← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 71

Sashe 10

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kowa yayi ko tayi iya yinta, daga nan zuwa k'arfe goma na daren yau a sanar nace duk wanda yaci wani abu a wurin nan nine zan biya" Ihun ne ya k'ara yawa sannan yace ciki isa

"D'an madami ze baiwa duk wanda ke wurin nan kyautar naira dubu goma daga yanzu zuwa k'arfw goma na dare" Nanma wata sabuwar sowar ce shima d'in a babban wurin dayafi kowanne k'ayatuwa ya nufa shida manyan abokanan sa don suci nasu abincin.......
Lokacin da khairiyya ta kammala cin abincin ta tana zaune jiran waitress d'in for payment amma batazoba.Wani ne yazo kanta ya irga dubu goma ya ajiye agabanta,kallonsa tayi "Na meye malam?" ta buk'aci sani cikin zafi "Calm down mana sis, kyauta ce daga Babban yaro" K'are masa kallo tayi "Bana karb'ar gift from strangers ka mayar masa" Wani xaro ido yayi "Ke ba'a mayar da kyautar babban yaro, cikin takaici tace "Malam na gode ka had'a nawa da naka nabar maka" Godiya ya mata ya juya ko'a jikinsa, aranta tana mamakin waye kuma wani babban yaro? se zuba tsaki take lokaci zuwa lokaci tana kallon agogon hannunta, ganin waitress d'in batada niyyan zuwa ya tilastawa Khairiyya mik'ewa taje reception nasu, kallon waitress d'in tayi tace "What is my bill you guys kept me waiting since, it is unusual naga kune kuke zuwa karb'a ko? Matar tana fara'a tace

"Bakiji ba kenan, ai Babban yaro ya biyawa duk wanda zeci abinci yau kud'i daga yanzu har goma na dare" D'an k'aramin tsaki tayi

"Count me out of that bullsh**t , my dear will u please tell me my bill" Kallon k'ofar tayi dake bayan ta,tace

"Ma'am its as simple as that fa, ba kud'inki ya huta ba" Duka Khairiyya ta kaiwa table d'in abinda k'aranshi ya karad'e ilahirin wurin harya janyo hankalin d'aukan mutan wurin akansu

"I said i will settle my bill, i have spoken!!! wane d'an iskan ne ya isa ya biya kud'in abincina, who the hell did he think he is, bannaso bana buk'atar alfarma awurin kowane d'an rainin hankali" Bilal dayaji kalamanta tamkar gaushin wuta seya kasa hak'uri ya tako yazo har gabanta yana watsa mata wani kallo

"ke! waye d'an iska" D'agowa tayi ta kalleshi ta wani yamutsa fuska

"Ohh God you again, Annah the mad man is here again" Be fahimci inda kalamanta suka dosa ba, kafin yayi magana wasu gayu sunyo kanta tamkar zasu cinyeta d'anye cikin isa tace

"You guys calm down mana, is he ur hero? kodan ya saya muku abincin wuni d'aya? waigawa tayi ta kalli waitress d'in datayi tsaye tamkar an dasata tace tana murmushi

"Daga yau zuwa wata shekarar iwar haka duk wanda zeci abinci a wurin nan na saya masa, be it breakfast, lunch or dinner or both the 3 meals per day!! Jakarta ta zuge ta zaro wani card a wata k'aramar waled ta d'aura akan table d'in

"Kullum kije ki cire kud'i adadin yawan abincin da kuka sayar a wannan card d'in" Harta juya babu wanda ya koda motsa ciki kuwa hadda Bilal, sanda takai k'ofa sannan ta waigo tana murmushi tace "3753 is the code, remember wata shekarar iwar harka i will come for my card so take care of it sosai sosai" Tana kaiwa nan ta juya tabarsu da sakakken baki kowa se mamakinta yake, Bilal wani bak'in ciki ya ziyarcesa yama rasa me zaiyi, ya tsani yarinyar dayakeda yak'inin 'yar sugar mommyn sace shizata wulak'antar har haka, amma idan yace ze gwada fushi yanzu shine zai wahala, dan baze samu abinda yakeso ba kenan, da sauri yabi bayanta dogarawa yagani a wurin motar dataje shiga atake aka bud'e mata k'ofar har zasu rufe ya k'araso yana haki

"I come to appologise, am very sorry please, am not bragging, am not doing it for my name, I'm only trying to help, bansan kina cikiba, dana zare sunanki aciki Ur royal highness" Ya k'arashe maganar kanshi a k'asa, this is exatly what Princess Riyya want, a duk'a mata, a nuna mata ita watace ,a girmama ta and he got her just right there, lokaci d'aya ta manta daduk wani abu daya shiga a tsakanin su na b'acin rai, ta sakar masa murmushi

"Bakada matsala, mun fahimceka" Yana murmushi yace

"Nasan ban isaba nasan ban kaiba, amma ina neman alfarma" Tana murmushi tace "Haka mukeso tame kenan?" Sosa sumarsa yayi

"I just want to befriend her Royal Highness" Tana murmushi tace

"Grab this. 08030000000, princess Riyyah from the kingdom of Baihatul Mulk. the code is 3753, i will be expecting ur call friend" Wayewar ta ta gama dashi, wannan tashin k'asar nan ce kuwa? ya ayyana a ranshi lokaci d'aya ya haddace komai sedai kuma be gane wanne code bane wannan, any ways kallon ta yayi

"Thanks for everything your royal Highness" Matsawa yayi aka rufe mata sannan ta zuge glass tace dashi

"Remember just friends" Had'e hannunsa yayi alamun godiya sannan yace

"My pleasure" Ya juya yana murmushin samun nasara!!!!

**************
Tunda suka dawo be sanya wannan munafukar a idanshi ba, bayamason ganinta, yanaso yaje gidan U jay amma bayaso yaga wannan mayyar Munafukar, dan haka bejeba se waya ya masa, a wannan yammacin ne aka aiko neman sa daga fada, badan yasoba ya shirya sosai ya nufi fadar idanshi a lumshe yana aikin daya saba na gudu. Mutanen fada yauma kamar kullum suna nan a jere kamar yanda suka saba, a tsakiyar su ya ratsa yaje gaban sarki, bayan ya duk'a ya gayar dashi sekuma yayi shiru seda fada tafi mintuna goma shiru sannan sarki yace

"Hamood yarinyar daka lalata zamu d'aura maka aure da ita nanda sati biyu, dukda kaji tanada matsalar k'walwa." bece komai ba se kallon uban dayake, shikuwa sarki yaci gama

"Na gayawa Aminina kuma abokina Sarkin masarautar Baiha, na Baihatul Mulk yakuma yi fad'a sosai akan zubar mana da mutinci dakayi, yace lallai a aura maka wacce ka lalata d'in bayan haka ya baka auren 'yarsa Khairiyya sabida dolene jini irin naka se naka, wato sarauta, 'yar talakawa sam bata dace dakai ba, dankai kajane" Wani irin bak'in cikine ya lullub'e Hamood tozarcin har nisan wata masarauta aka kaishi? Lallai mahaifinsa baya k'aunarsa, auren mata biyu aciki babu wacce yakeso, da k'yar ya had'a hannayensa biyu alamar godiya ya sunkuyar dakai sannan ya mik'e, me martaba cikin isa yace

"You are dismiss" Ba musu ya juya da gudu kamar yanda yazo da gudu, koyau dayazo kusada D'an galadima seda ya tsaya suka kalli juna atake ya karanto zuciyar D'an galadima dake kallon sa yana murmushi!!!

*****************
"Annah, wane magana nakeji wai, aure ni kuma am just 18 fa kasheni zakuyi, kuma bansan mijinba bance ina sansa ba se wani aure, wani abun takaicin ma shine wai kurma ne fa, duk ajina? Mik'ewa Annah tayi tana zagayen d'akin ta amma batace komai ba, me Sarki Mu'az yake nufi da itane wai? ita ba uwarsa bace ba, matsayinta da queen mother batada wani isa ne kam da za'ake mata wannan abun?..

*Bansaniba ko kuma kun rud'e yanda na rud'e, ku sani ko hawa bamuyi bare gangara, kuna kallon wannan puzzle d'in, anya zamu iya kuwa....kumuje zuwa, kuci gaba da bibiyar alk'alamin Mom Nu'aiym domin jin yanda zata kaya..

Yawan comment yawan typing, i cannot come and kill my self....lolxxx.

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*JOIN OUR TELEGRAM PAGE TROU THE LINK BELOW.*
*https://t.me/joinchat/FgfKMiS_mYc-DIjC*

*WATTPAD @68billygaladanchi*

*My Sunita this whole page is for you, nagode da tsaftatacciyar k'auna Allah yabar so ya nunamun aurenki.*

*SHAFI NA SHIDA*

"A parlon k'asa ya taddata a zaune da cup a hannunta da alama wani abun takesha, tsayawa yayi yana kallonta ita kuwa idanta yana kan tv zahiri amma a bad'inin ta wani abun ne daban a ranta, rayuwarsa tana raya masa cewar yaje ya shak'o wuyanta seta dena numfashi, kamar ance ta waigo segata tana kallon sa, da fara'arta ta mik'e tazo daf dashi tace

"So nake inje inyi wanka aruwan sama, amma ba'a ruwan sama ya zanyi?" Wani irin kallon tsana ya wurga mata sannan ya janye jikinsa daga nata ya nufi sama, bin bayanshi tayi ta rik'e masa riga ta baya

"Dan Allah yaushe za'ayi ruwa, nace dakai so nake inyi shillalo na aciki" Hannunsa yakai ya bige mata hannu cikin fusata ya d'are matattakalar da gudu yanzu kam, shagwab'e fuska tayi wane zatayi kuka, shikuwa seda ya d'are sannan ya tsaya ya waigo yana kallon ta cikin wani yanayi mara misaltuwa tana abin yara tace

"Niko Niko banama sonka, idan kaga ina wasana karkazo kace ka sanni ma,nama gaya maka" Ta koma kan kujera ta zauna ta sadda kanta acikin cinyoyinta tanata k'unak'uni!!!

Ameena ce ta kalli barira suka shek'e da dariya k'asa k'asa, Barira tace "Sabon salo gemu a kafad'a yarinyar nan fa da sabon samfuri ta dawo daga asibitin nan, batasan d'an kurma bane ba, zataci ubanta" Amina na dariya tace

"Bakisan iskancin datamunba d'azu ai, kawai basega yarinyar nan ta zauna duk ta b'ata wuri da soyayyen k'wai ba, kamar 'yar shekaru biyu fa, aikuwa na fakaicin ido na mammari shegiya, abinda yaban haushi ma shine yanda ta koma tana kuka tamkar wata k'aramar yarinya" Tsaki Barira taja

"Tsiya d'inkin ludayi, ni kuwa d'azu rok'ana tayi in kunna mata TV cikeda ladabi, nace a ina suka samo wannan wawiyar, wai a haka prince mood zata aura, Allah da farko naso sosai tabar gidan nan, naso idan Fada abinda suka soma yad'awa ya yad'u" Tab'e baki Amina tayi

"Dama ta koma gidan princess Barra niba k'aramin dad'i najiba, ko uban me tazoyi mana yau oho" Dariya Barira tayi me sauti

"Ameena sekinyi kyau da zama princess, kafatanin hadimai da bayin gidan nanke babbar suce a iya iya hege,idan yau ace ki zama sarauniya niko zanta miki bauta kodan indinga kallon yanda zakike yarfa mutane" Kan Amina ne ya kumbura tana wata tafiya tace

"Da kuwa tafiyana ma canjashi zanyi zuwa irin na Prince D'an galadima" suka kuma kwashewa da dariya har suna tafawa...

Wayarsa ya zaro a aljihunsa yana mamakin zuwanta gidan, wane irin behaviour ne haka yarinyar nan kanta d'aya kuwa, da sauri ya rubuta wa anty Barra message
Chapter 10 · 0% Book details