← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 71

Sashe 6

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabaki d'aya kan Hafsat ya d'aure, bazata manta meya faruba itada wad'an nan gayun, lokacin da take k'ok'arin tserewa se k'afafunta suka gaza, k'unar dake k'afarta ya tsananta azaba, hakan ne ya tilasta mata tsayawa tana mayarda numfarfashi har suka cimmata, a lokacin ne ogansu ya musu umarni akan su b'are masa ita haka suka dinga jan kayan jikinta har sukayi nasarar rabata da zaninta da hijabinta suka kuma yaga mata rigarta, tayi iya k'ok'arinta taga cewar ta k'waci kanta amma haka suka daddage seda suka rabata da har pant d'inta, sesukayi rashin sa'a tana period, bayaga haka kuma ya b'alle mata tamkar ruwa sabida tsananin firgicin datake ciki, ogansu dayaji haushin haka seyace shiba k'azami bane bazeyi ba amma gudun data sakashi su lakad'a mata shegen duka, wannan ne abinda ya k'ara haukatar da ita dan kuwa tasha duka sanda sukaga bata iya koda iya d'aga k'afarta sannan suka tsere suka barta agun tsirara! To meyasa wad'an nan mutane masu magana daban suke cewa wani ya mata fyad'e ita babu wanda ya mata fyad'e, hasalima a fuskar wanda suke alak'antawa da fyad'en bata tab'a ganin saba, dan harga Allah sanda yaje gunta bataga fuskar saba batamasan me take ba, shin meke faruwa da itane a rayuwa? su waye anan kuma waya kawota nan d'in?.......

***************

Lokacin da Hammod da Muhseen sukazo wurin Mami sun jima a zaune kafin ta fito, bayan sun gayar da ita ta amsa sekuma sukayi shiru, sedaga bisani Muhseen ya gyara zamansa ya kwashe komai ya gaya mata yanda ya faru da yanda abubuwa suka juye, kallon nutsuwa tayi masa sannan dayake matsalar ta iri d'ayace da Hammood sunaji amma basa magana seta shiga mayar masa da sighn language cikin fad'a

"Shishi kad'ai yafi kowa yawan mak'iya a masarautar nan, idan bashi bane yayi meye nakaita d'akinsa, idan taimako yakeso ya kawota guna mana, koya kaita wurin daya dace, yakaita a sibiti mana ko ya kira en sanda, yanada iko isa da matsayin daba wanda ze tunkareshi akan yayi karya idan ya aikata d'aya daga cikin wad'an nan, ina goyon bayan me martaba, hukuncin sa daidaine tabbas seya aureta" Tana k'arashe maganar ta mik'e zuwa ciki ranta a b'ace. Mik'ewa Mood yayi ya lumshe idansa, banda mahaifiyar sa, baze tab'a jurar fushinta akan saba har abada, Muhseen da azama ya mik'e ya rik'eshi amma seya zame hannun sa ya soma aikin daya saba wato gudu yana zuwa b'angarensa gaba d'aya yayi umarni akan a sallami hadiman sa baya buk'atar aikin aransa yana nazarin yanda zeyi sa wannan wawiyar yarinyar seta yabawa aya zak'inta seya wulak'anta asalinta indai sunan sa Hammood!!

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA HUD'U*

kai tsaye d'akin da aka tanada dominta ya shiga yana me banke k'ofar da iyakacin k'arfin sa, idanuwansu suka tsark'e dana juna atake jikinta ya soma b'ari tana zaune asaman gado ta takure wuri d'aya se rarraba ido takeyi! Yafi mintuna goma a tsaye yana kallonta bece komai ba, seda dan kanshi ya gama tunanin dayake sannan ya juya da zummar barin d'akin abinda yajiyo je daga waje ya dakatar dashi ad'an lobin dake tsakanin waje dacikin d'akin

"Bari bari bari prince mood anji haushi, ai yanzu ance ko sarki yaji komai, jakadiya ta tabbatar wa sarki wannan yarinyar 'yar hannu ce cikine sukaje su zubar yazo da gaddama, ance tutsiye yarinyar akayi ta fad'i gaskia akan dama saurayintane dasukaje azubar da cikin daya mata shine fa aka samu matsala seya d'akkota ya kawo ta nan besan asirinsa ze tonu ba" Dariya d'ayar tayi

"Daba sunce aure zasu masa da itaba? to yanzu naji ance sarki yace a koreta tunda abun hakane, yazata hakk'inta yaci daze d'aura aurensu yanzu kuwa korace" Tafawa sukayi

"Bakiji yanda na tsani yarinyar ba wlh, da akace ze aureta nace su kurma an iya zab'e wannan yarinyar kyau kamar aljana shegiya se gashi,yanzu danaji labarin za'a koreta se wani sanyi ya mamayeni, dankuwa ni wlh inasan sa haka" Duka d'ayar ta d'aka mata a cinya

"Banza yafi k'arfin ma'aikata da bayi ki kama kanki" Be jira sun k'ara wata maganar ba ya fito daga d'akin,yauma kamar kullum beko kallesu ba ya shiga d'akinsa jikinsa a matuk'ar mace wai meke faruwa ne? menene gaskiyar maganar mutanen nan su kuma manyan munafukai ba? yaya yakejin maganar tana juyawa up side down?..... Mik'ewa yayi yanzun ma da sassarfa ya sakko k'asa ya nufi motar sa, beko nemi Muhseen ba dankuwa yaga motarsa a sukwane ya nufi gidan *UNCLE JAY*.......

Tunda Anty Barra taji tsayuwar motar da gudun tasan D'an kurma ne agidan yau kamar yanda take kiranshi, dan hakanda azama ta juya daga parlor zuwa ciki

"Uncle Jay bazan iya da rigimar Kurma ba, naji tsayuwar motarsa nakumaji gudunsa dan Allah ka tashi kaje" D'ago kai yayi ya kalleta yana murmushi

"Dama nasan zezo ban tsammanin zezo yanzu bane ba" Murmushin ta mayar masa "amma lafiya dai?"

"Ba lau ba dai, Mood ne bashida wayau ko kad'an, duk abinda zeyi seya saka rashin wayau se uban zurfin ciki da miskilancin tsiya" Tana kallon sa harya kai aya, nisawa tayi tace

"Ka saurareshi yanzu, tunda yazo mayi maganar daga baya" Mik'ewa yayi

"Noo wife agabanki zamuyi maganar muje kawai, its good kina wurin with those ur boosting idea's i belive abubuwan zasuje mana da sauk'i" Ba musu suka fita atare hannayensu sak'ale ana juna, a parlor suka sameshi harya shigo yana zaune akan sopa ya sunkuyar da kanshi hannayensa duka cure acikin sumar kansa. Gaisawa sukayi dashi da yarensa sannan ya mik'awa Uncle Jay duk abubuwan da suka faru a rubuce a takarda har gulman dayaji ma'aikatan dayace a kora sunayi, ga alama be isa yace ayi ba ayi a yanzu! Tare da Barra Jay ya zauna suka karance takardar tatas kallon sa yayi sannan yace

"Naje gidan da safe gun Maminka tamun bayanin farko akan yanda ka shigo da ita, dakuma ya da maganar ta k'ara juyewa akan na ciki, sedai sarki be yarda da maganar jakadiya ba akamar yanda kaji ana tsegumi, hasalima ya kashe wannan maganar, abu d'ayane ya dai ya kafe akan seka auri yarinyar ranar juma'a" Da sauri ya d'ago ya kallesa,cikin yare irin nasu kurame da tsananin b'acin rai ya soma magana da hannayensa wannan karon har kansa da wuya mosti yake yana yi tamkar ze tashi sama. Seda ya lafa sannan Uncle Jay ya kalli Barra

"Barra me kike hasashe, da gaske kema abinda muke zargi akan had'in bakine da yarinyar haka kema kike zargi" D'an shiru tayi na wani lokaci kafin ta nisa tace

"kaso saba'in harda biyar acikin d'ari yana nuni kai tsaye da cewar had'in bakine musamman idan akayi duba da yanayin yanda al'amura suke tafiya acikin fada tsakanin Mood da sauran 'yan uwansa kai harma da mahaifin sa daya haifeshi da cikinsa,na biyu kuma ita yarinyar bata musa akan dikkanin abubuwan da ake cewa ba alhali ya tabbatar mana cewar ta ganshi sanda yaje d'aukan ta har tashi tayi se kuma ta kasa, kaga anan ya dace ta kareshi idan har taimakon daya mata yakai mata matsayin taimako bawai sharri ake k'ulla masa da ita ba. Abu na biyu kuma shine kaso 25 acikin d'ari suna nuni da cewar faruwar komai co-incidence ne kawai aka samu, duba da irin wowtar dashi yayi, mesa sanda ya d'aukota bezo nan gidan ba, besa beje wurin Muhseen ba, shin mema ya hanashi zuwa gun Mami koya sanar da ita a waya, wannan zargine dabaze goguba musamman da idon Fada suka tabbatar k'arfe biyu ta wuce sanda ya shigo da ita, CCTV ma ya shaida hakan, bayaga haka ga jini kuma, bansan yaya ze faruba su k'ulla sharri irin wannan hadd fake jini, kaina yana k'ullewa sosai" Ta k'arashe maganar taname jingina bayanta da bayan kujerar. Gyaran zama Jay yayi

"Melon think mana, say something please" Nisawa tayi

"I need an audience with the f**king bitch, kafin ince komai Swt" Ta k'arashe maganar tana me zube lumsassun idanta akan mijin nata" Mik'ewa yayi

"Get ready now, kema kinsan halin kurma baze barni in hutaba harse ance an fasa aura masa Munafuka kamar yanda yake kiranta" Dariya sukayi sannan suka wuce d'aki a tare, shikuwa yana nan zaune dafe da kansa yana lissafa maganganun Anty Barra.

Tunda suka doshi b'angarensa aketa kallon su, shi yasan duk munafukai ne suke kallon sa, 'yan sa ido masu jira suji me zasuyi anan, sanda yakai k'ofar hawa a saman sa sannan ya tsaya ya kalli wani daga cikin securities d'insa dasuka shigo tare dashi ya mik'a masa hannu alamun ya bashi paper da pen, da sauri ya d'akko ya mik'a masa shikuwa ya rubuta

"Dismiss everyone from here" Da sauri ya juya ya soma aikin tattara mutanen har zuwa sama.

*****Da sallama suka shiga d'akin sedai yauma kamar kullum atakure suka tadda 'Yar shara rakub'e ta k'ule a k'arshen gado k'afarta d'aure da bandage duka biyu alamun an mata dressing na wutar har an rufe ta. Jay da Mood akan kujerar dake d'akin suka zauna yayinda Barra ta zauna asaman gado ta tattare hankalinta duka zuwa kan 'Yar shara tana sakar mata lallausan murmushi a fuskarta, tsorone bayyane akan fuskar 'yar shara wanda yasan abinda ake cewa tashin hankali yana kallonta ze tabbatar cewar hankalinta a tashe yake

"Sannu yarinya ya jikin naki kuma" Tsatsareta tayi da ido tana rarrabasu akan ta amma batace da ita ci kanki ba, anty Barra ce ta kuma cewa

"Wannan Uncle d'in Hammood d'in sunansa Jamil ni kuma matarsa ce sunana Anty Barratu amma yara kamarki suna kirana da Anty Barra, yayinda shi kuma kawun naku ake kiransa da suna Uncle Jay, dafatar zamu zama Ant da Uncle naki kema" Nanma batayi magana se k'ara matsawa take akuryar gadon sekace wacce za'a yanka.Shiru Barra tayi na adadin wasu seconds sannan ta kuma cewa da ita
Chapter 6 · 0% Book details