Sashe 8
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
...........Innar Ma'u ce ta ƙaraso ta riƙe hannun A'isha, ganin yanda Inna take ƙoƙarin rikicewa yasa ta dube ta cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Karki tayar da hankalinki Asabe, na fi tunanin sumbatun ciwo take yi, kin san zafin zazzaɓi yana saka haka." Inna ta ce. "A'a Ladidi, taɓa jikinta ki ji babu wani zafi sosai, jikin nata ma fa ya yi sauƙi, gaskiya zazzaɓin jikinta bai yi yawan da zai saka ta sumbatu haka ba." Innar Ma'u ta ce. "To ko yunwa ce ta saka bata gani sosai? Kuma ga gari ya fara duhu shi yasa baza ta ga komai ba." A'isha dake sauraren su ta ce. "Innar Ma'u ba yunwa ba ce, gani ne bana yi, kuma idon ya mun nauyi." A rikice Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, wannan wanne irin ciwo ne haka? Daga zazzaɓi sai ki daina gani? Kuma ga idon naki nan babu alamar wani abu ya same shi, dan ko sauya kala bai yi ba." Innar Ma'u ta ja hannun Aisha suka fara tafiya ta ce, "Ina zuwa, bari na gwada wani abu." Mara mata baya Inna ta yi cikin tashin hankali. Kasancewar Innar Ma'u tana k'wan wutar sola a ɓangarenta sai ɓangaren ya samu wadatuwar haske sosai. Bayan sun shiga ɗaki ta cewa A'isha. "Kina gani yanzu?" Girgiza mata kai ta yi alamar a'a, fitila Innar Ma'u ta ɗauko ta haske idon A'isha, amma nan ma ta ce babu abun da ta gani. Hankalin Inna fa ya ƙara dugunzuma ta fara hawaye, jan A'isha ta yi jikinta tana ta duba idon nata kamar me neman abun da ya hana A'ishan gani. Ita ma A'ishan kuka ta fara tana faɗin. "Inna ki kai Ni a bani magani idona ya buɗe in cigaba da ganin ku." Rungume ta Inna ta yi ta ce. "Insha Allahu Idonki zai buɗe A'isha, ki cigaba da ganinmu." A'isha ta ce. "To Inna, raka ni in yi fitsarin." Innar Ma'u wadda hankalinta ya fara tashi ita ma da al'amarin ta kama hannun A'isha cikin sanyin jiki ta raka ta, ta yi fitsarin, dan sosai hankalin Inna ya tashi, kuka take yi ba kaɗan ba, jikinta gaba-d'aya ya yi sanyi, ga wata irin fad'uwa da gabanta yake yi. Cikin tausayawa Innar Ma'u ta dube ta bayan A'isha ta yo fitsarin ta ce. "Ki yi hak'uri Asabe, in Allah ya yarda ba wata matsalar ba ce, yanzu abun da za'a yi ki shirya mu je gidan Malam Ilyasu mai magani ya duba idon nata, ina da wasu yan canji za su ishe mu insha Allahu, tunda Ma'un ba ta dawo ba." Inna tana goge hawayen idonta ta ce. "Toh." Gidan Malam Ilyasu da ɗan nisa daga nan, dan haka Innar Ma'u ta ce bari ta yiwa Adamu ɗaya daga cikin yaran gidan magana tunda ranar Kasuwa ce duk suna nan ya kai su a babur ɗinsa, saboda kafin su samu na haya ɓata lokaci ne, dare ma ya yi duk sun tafi zai yi wahala su samu. Inna shiru kawai ta yi mata, amma ta san zai yi wahala ya je in ya ji su zai ɗauka. Suna soro suna jiran Innar Ma'u sai ga ta ita da Adamun, mamaki ne ya cika Inna ba kaɗan ba, amma dai ta shanye ta kama hannun A'isha da nufin su fara tafiya sai ta ji Adamu ya ce. "Aaa, Innar Ma'u ya na ga wannan Matar kuma? Da ita za mu tafi ne?" Cikin tausasa harshe Innar Ma'u ta ce. "Ita ma zaka ɗauka tare da Aisha ai, saboda A'ishan ma na kira ka, ka san ba ta da lafiya ba za ta iya doguwar tafiya ba." Adamu ya haɗe rai yana wani gyaɗa kai irin na wulak'anci ya ce. "Wallahi ba zan ɗauki Mayun nan a babur ɗina ba gaskiya, Innar Ma'u sai dai ki nemi wani." Innar Ma'u ta ce. "Haba Adamu, taimako fa zaka yi, kai ma watarana Ubangiji sai ya baka abun da ba ka yi tsammani ba sanadiyyar taimakon nan da zaka yi, dan Allah ka taimaka ka ɗauke su, ni sai in baka ɗan kuɗin Man babur ɗin ma." "Sai dai fa ki yi hak'uri gaskiya, dan baza ni ba." Adamu ya faɗi haka tare da juyawa ya yi tafiyarsa. Inna ta share hawayen idonta ta ce. "Mu je da ƙafa kawai Ladidi." Innar Ma'u ta ce. "Ya za'a yi mu je da ƙafa, ai mu in zamu iya zuwa A'isha baza ta iya ba." Inna ta ce. "Sai in goya ta." Innar Ma'u zata kuma magana, Inna ta katse ta da faɗin. "Karki damu zan iya, Ni dai burina mu yi mu je gurin mai maganin nan." Innar Ma'u ta ce. " To Allah ya kai mu lafiya." A hankali Inna ta zare A'isha wadda ta yi lamo a jikinta, sannan ta tsugunna ta ce ta hau bayanta. A'isha bata yi musu ba ta hau, Inna ta miƙe daƙyar har ta yi kamar zata tintsira saboda babu laifi A'isha tana da ɗan nauyi. Innar Ma'u ta ce. "Yi a hankali dai." Duk da Inna ta ji a jikinta da ta ɗauki A'isha amma haka ta daure ta jure suka je har gurin mai maganin, bayanta har sagewa ya yi, tana sauke A'isha ta shiga numfarfashi kuwa. Daƙyar suka samu ganin mai maganin, dan da farko cewa ya yi sai dai su dawo da safe yanzu dare ya yi. Innar Ma'u dai ta roƙe shi akan ya taimaka musu, ta faɗa masa daga ɗan nesa suke kuma da ƙafa suka zo. Tofi mai ganin ya yiwa A'isha a ido, bayan Inna ta yi masa bayanin abun da ya faru. Ya kuma ba su wani magani ya ce a haɗa mata da farin kwalli ana saka mata a cikin idon, indai jinnu ne kamar yadda suke tunani to idanun za su buɗe da yardar Allah, idan kuma har bayan kwana uku idon bai buɗe ba kuma an yi mata amfani da maganin to sai dai su je asibiti a duba mata idon. Godiya sosai suka yi masa sannan suka ba shi abun sadaka suka dawo gida, a dawowar ma haka Inna ta ƙara goye Aisha. Ai kuwa da jan ƙafa ta dawo gida, dan ba ƙaramin ciwo bayanta yake yi mata ba, gashi Innar Ma'u ta ce ta kawo ta taya ta da goyon A'ishan amma ta ƙi bata. Dan a ganinta hakan bai dace ba, ta ja ta sun yi tafiyar ƙafa kuma sannan ta ƙara mata da goyon ƴa. Duk da gajiyar dake addabar ta suna dawowa ta hau dakan maganin da suka karb'o, dan ita kawai burinta Allah ya buɗar mata da idon yarinyarta.