← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 55

Sashe 43

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy na zaune a parlour tana waya da ƙanwarta Khalifa ya shiga, ganin tana waya ya nemi guri ya zauna yana jiran ta gama. Hararar ƙasan ido ta wurga masa sannan ta ce. "Ina zuwa Kaltum zan kira ki." Ta ƙarashe maganar tare da zare wayar daga kunnenta ta katse kiran.
"Abba ne ya ce ki same shi a parlour'nsa yanzu ke da Baby." Khalifa ya faɗa a taƙaice, bai jira amsar ta ba ya tashi ya fita. Da wani mugun kallo ta raka shi, bayan ya fita ta ja tsaki tare da duban ɗaya daga cikin masu aikinta dake duƙe a gefe cikin jiran umarni, ta ce. "Ke! miƙo mini takalmin nan." Jikinta har rawa yake gurin amsawa tare da cika umarnin da ta ba ta cikin sakanni ƙalilan. Miƙewa Mommy ta yi ta nufi ƙofa cikin takun ƙasaita, da sauri mai aikin ta wuce gabanta ta buɗe mata ƙofa ta fita. Ba tare da sallama ba ta shiga parlour'n Abba ta zauna tana bin kowa da kallon ƙasƙanci, musamman Ummi da take jin tamkar ta shaƙe ta saboda tsana. Ba ta taɓa ganin A'isha ba tun da ta zo gidan, yanzu ma ba ta ga fuskarta ba kasancewar ta sunkuyar da kanta ƙasa. Taɓe baki ta yi ta dubi Abba ta ce. "Ga ni Alhaji an ce kana kira na."
"Na gan ki ai." Abba ya ba ta amsa da irin sigar da ta yi magana.
"To ina jin ka."
Girgiza kai kawai Abba ya yi ya ce. "Ina Baby?"
"Ta je gidan Bahijja." Ta ba shi amsa cikin tarar numfashinsa.
"Kuma shi ne har yanzu ba ta dawo ba ga Magriba ta kawo kai?" Ɓata fuska Mommy ta yi ta ce. "Mun yi waya ta ce mini ta taho." Bai bi ta kan maganar tata ba ya yi gyaran murya ya ce. "Masha Allah, mafi yawa daga ahalin gidan nan duk kun hallara, Safwan, Baby da Muneefah ne kawai babu." Ya numfasa idanunsa a kan A'isha ya ce. "Dalilin da ya sa na tara ku a nan shi ne don na sanar da ku wani abu mai mahimmanci da na zartar a cikin raina wanda duk ya shafe mu. Wannan Yarinya A'isha da tsautsayin accident ya haɗa mu za ta cigaba da zama a gidan har illa Masha Allah, a matsayin 'ya tamkar ƴaƴan cikina. Don haka ina gargaɗin ku akan kar na ji kar na gani wani a cikinku ya yi mata wani abu na muzanci ko wulaƙanci, idan hakan ta faru zan saɓar wa mutum fiye da tuanain shi ko waye." Mommy da take kallon shi tamkar idanunta za su faɗo ƙasa ta ce. "Alhaji ban fuskance ka ba, me kake nufi?"
"Komai ma." Ya ba ta amsa fuskarsa babu alamun wasa.
"Taɓɗijan!" Ta faɗa cikin tsantsar ɓacin rai da kololuwar takaici, lokaci ɗaya kuma ta saki wani murmushi, idanunta a kan Ummi ta ce. "Shikenan, Allah ya taya mu riƙo." Ta ƙarashe maganar tana miƙewa ta fice daga parlour'n.

Maganganun Abba sun saka A'isha a wani irin yanayi da ta kasa tantance na baƙin ciki ne ko akasin haka. Yau ta ƙara yarda mutum ba ya sanin yadda rayuwarsa za ta kaya sai ya ga yadda Ubangiji ya yi da shi, ba ta taɓa tunanin za ta yi rayuwa a wani gurin da ba garin da ta buɗe ido ta gan ta a ciki ba, amma ƙaddarar dake cikin rayuwarta ta ƙara jeho ta nan gidan, ba ta san kuma me zai faru a zamanta a cikinsa ba. Numfashi ta sauke a sanyaye ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ƙara arziƙi, ya sa aljanna ce makoma." Cikin kulawa Abba ya ce. "Amin Manana, Allah ya yi miki albarka ya ba ki lafiya." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Duban Maamah ya yi ya ce. "Kama hannunta ku koma part ɗin Mamanku, ta kwanta ta ƙara hutawa, na ga har yanzu jikin nata da saura."
"To Abba." Maamah ta faɗa tare da miƙewa. Khalifa ma tashi ya yi ya fita. Parlour'n ya rage daga Ummi sai Abba.
Ummi ta gyara zama tare da fuskantar Abba ta ce. "Al'amarin yarinyar nan ba ƙaramin ɗaure mini kai ya yi ba Abbansu, na kasa imagine yadda mutane biyu kacal za su yi rayuwa ba tare da wani jininsu ba, in ba dai a gidan marayu suka tashi ba." Abba ya ce. "Babu abin mamaki DR, hakan ya sha faruwa, kuma a yadda yarinyar ta ba mu labari ai kin ji mahaifiyar tata ta ce mata akwai dalilin da ya sa ta yi nesa da danginta, sanar mata ne Allah bai nufa ta yi ba har ta rasu." Ummi ta ce. "Haka ne Allah ya kyauta. Bari na je na shirya maka abin shan ruwa kar lokaci ya ƙure." Abba ya ce. "Toh shikenan, da daddare ma yi maganar diyyar matar, ki ba ni shawarar yadda kike ganin za a yi."
"Allah ya kai mu." Ummi ta faɗa tare da miƙewa ta fice.

Tunda Mommy ta koma part ɗinta ta kasa tsaye ta kasa zaune, ba ta son talaka da duk wani abu da ya shafe shi, ba ta san alaƙa da shi. Gani take tamkar talaucin zai goga mata. Ƴan aiki ma abin da ya sa take yin su don ta nuna isar ta ne da nuna ta kai matsayin yin su, amma ban da haka ba da ko gatekeeper ba za ta yi ba a rayuwarta. A haka Baby ta dawo ta same ta, ganin yanayin da take ciki sai ta ji babu daɗi a cikin ranta, da damuwa ta ce. "Mommy me ya faru? Ni fa ba na son na gan ki cikin ɓacin rai."
"Mahaifinki kuma burinsa kenan ya gan ni a cikin damuwa kodayaushe, duk abin da zai yi babu ruwansa da ɓacin raina a kai, in dai ƴar gold ɗinsa za ta yi farinciki shikenan, tunda Alhaji ya auri kinibabbiyar matar can na yi ban kwana da kwanciyar hankali da farinciki a gidan nan."
"Yanzu me ya faru?"
"Yarinyar da ya kaɗe ita ce wai za ta cigaba da rayuwa a gidan nan, don tsabar wani hali da son cusa mini baƙin ciki ba ma a matsayin ƴar aiki za ta zauna ba, wai a ƴa kamar ku. Kuma na san duk wannan abun tsinanniyar can ce ta kitsa masa shi." Ɓata fuska Baby ta yi ta ce. "Gaskiya Abba ya fiya janyo mana abin jin kunya da ƙasƙanci, yarinyar fa ƴar ƙauye ce, ranar suna hirar da Abba Abubukar na ji suna faɗa." Cikin ninkin ɓacin rai Mommy ta ce. "Wallahi matuƙar ina numfashi yarinyar nan ba za ta yi rayuwa a cikin gidan nan ba, gidan ɗana ne ai ba na Uban wani ba, mu zuba mu gani."
"Ya kamata dai ki ɗau mataki kam, kawai a wani kawo mana ƴar ƙauye gida mu rayu da ita, impossible wallahi, ko masu aikin gidan ba da daga ƙauye suke ba. Abba ma dai ya fiya kwashe-kwashe, daga accident ya haɗa ku sai ka ce za ka riƙe ta ban da ɗorawa kai." Ba tare da Mommy ta damu da kalaman da Baby take danganta Abba da su na rashin ɗa'a ba ta ce. "Ki bar ni da shi, wannan karon daidai nake da su dukansu."

Da daddare A'isha tana shan fruits ɗin da Ummi ta matsa mata ta sha a bedroom, Khalifa ya shigo ɗakin. Ba tare da ɗago kanta ba ta amsa masa sallamar da ya yi. Walking slowly ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta tare da saka hannunsa yana karkaɗawa a daf da idonta, gani yake kamar ta faɗa ne kawai amma tana gani, har yanzu mamakin jin wannan Black beauty ɗin makauniya ce bai bar shi ba. Kamar ta san me yake mata ta tsaya cak da shan fruits ɗin, yadda ƙamshinsa ya cika mata hanci ya sa ta gane yana kusa da ita. Murmushi ya yi ganin yadda ta yi da fuska ya ɗan ja baya tare da ajiye mata ledar hannunsa.
"Tsohuwa ga Ice cream nan na kawo miki, Allah ya sa kin iya sha?" Ya yi maganar cikin barkwanci. Yanayin yadda ya yi maganar sai ya tuno mata da Umar har ta ji gabanta ya faɗi, ko dan shi ma wani lokacin yana ce mata tsohuwa ne idan ya so tsokanar ta? Ko kuma don yana kawo mata ice cream ne? Zoben da ya ba ta, ta murza a hankali tare da yin ɗan murmushi ta ce. "Na gode." Murmushinta ya masa kyau sosai, har ya ji dama ta ƙara yi. Lumshe idonsa ya yi ya buɗe ya ce. "Don't mind beauty, Allah ya sa kar ya kashe miki wannan kyawawan haƙoran." Murmushi ta ƙara yi a karo na biyu ba ta ce komai ba, wanda tun kafin rayuwarsa Inna rabon da ta yi, sai yau da Khalifa ya sa ta yi ba tare da shirya ba. Don har yanzu zafi da ciwon mutuwar Inna yana nan danƙare a cikin zuciyarta. Khalifa zai kuma magana Ummi ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo. Tsare shi ta yi da ido ta ce. "What are you doing here?"
"Abu na kawo mata." Ya yi maganar cikin sauri yana shafa kai.
"To an gode." Ummi ta faɗa tare da nuna masa ƙofa alamun ya tashi ya fita. Mayar da dubanta ta yi kan A'isha ta ce. "NANA, taso mu je ku gaisa da Gwaggo Maman Abba." Da yake ɗazu ta ce da Nana za suna kiran ta sai ta gane da ita Ummi take, hakan ya sa ta yunƙura ta miƙe cikin rashin ƙwarin jiki, Ummi ta kama hannunta suka fita.

Zuwan Mommy parlour'n ba jimawa su ma suka shiga, tunda A'isha ta zo gidan ba ta taɓa ganin fuskarta ba, saboda duk kwanakin da suka yi a asibiti ba ta je ta duba ta ba, ɗazu kuma a parlour'n Abba ba ta ga fuskarta ta ba. Ummi na ƙoƙarin zaunar da A'isha a kan carpet Mommy ta kalle ta, wata mummunar faɗuwar gaba da razani ne suka yi mata dirar mikiya a lokaci guda, sanadiyyar kallon farko da ta yi wa fuskar A'isha a rayuwarta.........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖

*_Zeey Kumurya_*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*2️⃣6️⃣*
Chapter 43 · 0% Book details