← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 71

Sashe 24

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*To masu karatu sekub gafarceni, a haka tsarin labarin nan yazo, ida na sanja zuwa ra'ayi wasu tabbas ma'anar labarin zata sauya sabida haka kuyi hakuri*

*Dawuya na samu damab post a gobe, inada aiki fita zanyi.*
*Mom Nu'aiym.

  *TSINTAR AYA*  FREE BOOK

     *BILLY GALADANCHI*

*#@ SURAYYAHMS, WANNAN SHAFIN NAKINE UWARGIDAN PRINCE MOOD, KECE JAGORA DUK WATA MATA AWURIN KURMA KECE SHUGABARSU, AMMA BANDA BAHAR, KINSANFA JIKANE KARTA LA'ANCEMU ATOH.*

     *SHAFI NA GOMA SHA BIYU*

Shida kanshi ya d'agata, k'urawa fuskarta ido yayi, dukta kumbura har idanta,ga k'wancin jini nan ko ina a fuskarta yayi jajir, gaba d'aya bata cikin hayyacinta, kallon sa ya Mayar akan Muhseen cikeda mamaki, shi d'inma shi yake kallo, Muhseen yace

"Kidnappers ne, ko wasu 'yan iskan, amma su bazasu saketa haka kawai ba" Girgiza masa kansa yayi yana tunano yanayin yanda ya hango tafiyar ta, k'irjinsa yana dokawa, akwai wani abu amma ita gata acikin kyakyawar sutura, idansa ne kaishi ak'an bushashen jinin daya bushe a k'afarta, kuma tabbas daga k'ark'ashin jikinta ya fito, wazgewa yayi da sauri ya k'ara jan rigarta ya rufe k'afar bayaso ko kad'an  Muhseen yagani, bayaso sam! A daddafe Momy ta biyo bayan ta, ita d'inma  tari take da k'yar take tafiya, muryanta ne satake faman kiran "Khairiyyah, khairiyyah!! shine ya ankarar dasu dukkansu suka kalle inda take takowa, takowa tayi harta k'araso inda suke, zubewa tayi a kusa dasu ta rik'o hannun khairiyya

"Ki tashi dan Allah khairiyya, karkimun haka, ki dubi girman Allah ki tashi kice kin yafemun dukkannin abinda na miki" Kallon juna sukayi shida Muhseen da mamaki.Muhseen yana kallonta yace

"Baiwar Allah kamar nasanki, bake bace Head of operation (H.O.P ) ta Solara bank ba? Hajiya Fatima Bintu? D'agowa tayi tana kare bakinta saboda tarin daya taso mata tace

"Nice, ka taimakeni ka kaimun 'yata asibiti a duba ta, bazan iya tuk'i ba nisam, banida lapia nima" Kallon ta yayi sannan ya kalli Mood, da hannu Mood yamasa alama akan baze bari akai khairiyya asibiti ba seyasan meya sameta"

"Haba Mood meye haka kuma? yarinyar nan batada lapia ga mahaifiyarta atare da ita mezai hana ka bari a akaita asibiti" Kwantar da ita yayi k'asa yana me k'ara jan rigarta zuwa k'afarta sannan ya zaro jotter ya rubuta

"Seen kasan bannason gaddama ko kad'an, ka d'auri matar nan kuje asibiti, am taking Khairiyya to my guees house, i will call my doctor zeje ya duba ta acen"  kallon sa yayi bayan ya gama karantawa yace

"Amma ai ita lafiyanta k'alau ko" Sake karb'an jotter yayi

"Something is not right here Seen, i can smell something fisshy, who knows ko aikin galadima ne? quiet sure they really look alike but what on earth are they doing here  at thesame time, i believe khairiyya is badly injured but this woman here, i doubt  her, yarinyar da akace ta b'ata ta gudu daga gida meze kawo ta nan, dough banida wani ilimi akan family ta, but she's claiming to be her mother mezesa kayi tunanin matar sarki tana wani aikin banki kuma ta amsa ita d'incce did that sound right to you?  Sauke nannauyan ajiyan zuciya Muhseen yayi ya kalli matar data fara aman me jini aciki sabida tari da sauri ya hefar da jotter hannunsa ya rik'eta

"Sannu, dama bakida lafiya ne? Tana numfashi da k'yar tace

"Kayiwa Allah ka kaini National hospital wurin Dr. Sunita ga key na mota na, am dying here? kallon ta yayi yanda take matse hannta d'aya a kafad'arsa yace

"Ina motar yake" kasa magana tayi tun tana iya yunk'urawa tayi tari  harta kasa, anan ta zube tana numfarfashi sama sama, muhseen waige ya somayi haryayi karo da motar daya kalli ya tabbatar itace, kia ce vaganti baka wuluk me asalin kyau, d'agata yayi yayi k'ofar gidan da hanzarin sa yana gudu har ya isa bakin motar da sauri ya turata a ciki shima ya fad'a!!ya tasheta ya bar wurin kai tsaye National hospital ya nufa aguje....

   wannan ne ya sanyata ran Mood dake Hammood mutum ne me tsananin sirri, bakomai daya shafesa yakeso wani yaji ba, dan haka kai tsaye masaukin daze kaita ya sauya daga inda ya gayawa mood zuwa wani gidansa daya gama gini yana shirin zuba 'yan haya wanda akwai komai daya shafi Funiture acikin sa.... Seda ya kwantar da ita sannan ya farfad'o da ita numfashi take da k'yar amma bata iya bud'e idanta ba sam, haka ya kira Dr. Yaseer ya kwatanta masa gidan yazo ya samesa..... Bayan sun gaisa yakaishi wurin da Khairiyya take ya mik'a masa jotter

"She was my fiencee but not anymore, any way i think she's raped ga duka kuma dannaga duk ko ina an daddaketa please ka duba mun ita" Kallon sa Dr. yaseer yayi

"Ea to a ina abun ya faru, and mesa kake tunanin rape ne" matsawa yayi ya fahimci kamar ta sake zama unconcious sannan yace yana d'age rigarta k'afanta ya bayyana ga layin jini nan kam ya bushe amma alamar bawani kamar hauka ya zubaba, kallon sa Dr. Yaseer yayi

"Bara na duba d'in" Kayan aikinsa ya d'eba ya soma duba jikinsa dukane sosai akai mata, yana tunanin ma ta samu targad'e a hannu ga kuma mak'oshin ta ma harta wuya ya kumbura, seda ya d'aga har bakinta da wasu instrument na k'arfe haka, dake dama da wata macen nurse yazo itane ta tayasa dubawa, lokacin dayake k'ok'arin duba jikinta Mood parlor ya koma bayan ya idar da komai ya bata injection na jutawa da pain reliever sannan ya dawo wurin mood, zama yayi suka fuskanci juna dukda Yaseer ya girmi Mood amma tare suka karanci likitanci a U.S hakan ya tilasta masa zama abokin sa, yasar matsalar Mood har wacce ta tilasta masa barin aikin sa na likitanci ya dawo gida gaba d'aya,cikin nutsuwa yace

"Who is that to you? Kallon sa yayi sosai sannan da hannu ya nunar masa cewar matar daze aurace, jinjina kai yayi sannan yace

"Amma Hammood waya yi mata wannan mummunan aikin? Take gaban hammood yayi mummunan fad'uwa ya d'ago kai da sauri ya kalli yaseer, wayarsa ya janyo cikin hanzari ya rubuta masa

"Me aka mata? sannan ya bashi wayar, data karanta seya nodding kansa a hankali kafin yace

"Da farko na zata cewar maza sunkai biyar da sukayi raping nata bayan mummunan dukan da aka mata , amma daga bisani koda muka duba jikinta zallan mugunta ne babu raping nata da akayi, they used maybe sharped object, something like a blade suka saka a jikinta suka yayyanka ta, nurse d'ina tana tunanin faratane masu k'umb'a akayita tura mata, ga full verginity ga k'ananun shekaru, to cut the long story short d'ai, an mata mummunan duka, anyi amfani da bakinta aka tura mata wani abu da k'arfi anyi nasarar ji mata rauni a maqoshi, dana duba bakin da kyau naga sperm acikinta, so probable someone force it on her through her mouth, and lastly they used maybe a sharped object or fingers with long nails to destroy her verginity, sunyi nasaran fitar da ita hayyacinta sunyi masarar yayyankata, yankanta gaskia se ammata d'inki, coz ko haihuwan fari tazo se haka wlh, fata na farko dana biyu duk sun yaga mata, kuma wurare da yawa" Gabaki d'aya tsigan jikin Mood seta suka tashi, hankalin sa ya tashi ainun ya shiga d'amauta gaba d'aya besan ma me yake soba, lokaci d'aya komai nasabya tsaya cak, wane me neman zuwa lahira ne ya tab'a masa Riyyan sa ? wanne me tsautsayin ne? idan har babu abinda namiji yayi da ita se wannan kenan zallan mugunta ne? idansa jajir ya kalli Dr. Yaseer, wayarsa ya k'ara d'auka ya rubuta masa

"Yanzu menene mafita? kallon sa yasir yayi sanda ya tura wayar agabansa

"Mafita d'aya shine amata d'inkin nan tunkafin wurin ya mata tsami, danya rigada ya soma inaga abun befi sa'o'i biyu dudu da faruwa bafa, amma dan Allah ina kuka ganta? iyayenta sun sani kuwa? Da wayar ya k'ara rubuta masa

"'yar sarkin Baihatul Mulk ce, itace tabar gidansu da sunan bazata aureniba ni kurma ne, tace lallai idan har iyayenta basu janye zancen aurena da ita ba zata shiga duniya, toni bansan daga sama ba kawai dai a hanya muka had'u da ita tana tafiya tana layi a hannunmu ta suma nida Seen" Jinjina kai Yaseer yayi

"Amma gaskia yarinyar nan an cutar da ita, inaga wasu miyagun ne suka had'u da ita suka cutar da ita amma yanzu meye shawara, muje asibitinne kokuma anan za'ayi d'inki? Nisawa yayi kafin ya masa alama da hannu akan ayi d'inkin anan bayaso maganar ta fita ze mayar da ita gidansu inta wartsake ne" Hakan kuwa akayi da yamma sosai Yaseer ya dawo aka d'inke wurin data samu raunukan da wannan karon hatta Mood seda ya duba da kansa, yakuma tabbatar cewar hak'ik'a yatsune duka hannu ma sukutum akayita tura mata shisa duk ta yage......

Muhseen tunda yakai Momy asibiti bebar wurinba har seda ta dawo hayyacinta, tana samun sauk'i sunan khairiyya shine abakinta, anan yayi kokarin kwantar mata da hankali sannan ya nemi sanin a 'yan uwanta wazai kira? dan kuwa Dr. sunita koda ya kawo ta an sanar masa taje Dubai tafiyar yin wani course ta sati biyu dukda yake ta gayawa momyn ma mantawa tayi. Lokaci d'aya hankalin Momy ya tashi, tabbas 'yan uwa rahama ne, seda mijinta ya nemi yi mata sutura ta tsere daga wurin sa, seda yaso rufa mata asiri tayi masa izgili, seda yaso ta zauna acikin yan uwa taki, ace duk dukiyar data mallaka tome aikin ya tsinana mata yanxu ? kallon Muhseen tayi tace

"Nagaji da b'oyewa mutane wacece ni, nagaji da b'oyewa mutane ainahin mugun halina, sunana Bintu ni tsohuwar matar sarkin Baiha ce, nice mahaifiyar Khairiyya dakuma Bilal, sannan nice wannan matar daka sani ina aiki banki, banida kowa se 'yan aikina, suna cen gidana zan baka address sekaje ka tahomun dasu da d'an abincin da zanci, ka kuma bincimamun wancen abokin nata yaya khairiyya take, kawo hak'uri yaro nasan na takuraka da yawa" Jinjina kansa yayi yana murmushi kafin yace

"Kibani address my driver will go instead, i will stay here with you kafin suzo, i cnt just leave you here ma" Murmushi ta sakar masa kafin tace
Chapter 24 · 0% Book details