← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 71

Sashe 30

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Appologize" Nan ma bata dena kallon sa ba kuma batayi abinda yace d'in ba, zuciyar sa gaya masa take ya wanke ta da mari amma bayaso yake dukan mace ba halin sa bane ba, amma me yarinyar nan take nufi dashine haka wai? cikin fad'a sosai yanzu kam ya kuma mata alamar ta bada hak'uri amma bud'ar bakin ta se cewa tayi

"Shine ya dace ya bani hak'uri and thats what am waiting for, i did nothing wrong then why should i be the one to appogize, how can he just grab my hand d'an iskan inane shi daze kaman hannu na" Mamaki sosai ya k'aru a fuskar Mood what is this girl wai? ya tambayi kansa a sarari kuma masifa yaso ya fara da hannayensa Bilal yayi saurin cewa

"K'anwata am sorry, i really am, kinsan na rayu anan shenaru sunkai goma sha biyar, am used to, anan ba komai bane sam na manta da hakan shisa akeso kake zama tushiyar ka kodan gudun manta irin wannan abubuwan, amma God know's i mean nothing" Murmushi ta masa

"What ever" Tana shirin mik'ewa Mood ya saka k'afarsa ta durk'ushe awurin da hannu ya kuma mata alamar "Apologize now" Tab'e baki tayi

"Wainikam baka ganewa ne? shi yama fika hankali ya gane me nake nufi dan kaga ya bada hak'uri" Damk'o kanta khairii tayi

"Me kike tunanin kice? cewar Prince dak'ik'i ne kome? ke kanki d'aya kuwa? Yauma kamar ranar haka ta durk'ushe tajuya fskantar khairi hannun ta ya langwashe ta k'walla k'ara kuma dole ta sake mata sumar da har hular kanta ya fita ta barbaje, hannu bibbiyu ta saka ta tureta taje cen Hammood ya rik'e ita kuwa ta kwasa a guje sumar kanta daya baje kamar wata haihuwar indiya tana gudu sumar kan nata tana shawagi sabida gyaran datasha an kashe kud'i wurin gyaran ta sosai, dan kuwa Bahar ba baya ba akwai tsafta, Hammod tsaye yayi ya rik'e k'ugu yana kallon ta shi kuwa Bilal yana dariya yana tafa hannu yace

"That funny thing, she's very honest inason mutum me irin halinta, so staright forward, gaskia tafimu gaskia" Kallon takaici Hammood ya masa yama rasa mezeyi, kawai barin wurin yayi. Kallon 'yar uwarsa yayi yace

"Khairii be very carefull with that girl, nasan ki da fad'a da tsanar me kyau, that poor thing u see there ko, zatayi wuyar sha'ani a murd'e take kaman namiji karki rik'a cewa zaki shiga sha'anin ta kinji ko? Murmushin yak'e tayi sannan tace

"Yaaa Bilal i really want to get rid of her, na tsani ganin ta agidan nan wlh, yarinyar batada kunya" Yana murmushi yace

"And she's beautiful nasan ki da tsanar masu kyau karki damu da wannan my sister is the most beautiful of all, by the way who is she? badai k'anwar saba naga suna kama" Wara ido tayi cikin takaici

"She's just a maid ba, k'anwar safa Allah ya kiyaye" Dariyar sa ya kumayi yana tafawa "You most have gone crazy, maid? lallai kin manta ma, kinsan school datake zuwa a garin nan is the most expensive of all, yaran masu kud'i sosai ne suke zuwa wannan school d'in idan me aikine ita waya saka ta" Tab'e baki tayi

"Allah kuwa yar aikine, wai uwar sarkice take mugun sonta shine ta 'yanta ta kaga tana rainawa mutane hankali" Murmushi yayi

"Ohh is that so, but still she's cool ai" Bata kuma magana akan Hafsat ba tace dashi

"Is mom still calling you? yana kallonta yace

"Kin manta na gaya miki tafi 4weeks bata neman a waya ha, dama ba d'agawa nake ba, inaga ta huta abinta" Nisawa tayi kafin tace

"Yaa Bilal what am about to tell u now is the most terrible and traggic story da inaga ka tab'aji arayuwar ka, but i have no option there is no one i can share this secret with except u, bayita dannan zuciyana akan karna gayawa kowa but the is ko" tayi shiru tana kallon sa da hawaye a fuskar ta shima ita yake

"Its really killing me inside wannan abun shine zeyi ajalina idan nayi shiru" Da sauri ya kalleta "Subhanallah khairr, wannan wane irin magana ne?" Zaunawa tayi shima ya zauna tana share hawayenta tace

"Wannan auren nawa dakake ta tambayar dalilin dayasa aka yishi agurguje bakanan bakama sani ba to dalilai biyu ne suka sanya kaga anyi auren nan, Na farko mijina kurma ne sanda aka bashi aurena na nuna bana so harna gudu daga gida wanda na tabbatar an gaya maka wannan, na biyu kuma dalilin dayasa na amince ina dawowa da maganar auren sabida ammun fyad'e ne" Cikin tashin hankali ya kalleta

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, khairiyya yaushe haka ta faru ban saniba? share hawayen ta tayi

"Babu wanda yasan ammun fyad'en dagani se wanda yamun fyad'en se momy se kuma mijina" Mamakin sane ya k'aru
"Momy kuma da mijinki? why ? nisawa tayi sannan a hankali ta soma labarta masa komai har kawo aurenta da Hammood ta k'ara da cewar

"Ni abinda yake damuna shine gaba d'aya na rasa meya hau kaina na gayawa Hammod sirrin mahaifiyar mu tabbas bana cikin hayyacin kaina, gaya masa sirrin momy yafi damuna akan maganar abinda Bilal yamun, ze iya tausayamun akan ba laifina bane amma mutuncin mahaifiya fa, anya Yaa Bilal inada kai kuwa? meya kaini gaya masa? mema yasa na masa bayanin wani abu? gabaki d'aya narasa yanda akayi nayi wannan katob'arar, narasa meke kaina, narasa inda hankalina ya tafi, mutuncin mahaifiya na sayar na tona mata asiri duk sanda na tuna wannan abin it keeps hunting me" Nisawa yayi yana d'auke hawayen idansa kafin yace

"Am so sorry khairiyya, duk wannan abun ya faru dakene sabida am not a good brother, da ina kusa dake bazaki bi shawaran wani banza ba, nice na wofintar dake nabarki bana tuntub'ar inji me kike ciki,ki gafarceni k'anwata kinji, wannan abun da Bilal ya miki na godewa Allah dabe samu sa'a duka a kanki ba, dana shiga uku, momy kuwa banaji abinda take ya shafeni ko wanda tayi itada Allah abu d'aya na sani dolene mu mata biyayya, dolene mu saurareta mu mata wa'azi, dolene mu kwantar mata da hankalin ta, dolene ayau musan me take ciki, bata kyautaba data lalata yaran mutane amma shima k'wad'ayayye ne and for abinda ya miki wlh senaga bayansa acikin ruwan sanyi, seyasan cewa ni Bilal sunan mu kawai iri d'aya amma hali yasha banban, abinda kika gayawa mijinki ki manta dashi kawai haka Allah ya tsara ba tsarinki bane ba, amma dolene kiso Hammood idan de ke 'yar halas ce, dolene ki masa biyayya ki kuma so duk abinda yakeso He sure is a good husband"Nisawa tayi cikin jimami

"Now i am relieved, now i can rest, now i can sleep in peace, at last na gaya maka abinda yake cina, maganar momy dakake cewa yaya zan b'ullowa labarin toh? nifa ta gagara ma ko kirana a waya" Murmushi yayi yace

"Allah sarki Momy, bazata ita kiraba ai, Allah ya k'yaleta tanata aikata masha'a tazata taci bulus ashe akanmu abin ze k'are kada ki damu kinji, zan kirata a waya anjima zan bata numberki na nan ita da kanta zata kiraki, ki dena damuwa kinji" Jinjina masa kanta tayi alamun to sannan sukaci gaba da tattaunawa.

***************
Mood bebi takan Hafsat yayi tafiyarshi yabar gidan, sanda ya dawo ma beko tunata ba danshi bata gaban sa, yau dai ya kula Khairin sa tana cikin damuwa wannan ya sanya ya zaunar da ita a k'asa yashiga yamutsa matsa sumar kanta yana sosawa a hankali, murmushi take zuba masa tana so suyi hira amma rashin sa'arta d'aya mijin nata baya magana, nisawa tayi data tuna yanda yanzu take tausayin rashin maganar sa, inama ace wannan kyakyawar fuskar tabud'i baki tayi magana, ta tabbatar da babu abinda ze hanawa muryar sa dad'i, kwantar da kanta tayi asaman k'afafuwansa fuskar ta tazo sama, suka sakarwa juna murmushi, tace dashi

"D'azu Bahar Sarauni tazo neman ka Hammood, wai wannan yarinyar bayada lafiya ta suma kuma bata farfad'o ba dan haka sunje asibiti da ita, tace baka d'auki wayaba idan kazo in gaya maka, mantawa nayi se yanzu gashi kuma har k'arfe shabiyu ya gota" Shiru bece mata komai ba amma aranshi yanajin wani iri me kuma ya sameta? ya tambayi kanshi ganin babu amsa ya sanya bata kuma magana ba.

Tunda ta tashi takejin ta tamkar babu abinda ya sameta jiya, kallon Bahar tayi data tare k'ofar wai bazata fita zuwa school tana dariya siririya ta fad'a jikinta

"Ammu na, nafa warware, kuma yau zamuyi test ne so kike karnaci komai, nanfa ba kamar Nigeria bane Ammu, idan na fad'i da gaske bazan kara ajin gaba ba" Nisawa Ammu tayi cikin tausayi

"Kiyi ki gama wannan test d'in, gwanda kawai amiki aikin nan ki huta, nayi nayi ki gayamun meke damunki kink'i, waye yake takuraki agidan nan? Murmushi ta k'ara k'ak'alowa

"Ammuu!! kina kusa dani fa, waye ze takurani, ni bansan tunanin meye akai naba" Murmushi Bahar tayi

"Waye ya isa ya tab'aki yau la'ana ta tabbata akansa shalelen Bahar" Rungumeta tayi tana dariya, bahar tace tana janyeta ajikinta

"Zata b'alla tsohuwa, yanda kiketa murjewa hakan nan nikam nace anya Hansatu bazakike sanya k'aton skirt zuwa makarantar nan ba, koma ki dinga sanya hijabi kawai" Kallon kanta tayi tana murmushin takaici

"Allah kuwan Ammu nikaina nasan banyiwa addinina adalciba, ba yanda zanyine amma wannan bujen shisa na matsu in kammala karatun nan, kalleni fa" Dariya Ammu tayi

"To kike sanya wani abu akai kafin kine school d'in" jinjina kai tayi tayi tana dariya
Chapter 30 · 0% Book details