← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 71

Sashe 27

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Halin ja'irancin ya motsa kuma, se kace kina jinjira kina zuba wannan shagwab'ar dan kinajin bacci" Nan da nan idanta ya kawo ruwa

"Ammu nifa baccin gaske nakeji zo zan kwanta so nake nayi pilo da cinyarki" D'auke kai Bahar tayi, k'wallan idanta ya gangaro

"Ammu dan Allah fa" Sauke ajiyar zuciya Bahar tayi sannan tace

"Tozo ki k'arasani, ubanki yana biyana kud'in jinyar k'afana idan kika b'allani da sakarcin ki" Tana murmushi tana share hawayen ta

"Dududu how many kg nake waighying haba Ammu"

"Naji zo ki kwanta d'in" Ran Khairiyya ya b'aci gata ita za'a nunawa gata ita dakeda Annah, in yanzu takeson ganin Anna kuma ta k'irata a waya tace tanaso su had'u acen tanaga se hirgin Annah ya riga nasu U.S, d'an gajeran tsaki taja wanda Hammood ma ya jita sannan ta kawar da dubanta daga garesu a ranta tana zagin dukkan su, ita ko wannan tsohuwar bataga dalilin dazesa a had'o ta da itaba a rayuwarta gaba d'aya ta tsani takura, dagani seta dinga shiga hancin ta, sam ita bazata lamunci shiga hanci ba dan babu wanda take zaman sa.

********************
    Zaman shirun ne ya ishi Jay ya kalli Barra cikin kulawa da tausayawa yace

"Barratu" Ita kanta duk sanda taji Jay ya kira sunanta gaba d'aya kai tsaye haka ta tabbatar koma menene magana ce dake neman nutsuwar ta, cikin tausayin kansu ta kallesa, amma batayi magana ba

"Kiyi Hak'uri Barra, banaso ko kad'an na ganki a irin wannan yanayin, gabaki d'aya hankalina seyake tashi gani nake tamkar nine sanadi, Barratu da sam ba haka kike ba, kowa yasanki da walwala amma acikin shekaru biyun nan kinfi ko yaushe sauyawa, Barrana tamkar akan aurena da zulaiha ne kika shiga wannnan rayuwar"  Hawayen idanta ta share sannan tace

"Jay ba haka bane wlh, kawai tausayin mu nakeji, ka k'ara aure ma amma ace ko zulaiha shiru har yanxu ko b'atan wata bata tab'a yiba ya zanji nikuwa" Murmushi yayi sannan yace

"Barratu mufa shekaru goma kawai mukayi bamu haihuba, wayasan inda rabonmu yake? kika sani ko lokacine beyi ba? inaga wannan ai shiga hurumin Allah mukeyi kawai hak'uri zamuyi da kuma addu'a" Aman dataketa yi tun safe ne ya kuma taso mata da sauri ta mik'e tana dafe bakinta tayi hanyar toilet, this fast few day's yana ganin sauyi sosai a wurin Barra, meke damunta batason sanar dashi? ya rasa gane kanta kwata kwata, da sauri ya bita toilet d'in ya taimaka mata ta kuskure bakinta sannan suka dawo bed room d'in, kallon tsukakken waist d'inta yayi acikin rigar dake jikinta wacce tabi lafiyar jikinta gaba d'aya, Barra jiki ta k'ara haka ya ayyana a ransa tana tsaye tana shan ruwa ajikin bedside, zuwa yayi ya d'aura hannun sa akan waist d'inta

"Barratu meke damunki wai? Kallon sa tayi idanta yana lumshewa

"Bacci nake yawan yifa, nafi 3month ina fama da cutar baccin nnan aika sani ko? to yanzu ko kitchen nake a zaune ma bacci nake, daga tsaye gyangyad'i nake" Murmushi yayi

"Ba bacci nake magana ba, wannana aman" D'an shiru tayi na wuccin gadi

"Amai ko? kaman zekai sati uku ba dama insha kamu, kuma inaso nasha amma duk nasha sena amayar nikuma bawai bari zan ba, kaga zulaiha tana jiranka please kazo ka wuce" Hannsa ya sanya ya shafi cikinta

"When last kikayi period? Da sauri ta juyo suka fuskanci juna

"Ko? hakane kuma yakai 4month yanzu, amma kasan bawai na saba yana zuwa wata wata bane shisa ban damuba, nikanyi 50days bezo ba amma 4moth bantab'ayi ba" K'irjin sane ya harba sannan cikin tsatsare ta da ido yace

"Kikace dani last week bakyason warin tea ko? kallon sa tayi "Ea bana so kam, k'arni madarar take mun?

"Amma nasan kinaso or have u ever felt that before? tana kallon sa tace "Wait could it be...... noooo that cnt be bazan tab'a haihuwa na sani" Murmushi tayi

"Banaso in saka raina yazo ba haka bane ba, but i notice some changes Barra, kin tab'ayin k'aton cikine? look at this fa wannan rigan dak'yar kike numfashi aciki" kallon cikinta tayi da sauri ta janye sa daga jikinta ta bud'e wardrop its being long tayi amfani da pt strip d'inta dakae ajiye park d'aya, toilet ta fad'a bayan ta zari hud'u seda tayi fitsari sannan dukkansu ta zura aciki ta jere akan wash hand base ta zuba tagumi🙀, gabaki d'aya atare suka jere mata result ta zuwan postive layi biyu ko wanne, cikin d'aya murya sosai tace JAYYYYYY..... A hanzarce ya rugo da gudu zuwa toilet d'in fad'awa tayi jikinsa

"Jay please take me to a near by hospital dukka layuka biyu suka nuna mun, inaso na tabbatar" Binsu yayi da kallo yana murmushi sannan cak ya d'aga suka nufi asibiti.

****************
   Zuwan su U.S.A da kwana biyu akayi waya akan maganar cikin barra lokaci d'aya Bahar ta tashi hankalin ta akan akawo mata 'yarta harta samu k'afa, Jay baze iya barin Barra ta tafi ita kad'aiba wannan ya sanya ake shirin tahowar su a tare.

Hafsat sosai takejin dad'in zaman garden, kwana biyu da zuwansu amma ta soma sabawa da zama wurin, yau gaba d'aya batajin lissafinta daidai koyaya Mood d'innan ze dubeta da 1yrs yace ze mayar da ita SS2, tayi wannan karatun yana gaya mata karatun cen dana nan ba d'aya bane after that kuma kawai har Ammu Bahar zasu daddage su sauya mata suna zuwa sunan sarki, sam bata k'aunar abinda ze rabata da marigayin ubanta mesa arayuwa zasu mata wannan rashin adalcin, Hafsat Habu mak'eri wannan shine sunan datafi sha'awar akirata dashi amma wani Hafsat Muhammad Takawa, sam tagode da d'aukakar amma banda na ture sunan mahaifinta, tsaki taja a karo na barkatai sannan ta mik'e zuwa cikin part gidan gaba d'aya fuska a shagwab'e, karo tayi dashi yana hanyar barin gidan, yauma kamar mayya hijabine ajikinta ya rasa uwar datake b'oyo, k'in matsawa tayi ya wuce ta daddage ta tsare gabansa, kamar yanda Ummin su ta Nigeria tace take kiranshi da suna Yaa Mood haka tace a shagwab'e

,"Yaa Mood magana nakeso zanyi dakai" Rab'eta yayi yana shirin wucewa ta rik'o hannun rigarsa

"Dan Allah ka tsaya ka saurareni mana yaa Mood" Lafiyyen mari ya sauke a kuncinta dayayi hanzarin gigita duniyar ta,lokaci d'aya ta dafe kuncinta cikin k'araji tace

"Ammu" k'afa yasa ya tad'e k'afarta datake shirin rugawa da ita atake ta fad'i wurin a kife ta buga goshi ta goga hanci bakinta ma seda ya bugu lokaci d'aya jiri me tsanani ya d'etaba, dafe kanta tayi tana ambaton sunan Allah, kukan ma ta gagareta, tana kallon sa ya wuceta yana tsaki yabar gidan, tun tana ganinsa dishi dishi har d'if komai ya d'auke mata. Khairiyya dake jikin k'ofa tsaye tare da kuyangin ta juyawa tayi ciki suma duk suka rufa mata baya, zama tayi ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya sannan tace

"Akwai wata Hadima acikin Hadiman b'angaren prince na Nigeria sunanta Ameena akwai watama Barira kaman itako tace sunan ta, ke Ummalo jeki ki kiramun su" A hankali ta mik'e bayan ta amsa da "To Ranki ya dad'e" sannan ta fito itace ta d'auki Hafsat dukda ba imata takeyi ta tafi da ita cen side d'in Bahar,gabaki d'aya ganin Hafsat a haka hankalin bahar tashi tayu ta soma k'ok'arin zuba mata ruwan sanyi ta samu kanta dak'yar, lokacin datake tambayar ta meya sameta se Hafsat ta tsinci kanta da kasa gayawa Bahar Gaskia tace fad'uwa tayi bayan datayi tintib'e..... Lokacin da su Amina suka isa wurin khairiyya zubewa sukayi cikeda ladabi suka gayar da ita ta amsa a wulak'ance sannan tace

"Ku zauna akwai abinda nakeeso in tambayeku, Allah yasa wata shegiya tamun k'arya kn ganeta kuga yanda zanyi saku" Amina ce ta fara sunkuyar dakai "KainHaba mu mun isa, ai rayukanmu ma zamu iya baki yar sarki jikar sarki matar eqrku kuma uwar sarki inshaa Allahu, ki dad'e kiyi k'arko ranki ya dad'e, da girman kunerar ki uwar marayu, kai dama masu iyaye duk uwarsuce ke, Allah yayi jagora me taimakon talakawa" Gyaran zama tayi kanta yana mata nauyi sabida ana shirin fasa mata shi, dukda zuciyar ta a jagule take sabida abinda ya faru da ita hakan be hanata jin tamkar tana akan gajimare sabida son girma

"Kece Amina ko? tana washe baki

"Nice Allah Ranki ya dad'e sarauniya a masarautar Baihatul mulk kuma Sarauniya a masarautar Daulatul Dinar, darajarki daban take data kowa, wanda duk Allah yaso bashida mak'iya, mak'iyanki fadawanki gimbiya khairiyya, Alherine ganinki me sunan Alheri" Kallon sosai khairiyya ta mata kafin tace

"Wacece uwargijiyar ki a fad'in masarautar ku?" Zubewa tayi tana k'ara k'ask'antar da kanta "Dakon jiran zuwanki nake Gimbiyar Alkhairi, banida wata uwarginiya sama dake kaf duniyar nan, me kike buk'ata daga gareni ya tabbata yanzu base anjimaba" Murmushin fuskar khairiyya ne ya k'aru da kalli mutanen ta tace

"Kubamu wuri" Sumsum duk suka watse banda Barira da aka kirasu tare, seda ta gama k'arewa yanayin su kallo sannan tace

"So nake ku bani labari gameda waccen baiwar datake tare sa Bahar sarauni, kunsan ni bak'uwace, Prince ya sanar dani cewan 'yar aikice in sakata duk aikin danake so amma mesa zatake takaran saka suturu irin na alfarma dani, hankalina be kwanta da ita ba sam" Kallon juna sukayi ta k'asan ido, Amina sarakan tsegumi ce tace

"Ai Ranki ya dad'e mu 'yan na gadane amma ita ai taka haye tayi, tsintarta akayi kinsan sarki da tausayi shine ya sakata acikin bayin gidan uban talakawa kenan, tofa shine aka turata Fadar Sarauni acen ne bahar tace tayi kamanceceniya da 'yar ta Zainaba da Allah yayiwa rasuwa, kinsan tsofaffi shine tace ta 'yanta ta ta mayar da ita yanda kika ganta, prince mood yafi kowa tsanarta, ko yanzu beso zuwa da ita amma Kinsan Bahar dolece ta saka akazo da ita badan rai yana soba" Nisawa Khauriyya tayi cikin samun relief

"Ohh Hakane, zan tabbatar mata da cewar itad'in 'yar aikice, seta yabawa aya zak'inta naga alamun neman had'a kafad'a take dani, ni zata kalla ta kirani khairiyya gatsai tsintacciya da ita" Cikin neman k'ara hura wuta Amina tace
Chapter 27 · 0% Book details