← Book details Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 71

Sashe 17

Tsintar Aya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hammude agidan ubanwa ka nemo wannan gayyar mayun, anya ba 'yar iska bace ba kuwa ? ke balagai balagai dake kike wannan sakalcin" sakeshi tayi tasoma bubbuga k'afanta a k'asa se kukan gaske kuma, nan ta zauna tayita yi, Bahar se banbami take, kawai jiri hafsat ta soma gani, da sauri ta dafe kanta daga tsayen datake, cikin seconds kad'an segata ta sulale a sume da sauri ya tareta ta fad'o jikinsa, an sanar dashi matsalarta, ba'aso tana yawan kuka, idan akaga tana abun rarrashi takeso ba fad' ba, zatayita samun suma ne har abinda ake gudu ya faru, kwantar da ita yayi agefe ya kalli bahar, da hannu ya mata nuni da ruwa ruwa, bata ko motsa ba se baiwace ta kawo ya yayyafa mata ta soma sauke gaurayen numfashi hular kanshi ta facecap ya cire yanata mata fita, bahar ta hard'e hannayenta tace

"Sabon salon la'anta, lallai ma kurma ka iya iskanci, rabu da wannan shashashar maza kazo abinda yasa nake nemanka daban" mik'ewa yayi ya soma janyo wayar sa, sak'o ya tura kamar haka

"Anty Barra, kizo fadar sarauni, that witch is sick again,suma ma tayi, kuma kuyiwa bahar bayanin yanayin ta, she's messing off here kuma sarai kinsan halin Bahar" yana aikawa ya kalli inda take kwance, har yanxu bata bud'e idanta ba, baze tafiba se Barra tazo dole, yana tunanin kiranta sega reply nata akan dama gidan zatazo.

Mom Nu'aiym.

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

JOIN OUR TELEGRAME PAGE TROU THE LINK BELOW.
https://t.me/joinchat/WVNVv7LzJdo-DIjC

*ASSALAMU ALAIKUM, INASO NAYI AMFANI DA WANNAN DAMAR WURIN MEMAN YAFIYAR DUK WANDA WANI ABU YA TAB'A HAD'ANI DASHI A MEDIA, DA WANDA MUKA FADA, WANDA NA ZAGESU A BAYANSU, WANDA NAYI GULMANSU IDAN MA NAYI, WANDA AKACE NAYI GULMANSU KODA BANYIBA,WANDA KE GANIN NA HAD'ASHI FAD'A DA WANI, WANDA KE GANIN RASHIN ADALCHINA, KAI DAMA WANDA KODA SUNANSA NA AMBATA A BAYANSA,DAN ALLAH YA YAFEMUN, ANATA MUTUWA BANNASO IN MUTU DA HAKK'IN KOWA AKAINA, NIMA NA YAFEWA KOWA DA ABINDA KAMUN INA SANE DA WANDA BAN SANIBA DUK NA YAFE, ALLAH YA SANYAYA ZUCIYAR DUK WANDA NA ZALINTA YAJI YA YAFEMIN HAR ZUCIYAR SA AMEEN. SAK'O BILLY GALADANCHI.*

*SHAFI NA TARA*

Be gama zama a parlon ba ta Barra ta shigo, a hautsine kallon sa tayi

"Meya sameta? K'ureta yayi da ido amma bece mata komai ba, kallon mahaifiyarta tayi

"Ammu Bahar, meya sameta haka? Yatsine fuska tayi

"Daga sama aka jehoki ne? Cikin damuwa tace

"Ammu dan Allah meya faru, koda yamun sak'o ina kan hanyar zuwa nan d'in dama"

"Yarinya sekace mahaukaciya Barratu, iya hege kala kala, abinci anbata ta dagula wuri, se sakalci wai dan an mata fad'a taketa kuka daga k'arshe segata tana fad'awa ajikin Hammude nace wannan wai salon son a la'anceka ne kaga laifin mutane" Nisawa Barra tayi

"To Ammu seme kuma ya faru?" Tab'e baki tayi

"Suma tayi hakanan kawai, shine sarakan tausayi ya rud'e dukya fita hayyacinsa, amma na kula tana numfashu ta dawo hayyacinta kamar baccine ya kwashe ta" Jinjina kai tayi

"Abinda Jay yace nazo na miki bayani kenan akan yarinyar nan Ammu, batada lafiya akanta, anan aka rasa meya fad'ota daga bene ta buga kai, shine ta samu cutar irin ta tab'uwar wani b'ari acikin kanta da wasu lokutan kawai seta sauyin abubuwa irin na yara, amma zaki iya wuni da ita koma kwana biyu abun be tashi mata ba, sabida haka dan Allah Ammu kiyita hak'uri da 222,idan ana hantarar ta inji likita setayita samun attack irin na suman nan, kuma idan har yaci gaba wata rana idan ta suman bazata sake farfadowa ba se mutuwa" Wara ido Bahar tayi

"Yau naji labarin Assha, anan gidan haka ya faru? Nan dai barra ta kwashe komai ta gaya mata har rashin lafiyar Hammude da aketa b'oyeta, anan Bahar ta fahimci tabbas gadar zare ake shiryawa Hammuden ta, sedai ita sam bata zargin yarinyar, duk yanda akayi wasu ne suke bibiyar ta ya ceceta, tinda har aka ganta da wuta me alamar k'arfe da zane ajiki, wama ya sani ko 'yan yankan kaine sukaso su hallaka ta ? Cikin nutsuwa ta kalli Hammood tace

"Hammude nasan kana jina, dalilin dayasa nayi kiranka anan dama shine in gaya maka, tafiya dai dazakayi America k'afata k'afarka, kana cika son sanya damuwa aranka kuma ni dama nagaji da zaman fadar nan, kasan halina batun yauba tun zamanin da banason takurar da akewa matam sarki, inaso inje ind'an sha iska inke d'ebe maka kewa, to amma wannan maganar da Barratu tazomun da ita akan maganar baiwar Allah cen ta sanya na sake shawara, ni dakai dakuma yarinyar nan atare zamuje America, dole semun nema mata lafiya acen d'in, lakurarta a hannunmu ya sameta dan haka ka shirya tafi banda bayi harmu biyun, akwai wasu bayi guda biyu dasuke b'angaren ka mata ina yabawa da kokarin su Barira da Amina dasu za'aje, Hammude banasanjin kamun gaddama munsan halin juna ai" Jinjina kansa yayi sannan da hannu yayi mata alamar aiba matsala, yazone ya gaya mata zeje wurin waccen yarinyar daze aura me martaba yace yaje gobe, to yau zebar garin sabida nisa inyaso ya isa gidan nasu gobe" Rabin rayuwar Hammude yayita ne awurin Bahar, lokacin kawunsa Jay shima hannun Bahar yake duk yanda yake magana ta fi k'owa k'warewa a wannan fannin,batace komai ba se jinjina kanta yaci gaba

"Mezan je dashi? yayi alamar tambaya? Gyaran zaman ta tayi

"Ka tab'a zuwa ka duba wannan wama sunanta" Gyaran zama Barra tayi tace

"Tace dani sunanta Hafsat ana kiranta 'yar shara" Da mamaki Bahar tace

"Yar shara kuma wannan wane irin suna ne na wulakanci?

"Haka dai tace sunan da ake kiranta Bahar"

"Karnaji wannan sunan agidan nan, akirata da Hafsat d'in nan, inba tsinancewa da lalacewa ba meye kiran sunan mutum had'e da kalmar shara fisabilillah, kai ina jinka nace itafa ka kai mata kyauta kaje kun gaisa? K'urawa Bahar ido kurin yayi aranshi yace wannan bak'ar munafukar zewa wannan akan me? ganin yayi shiru yace tace masa

"Nice uwarta Hammude, idan ka dawo daga Masarautaul Baihatul Mulk wurin amaryarka Lallai a kawowa uwargida Gaisuwa ta musamman tare da kyautar ban girma, ka girmi millions ina sane da hakan, kanada kud'i sosai dan haka kyautar gaske zaka shiryawa kowaccen su daidai" Barra ce tace

"Amma waccen ai saraki ce Ammu, yaya xa'ayi mata kyauta daidai da wannan tsintsacciyar magen sabamuda tabbas akanta ma" Harara ta wurgawa Barra

"Nice uwarta kuma nice ubanta, itama saraki ce dan kuwa itama 'yace awurin uwar sarki, sarki yayanta ne kuma d'an sarki zata aura, ku bakuda tunani tayaya za'ayi su shirya masa gadar zare da yarinyar kuma har yabi layi har haka, Allah shine yasan dalilin had'asu da Hammude amma ni wannan yarinyar dakuke gani koda ku yarda ko kada ku yarda nasan batada laifi batada masaniya, in har zata dauki komai banda azabar wuta, shidai ya taka sawun b'arawo su kuma sunyi amfani da wannan damar sunso su murd'e abubuwan su saka har ita, likitan dasukace yace ammata fyad'e ma k'arya suke, duk shirine shi Yayanki Tahir mugun gab'o ne sarautar ma da mace nayi ke zan bawa, yana kallo da sanya hannunsa ake cutar da nasa sekace besan halin fada ba da masarauta" Mik'ewa Hammood yayi ze fita ta rik'o hannunsa

"Banda iya shege mun gama da kaine? gidan wa zakaje da sanaben tsiya" kallon mamaki ta wurga mata sannan da hannu yace

"Duk abinda kikeso bahar ba musu zan miki zanyishi, kawai banda zuwa zance wurin waccen mayyar" Harara ta wurga masa a karo na barkatai

"Iya shegen banza, kaji yaro da kafid'inin tsiya, ban haifi mayya ba, duk wanda yace da Hafsat Mayya tokuwa tabbas niya cewa, zuwa gaisuwa kuma sekaje uwar saraki ma bare sarakin aikin banza aikin wofi, duk abinda ze la'anceku shi kukeyi dan shashancin wofi" Nisawa yayi Barra ta masa alama da ido akan yace to ya kalli Bahar ya mata nuni da cewa tayi hak'uri zeyi. Anan tace

"Lau dadai inga karshen fi'ili, yarinyar nan ina kallonta naji ta kwantamun arai, dan haka dole kowa ya sota, zanje in gayawa me martaban dakuke tak'ama dashi lallai abata matsayin gimbiya, ya mayar da ita halastacciyar 'yarsa niko tazama jikata, Tazama 'yar Sarauniya Maryama inga k'arshen wulak'anta ta, yarinya ko lafiya batada na tabbatar labarin ta seyayi abun tausayi" Nisawa yayi danyasan duk abubuwan nan data fad'a tabbas zatayi su, yana murmushi yace

"Nizan tafi" da hannu yayi alamar tace tana d'auke kanta

"Yadai fi mutum ya tsaya nemawa kansa la'anta, kuma ka tsaya kuduba yarimyar nan idan bataji sauk'i ba asibiti zamuje" Beyi musu sukaje kanta anan aka tasheta daga baccin daya sureta, tana farkawa ta takure wuri d'aya da sauri ganin Hammood, gayar da su tayi duk suka amsa banda hammood tace da Barra

"Anty Barra yaushe kikazo? Murmushi ta sakar mata kafin tace

"Kinata aikin bacci yaushe zakisan nazo" Murmushi tayi sannan tace

"Anty Barra dan Allah kije da Ammu Bahar take barina ina aiki, Allah banajin dad'in komai amun, nasaba da aikatau sosai, jikina baya karb'ar zaman nan" Murmushi Barra tayi tace

"Kinsan lafiya be isheki ba, ban b'oye miki komai ba akan Lalaurarki Hafsat, idan kikazo kina yawan aiki se abubuwa su iya taso miki"

"Anty na fahimci idan nacika zama ni kad'ai kaina seyayita ciwo daganan se inta bacci, gwara ina aikin sena dena tunanin komai" Shiru ta d'anyi kafin tace

"Zan soma tambayar likitanki idan zaki iya ayyuka Hafsat idan har babu matsala, amma idanda matsala sedai ki hak'ura gaskia".

******************
Chapter 17 · 0% Book details