← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 71

Sashe 19

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bilal wannan ai me sauk'ine na yadda wlh, duk ayi hakan, gidan dazan baka ginawa dama zanyi zan saya fili sena baka kud'in gidan tunda nidakai zamu zauna, kayan lefe da komai na waccen duk zan baka kud'in su yau bama se gobe ba, kaidai kawia ka rik'e alk'awari" Murmushi yayi sannan yace

"Momy bazan tab'a iya rayuwa babu keba, na saba dake kobaki rok'eni kinmun wad'an nan abubuwan ba dole ya zamemun na aureki dan inasanki fiye da yanda nakeson kaina" Mace dai macece ko shekarunta nawa ya ayyana aransa sokuwa kawai

"Nagode Bilal, yanzu nawa ze isheka lefe, kuma wacece yarinyar? Murmushi yayi yace

"Momy mubar zancen lefe nifa akan sonki banida wata budurwa yanzu zan nema, kuma akwai sauran kusan 2.m cikin acc nawa please save your money,basekin mun aure zan aurekiba, kawai so nake tubanki ya zama na gaskia mun d'auki zunubu da yawa momy, tukunna mawai sau nawa kika zubar da cikina" Yanxu kam kunyace ta tilasta mata sauke k'wayar idanta k'asa kafin tace

"So d'ayane kuma da kansa ya zube Bilal, banmasan dashiba seda ya zube inaga ko k'wari ma beyiba"

"Daganan kuma sekiketa shan maganin hana d'aukar ciki ko? ya furta yana tsatsareta da ido, tarasa dalilin daya sanya takejin tsoron Bilal a yanzu

"Nafi shekaru uku ban shaba wlh, kawai cikinne Allah ya tsare be kuma zuwa ba" Nisawa yayi kafin yace

"Yau zan koma fa" Jinjina kai gwanda Bilal ya tafi, gwanda baya kusa da ita shed'an baze dena kwad'aita mata shiba har abada

"Ba damuwa zan tura ma kud'in idan naje office da safe" Murmushi kawai yayi ya juya.

*****************

Bak'in k'irin da Rai khairiyya tayi yayinda Muhseen keta xuba zance akan setayi hak'uri abokin sa baya magana sedai tabbas duk abinda take fad'a yana jinta, shek'ek'e ta kallesa

"Allah ya tsari gatari da saran shuka, ina zan zubar da ajina wurin yiwa namiji magana shi bemunba, idan har baze bud'e baki yayi magana ba tokuwa har abada zamu tabbata ne muna kallon juna, banda sanabe mema yazoyi guna ga yanda Allah ya halicce sa, kawai yaje ya nemi mara magana irinsa, tunda yana jin me ake cewa na tabbatar cutar mata kurumta bace ta maganta ce, katab'a ji an kira mutum da kurma kuma ance yanaji? Da mamaki Muhseen ya kalleta da wannan cin fuskar ta wulak'anci yace

"Haba gimbiya? bak'onka ai annabin kane dan mutum yanada lalura seki hau gaya masa magana shima ai bashi ya halicci kansa hakanba, kurumta kuma dakike gani farkon da aka haifesa koji bayayi, yanada shekaru goma akayi nasarar magance ya dawo yanaji amma har yanzu Allah be bashi ikon yin magana ba" gyatsine tayi kafin tace

"Toni dai kam Allah ya bani ikon magana, kuma yabani ikon ji, yaje cen ya nemi kurma kuma bebiya irinsa karyazo ya manna mun masifa, salon kawai inzo in haifi 'ya'ya kurame da bebaye, Allah kiyaye" Kallon sa Muhseen yayi yaga yanata dariya cen cikin k'irjinsa, not bad she's really beautiful above all kuma yanasan tsiwar ta tana burgeshi, da hannu yayiwa Muhseen alamun yabarta taci gaba da tsiwar tata, mik'ewa tayi tana harararsu

"Allah ko, gwanda kaje ka sanar agidanku baka sona ka ga ninan sun addabeni da maganar sesun mun auren da kurma, kai kuma namiji ne zaka iya dasu" Mik'ewa kawai shima yarigata ficewa amma me da sauri tasha gabansa

"Kaji, dansan manzan Allah kace baka sona, wlh banaso in auri kurma, inba hakaba zan gudu daga gidan nan wlh" Kakkafeta yayi da ido amma beko motsaba, shi soma yake tayita tsiwar kokuma ta bashi hanya yayita gudu

"Yaya Kurma dan Allah fa" Muhseen ne yace da ita

"Malama ga kayan gaisuwa cen, bamu gadi rashin tarbiya ba, saraki a masarautar mu baya magana biyu, dan haka kisan me kike ciki, idan tashi gudu kije bangon duniya" Waigowa Mood yayi yana kallan sa da mamaki, beso ya biyeta ha seta rainasu ai, cikin tsiwar tace

"Kadena mun magana banida lokacin ka inadai bakai bane kurma? da wata mummunar fuskarka awurin" Muhseen yaji zafin kalamanta cikin jin haushi yace

"Nagode hurul ain" mood murmushi ya kalleta yanayi sannan yakai hannunsa ya janyo nata ya tura mata wani zoben zinari a yatsanta daba komai kallon sa tayi sannan ya zaro jotter ya rubuta mata

"Na biya sadakin ki wannan zuwan danayi, kin rigada kin zama rabi ta kurma" kafin ma ta gama karantawa yayi gaba abunsa beko sake kallon taba, itakuwa zama tayi tana kuka, Muhseen kam bayan sa yabi yanata banbami. Tunda suka bar masarautar suka d'auki hanyar barin garin yake zuba murmushi, wato da gaske wannan sarakan tsiwar burgeshi take, yanda take masifa abun seya k'ayatar dashi gatanan kyakyawa da ita son kowa k'in wanda ya rasa, Muhseen ya fahimci abokin shi ya kamu dason wannan k'wayamar shi harga Allah takaici take bashi yarinya ba komai a kanta se fitina da rashin mutunci shegiya....

Tunda Hammood yake an dasashi shida Hafsat ala dole yazo su gaisa bece mata ci kanki ba, gashi shishi kad'ai yazo duk se ya kasance atakure Hafsat take ganin sun shafe 30mns beyi magana ba ya sanya tace

"Ranka ya dad'e dan Allah kayi hak'uri, wlh duk abubuwan dakake tsammani da sanina suka faru wlh bansan komai ba, nima kaina tsintar kaina kawai nayi a yanayin daka sameni, gidan nan bansan kowa ba, zargin da aketa laftawa akanka dani bansan komai ba dan Allah kayi hak'uri" Tab'e bakinsa yayi sannan ya mik'e tsaye ya soma shirin barin parlon, da gudu ta ruga ta tsuguna a gabansa

"Dan Allah badanni ba koda bazaka yarda dani ba ka saurari labari na" Wani mugun kallon tsana yake zagayar ta dashi tafi minti uku bece mata komai ba, kafin daga bisani ya zagayeta gaba d'aya yanemi barin d'akin, kanta ne ya sara mata tayi hanzarin dafewa.

****************

Duk wani shirye shirye na guduwa Khairiyya tagama tsarashi itada Bilal, dan haka yauce ranar tafiya tagama tsarawa saga 8 na safen data fita tafita kenan se bayan sati daya sesun tsorata sun fasa mata auren dole, letter ta ajiye da wayoyinta gaba d'aya kamar yanda Bilal ya tsara mata, he sure knows that zasu iya nemanta through mobile tracking, bayaso sam a b'ata masa aikinsa, badai Momy ta bashi 50.m ba tace gini 45.m ga filin data saya da sunan sa, ga kuma 5.m na lefe lallai yagama samun abun zaman duniya dan haka bashida case yagama da yarta ya bada video ta kalla dama ya kammala karatunsa sedai ta nemi wani amma har iyayensa dare d'aya zata nema ta rasa!!! Daga baya ya karb'i takardun sa na school.ko baya kusa.

*Mom Nu'aiym.*

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

~NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GAREKI MEENAT A 'YANDOMA, ALLAH BAYAR KAUNA YA SAKA DA ALKHAIRI~

"SHAFI NA GOMA"

Mik'ewa tayi tabi bayanshi da kallo, bazata koma gidan Momy ba sabida Bilal baze tab'a barinta ba kuma sannan momy batada halaye na garin daya dace a zauna da ita, bakuma zata tab'a komawa wancen garin wanda yake tushe kuma mafarinta, idan har wanda ya kawo ubanka duniya ze cutar dakai a rayuwa waye baze cutar dakai ba? Wannan mutumin kuma gashi nan kansa a murd'e yak'i ya saurare ta, shikenan bazata matsa masa ba amma wlh zezo lokacin dayakeso yaji labarin wani abu daga bakin ta bazata furta koda kalmar ci kanka bane. Kannata yanaci gaba sara mata, tasoma fahimtar irin ciwon dake damun ta, yanzu yanzu zata suma kokuma tama rasa metayi sedai ta farka ta ganta a kwance kaman tayi bacci ta tashi, zuwa tayi ta kwanta akan doguwar kujerar dake parlor d'in amon sautin muryar D'an galadima yana ratsa dodon kunnenta

"Na fahimci matsalarki danginki basa sanki, na fahimci cikin shege akayi aka haifeki, nagama fahimtar bakida gata, to bari kini wannan masarautar dakike gani ta kowa ce, muna baiwa marayu irinki masauki, idan kinyi abinda nakeso in baki matsayin ko baiwa , idan kika kuskura kika bud'e bakinki kika baiwa wani labarin ainahin gaskiyar meya faru kokuma ke wacece tabbas sena azabtar dake, wlh maza hamsin zasu miki fyad'e kuma in wurgaki a teku ba abinda za'ayi mukeda mulkin, karnaji kin bud'i baki kinyi maganar asalinki ko danginki, yanda zakiji likita ya fad'a bakya iya tuna komai lallai komai nisan zaman dazakiyi agidan nan ki tabbata a haka, ranar daduk kika tonamun asiri wlh sena tona miki asiri kema" Lumshe idanta tae, after all she decided to talk and this man is feeling himself, like seriously what is he feeling like? sarki kokuma d'an sarki, ita Allah yayi acikin bayinsa talakawa, amma ya d'aga darajarta tayi primary dukda a primary 4 tayi common entrance tashiga j.s.s. 1 kuma bayan tazo nan garin ta baro garinsu mamanta tana 'yar JSS 3 kuma data koma garinsu Babanta suka turota aikatau momy ta sakata school kuma tana shirin zana wa'ec ma wannan abun ya sameta, tanada ilimin addini daidai gwargwado tome yayi zafi shiba wutaba da har ze soma tunanin yafita ilimi kome? duk tayi irin nasa kuma ita sam ba jahila bace ba, bahar ta sanar da ita an karb'eta agidan a matsayin 'Ya awurin bahar hakan ya bata daman zama 'k'anwar sarki wanda a musulunce tasan an halasta adoption, mesa zatayiwa Allah addu'an neman d'auki ya kawo mata agaji kuma ta watsar, bazata yiwa Allah butulciba zataje wurin da aka shirya don gabatar da ita matsayin 'yar gida, zata karb'i sabuwar rayuwar datazo mata, shi kuwa Mood su zuba shida ita, bata masa komai bazata d'auki dizgi da wulak'anci ba, after all abinda yakeji dadi jinin sane kawai babu ajikin ta amma itama tanaji da irinsa yanzu!!
Chapter 19 · 0% Book details