← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 55

Sashe 5

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daren Yau Inna bata rintsa ba, tunanika kala_kala ta kwana tana yi. Na farko tana tunanin yanda rayuwarsu zata kasance nan gaba a halin da suke ciki, na ƙyara da nuna musu tsana ƙarara da mutanen gari ke yi. Na biyu kuma halin babu da suke ciki, dan yau ma gidan wata mata da suke mutunci ta je a can unguwar Sabon gari ta taya ta aikin k'uli_k'ulin da Matar take yi na siyarwa, shine ta samu matar ta bata k'ulin da ɗan Kuɗi wanda a cikinsa ta siyowa A'isha awarar da ta bata ta ci, ita kuma a gidan matar ta ci abinci. Washegari da zazzaɓi da ciwon kai A'isha ta tashi, sai Inna ta danganta hakan da kukan data ce mata ta yi ne a makaranta da kuma zaman da ta yi da yunwa bata ci abinci ba Jiya.

Ƙarfe Bakwai na safe Inna ta fita ta siyo mata koko da k'osai ta dawo. Tabarma ta shimfid'a a tsakar gida ta ɗauko A'isha ta kwantar da ita a kai. Inna tana taɓa goshinta ta ce. "Jikinki ya yi zafi sosai A'isha, tashi ki sha kokon nan ko yaya ne, anjima sai in siyo miki magani ki sha." Girgiza kai A'isha ta yi tare da lumshe idanunta. Inna ta ce. "Daurewa zaki yi ki ɗan kurb'a, ai ba zai yiyu ki zauna baki saka komai a cikinki ba." A'isha tana taune lips ɗinta ta miƙe daƙyar ta zauna ta jingina bayanta da jikin bango. Inna tana zuba mata sugar a cikin kokon ta ce, "Sannu, Allah ya sauwak'e." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. A baki Inna ta bata kokon ta yi kurb'a ɗaya ta kau da kai, Inna ta ce ta daure dai ta ƙara sha. Tana ƙara kurb'a sai kakarin amai, kafin ta yunk'ura ta miƙe har ta fara aman a gurin. Inna ta riƙe ta tana jera mata sannu cikin tausayawa. Bayan ta gama Inna ta dauraye mata fuska da baki ta cire mata rigar jikinta da ta ɓaci da amai. Cikin Muryar marasa lafiya A'isha ta ce. "Inna ki mayar da ni ɗaki ki lullub'e ni sanyi nake ji sosai." Inna ta ce. "Toh." Sannan ta kama ta, ta kai ta ɗakin ta kwantar da ita, cikin ikon Allah sai bacci ya ɗauke ta. Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta fito tsakar gida ta fara ɗan ayyukan gida, jikinta duk ya yi sanyi da yanda ta ga jikin A'ishan. Da Ma'u ta biyo mata makaranta Inna ta sanar da Ma'un baza ta samu damar zuwa ba, bata jin daɗi, Ma'u ta shiga ɗaki ta duba ta sannan ta yi mata addu'ar samun sauƙi cikin tausayawa.

Wajen ƙarfe goma na safe har lokacin A'isha tana ɗaki tana bacci, Inna kuma tana tsakar gida tana karyawa aka yi sallama a zagayen nasu. Inna ta amsa tare da duban Matar da ta shigo, duk da ba ta taɓa san ta ba amma ta tarb'e ta cikin fara'a tare da bata gurin zama. Bayan sun gaisa Matar ta ce. "Na san baki gane ni ba ko?" Inna ta ce. "Gaskiya, dan zan iya cewa ma ban taɓa ganin fuskarki ba." Matar ta yi murmushi ta ce. "Haka ne, Nima ban taɓa ganinki ba sai yau, kuma na zo gurinki ne da wata samuwa da nake fatan zaki karɓe ta hannu bibbiyu." Inna ta ce. "Samuwa kuma? Wacce iri?" Matar ta gyara zama ta ce. "Da farko dai Sunana Hajiya Kareema, Ni mazauniyar ƙasar Saudiyya ce a can nake kasuwanci na." Inna ta jinjina kai tana ƙara bin matar da kallo, a ranta tana mamakin dalilin zuwanta gurin ta. Matar ta cigaba da magana da faɗin. "Shekaran jiya na zo nan gurin Ramatu abokiyar zamanki, sai yarinyarki A'isha ta shiga zagayen su, anan na gan ta, dalilin zuwana ma gurinki a yanzu saboda ita ne." Inna ta ce. "To, Allah yasa ba wani abun ta yi miki ba?" Hajiya kareema ta girgiza kai tana bin zagayen su Inna da kallo sannan ta ce. "Na zo ne in tallata miki wata hanya ta samuwa kamar yadda na faɗa miki tun farko, duba da yanayin talauci da k'uncin rayuwa da kuke ciki na ji ina son in taimake ku." Inna ta ce. "Taimako kuma wanne iri?" Hajiya Kareema ta tauna cingum ƙas_ƙas sannan ta ce. "Yarinyarki A'isha zaki bani in tafi da ita Saudiyya komawar nan da zan yi ta nemar muku kuɗi a can, cikin ƙanƙani lokaci zaki ga kakarku ta yanke saƙa kun yi bankwana da talauci, zaku samu kuɗi sosai wanda zai isa ku bar wannan ƙauyen ku fita duk inda kuke so a cikin birni ku gina gidanku na zamani, ku ji daɗin rayuwarku. Musamman ma da ya kasance A'isha kyakkyawa ce gata da ɗan dumurmur ɗin jiki za'a amfana da ita sosai" Ta ƙarashe zancen tare da sakin wani irin murmushi............✍️

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*0️⃣4️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
Chapter 5 · 0% Book details