake dashi akan al'umma an had'a kai da yarinyar dabe saniba an cutar dashi, anyi destroying rayuwar sa acikin sa'o'i dabasufi 12 biyu, da wanne bakin ze kare kansa koda yanadashi tunda wanda suka aikata masa sun shirya abunsu tunkafin yasani, ya afka acikin muguwar ramin su, ya tsunduma sosai acikin bak'in kogin da aka k'irk'ira domin sa kawai!! Muryar yarinyar ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin dayaje na wuccin gadi!

"Karka k'onamun k'afata, ban maka komai ba, kayi hak'uri, dan Allah kaikuma karka mun fyad'e, karka zo kusa dani, ku rabu dani karku ketamun haddi na, niba 'yar iska bace dan Allah kayi hak'uri" Wani uban ihu ta saka sekuma ta farka a zabure, ganin mutane a kanta kuma duk maza ya sanya tayi azamar soma rufe k'irjinta dake a bayyane, sannan ta soma gyaran zaninta tana kuka sosai! kalaman datake furtawa sune suka tabbatar da zargin dake zuciyar Hammood akan cewar had'a baki akayi da ita ake shirin cutar dashi, sannan tsawon dare yana tare da ita amma bata farkaba seda suka shigo wannan duk shiri ne. Salati wurin ya d'auka Manyan Fada suka dinga tsinewa Hamood, seda surutu ya lafa sannan Me martaba ya taka har wurin da yarinyar take yace yana kallon ta

"Ki kwantar da hankalinki yarinya, nan wurin kina wurin dazamu k'watar miki hakk'inki da tsare mutuncinki, kina hannun iyayen wanda basuda iyaye" Cikin kuka tace

"Hijabina zaku bani intafi dan Allah" Idan D'an Galadima ne ya sauka a kan tafukan k'afanta yahau salati

"Me martaba kalli k'afafun yarinyar nan, wai anya akwai imani akan Mood kuwa, haba mana se maganar karya k'ona mata k'afa takeyi" Ita dai se kuka take su kuwa mutane se lek'en tafukan k'afarta suke suna k'arawa da salati, sallamar kowa me Martaba yayi ya tura akan akira masa Jakadiya, yarage a d'akin iya shine dakuma Hammod se kuwa 'Yar Shara, kallon sosai Me martaba yayi masa sannan yace

"Ka sauk'ak'a abubuwa sosai agareni Hammood, nagode daka bari mukazo wannan lokacin acikin sauk'i kajiko" Har lokacin kallon sa yake bayako k'iftawa idan nan ya kad'a yayi jajir jijiyoyin dasuke a murd'e se walk'iya suke gaba d'aya sun k'ara fitowa sunyi rud'u rud'u, zuwa wannan lokacin zuciyarsa tafarfasa takeyi k'irjinsa se ciccira yake alamun abubuwan na shirin taso masa, suna haka Jakadiya ta iso, janye fuska me martaba yayi daga ta Hamood koda wane lokaci karonsu baya kwashewa lafiya besan dalili ba shikam

"Jakadiya a suturta yarinyar nan fyad'e aka mata, a duba idan akwai rauni a jikinta, a k'asan k'afarta duka biyu akwai rauni me alamun k'una ce, zan tura akawo likita kokuma akaiku asibiti, na baki izinin ajiye duk abinda kike ki kula da ita sosai dan kuwa Matar da Hammood ze aura ce, daga yanzu zuwa lokacin dazata samu sauk'i" Zubewa k'asa tayi tana me.jadda da masa bin umarnin sa shikuwa Hammod siririya dariya yayi yanzukam wacce harta bayyanar da sautin muryarsa da babu wanda ya tab'ajinsa a duk fad'in duniya! shi kanshi bazece ga amon sautin dariyar saba sabida bayi yake ba, Aransa yace here we are @ last! Dama nasan da manufa akayi dukkan wannan shirin, girar sa d'aya kawai ya d'age har lokacin murmushi bebar fuskar saba, Me martaba yace yana kallon Jakadiya

"D'akin dake kusa da nasa zaki gyara mata, ai b'arnar sace, idan mun gama gyarata sesu tare" Har lokacin bece komai ba se murmushi haka me martab'a ya fice yabarshi a tsaye, Jakadiya ta hau gyaran 'Yar shara da har lokacin kuka takeyi, tanayi tana mata sannu sabida yanayin tausayin datake bata a ranta tanata tsinewa Hammood akan b'akar halayyarsa mara kyau.....Yajima sosai tsaye yana k'arewa 'yar shara kallo, tunda yake tsanar mutane be tab'a tsanar wata halitta sama da wannan halittar daya zata abar tausayi bace ada, dajin sautin kukan nan nata gwanda jiyo sautin kukan mutuwar sa, ya tsani munafuki, bayason munafuki konan dacen, meya mata wacece ita? zata d'and'ani kud'arta a hannunsa tabbas! Muhseen ne yazo yaja hannunsa suka bar d'akin kai tsaye ma gidan yajashi suka bari sukaje gidansu muhseen d'in, atake ya rubuce masa tun farkon ganinsa da ita dakuma abinda ayake zargi zuwa yanzu, nisawa Muhseen yayi sannan ya fara magana a hankali

"Ban saniba ko abinda kake tunani hakanne amma banaso ka yankewa yarinyar hukuncin abinda bashikenan ba, wannan zargi kawai kake amma bamuda tabbacin cewar had'in baki ne, abu d'aya na sani, acikin biyu kodai hakan take had'in bakine kamar yanda kace kokuma inaga an sarane akan gab'a" Cikin fusata ya soma magana irin ta kurame ransa a b'ace

"Muhseen niba yaro bane ba, nasan sarai me suke nufi dani, tayaya wannan yarinyar duk inda nabi acen itama takebi? mesa ze zamana seni kad'ai, sunyi amfani da halina da suka sani na tausayi suka cutar dani, kaima kayi tunani mana ina iyayen yarinyar? daga faruwar abu se zancen aure? kaji sun tambayeta danginta ne? kokuma kaji sun tambayeta wani abu daya faru a tsakanina da ita, they used me suka kuma cutar dani, gayamun idan kaji sunyi wata magana dake nuni da cewar basusan komai akanta ba, ka dubafa ka gani muhseen awurin dana sameta ita kad'ai ba kowa, jinin dake fita ajikinta is not real, they planned everything they set me up" Ya k'arashe alamar maganar da hawaye a idanshi" Jinjina kai Muhseen yayi

"Yanzu na hango abinda kake hangowa tun d'azu mood, yanzu na harbo jirgin tabbas shirine, amma ya zamu b'ullowa lamarin? Da hannayensa yaci gaba da amfani da sign language wurin yi masa magana

"Sun rigada sunje sun gayawa Mami nssani, bansan mezance mata ba yanzu, she will not listen to me, please muhseen help me out" Rungumesa D'an uwan nasa yayi yana patting bayansa a hankali

"Calm down mana Mood, komai zezo ya wuce ne kamar yanda na baya suka wuce kaji" Shiru dukkabsu sukayi se sauke ajiyar zuciya da Mood keyi cikin jin zafin zuciyar sa.

**********
Chapter 5 · 0% Book details