Sashe 17
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
.........Wani kyakkyawan Matashi ne ya fito daga cikin gidan Sarki hannunsa riƙe da umbrella. Sai da ya zo zaure sannan ya tsaya yana nannad'e umbrellar. Dai_dai nan Allah ya bawa A'isha sa'a ta gantsarawa Hamza cizo a tafin hannunsa, cikin sauri Hamza ya janye hannun nasa saboda azabar zafin da ya ji ya shiga yarfa hannun, hakan ya bawa A'isha da ta fara fita daga hayyacinta damar ƙwala ihu. Cak matashin ya tsaya a inda yake cikin mamakin abun da kunnuwansa suka jiyo masa, kalle_kalle ya fara yi dan idan ya ji dai_dai kamar a cikin zauren aka yi ihun. Wani ihun A'isha ta ƙara yi saboda marin da Ɗan_juma ya wanka mata, wanda ya yi tunb'ur haihuwar uwarsa. Kallon ƙofar ɗakin Ɗan_juma Matashin ya yi, haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta ba da ihun da yake jiyowa, lemar hannunsa ya ajiye cikin sauri ya nufi ɗakin ya buɗe ya shiga. Tozali ya yi da Ɗan_juma tsirara yana ƙoƙarin cirewa A'isha riga, ita kuma sai jujjuya kai take yi hawaye na shatata daga cikin idonta. Cikin kid'ima ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, mene haka? Me kuke shirin aikatawa?" Juyawa su Hamza suka yi suna kallon sa a rud'e. Banda Ɗan_juma da ya cigaba da abun da yake yi, dan tunda ya samu wannan damar yau ba zai so ta kufce masa ba, bai ga kuma uban da ya isa ya hana shi yin abun da ya yi niyya ba. Runtse ido Matashin ya yi ya buɗe cikin tsananin ɓacin rai ya ƙarasa inda suke ya daddage ya saukewa Ɗan_juma wani uban naushi a tsakiyar gadon bayansa, gantsarewa Ɗan_juma ya yi dan naushi ya shige shi ba kaɗan ba, wani naushin Matashin ya ƙara sakar masa wanda ya saka shi yin taga_taga ya faɗi a ƙasa yana faɗin. "Aushh.....!" Ganin haka su Hamza suka miƙe cikin hanzari da niyyar guduwa, Matashin wanda zuciyarsa ke wani irin tafarfasa saboda baƙin ciki ya cakumo su dukan su ya bazar da su a ƙasa, ya ba su nasu rabon naushin. Sai ga su gaba-d'ayansu duka a ƙasa suna sassauke numfarfashin wahala. Jikin Matashin gaba-d'aya tsuma yake yi, kyawawan fararen idanunsa sun kada sun yi jajur. A hankali ya ƙarasa ya tsaya yana kallon A'isha wadda tuni ta sume, cikin sauri ya dauko hijibinta ya zira mata sannan ya ciccib'e ta ya fice da ita daga cikin ɗakin, sai a lokacin ya lura da jakar makarantar ta dake yashe a ƙasa a cikin zauren. Girgiza kansa kawai ya yi ya nufi wata ƙofa dake pacing ɗin ɗakin Ɗan_juma ya buɗe da key ya shiga. Akan ƙatuwar katifar dake ɗakin ya shimfid'e A'isha, sannan ya fito ya ɗaukar mata Jakarta ya koma ɗakin, har lokacin ruwa ake yi bana wasa ba.
Zama ya yi a gaban A'isha yana sassauke numfashi, ƙura mata ido ya yi cikin tsananin tausayinta na ƙoƙarin keta mata haddi da su Ɗan_juma suka yi, fuskarta ta yi jajur saboda kukan da ta sha, shatin hannun Ɗan_juma rud'u_rud'u akan fuskarta. Haka kawai ya ji gabansa ya yanke ya yi wata irin fad'uwa, kasa ɗauke idonsa ya yi daga fuskar A'isha, lokaci ɗaya bugun zuciyarsa ya sauya, ta fara bugawa da sauri_sauri. Daƙyar ya yi ta maza ya janye idonsa daga kan A'isha ya miƙe ya nufi ledar pure water ɗin dake ɗakin ya dauko ɗaya ya bula ya shiga shafawa a fuskar A'isha zuwa wuyanta, tsawon mintuna biyu yana hakan sannan ya ji ta ja wani gauron numfashi, lokaci ɗaya kuma ta yi yunk'urin miƙewa jikinta na wani irin k'yarma tana kiran sunan Inna, tare da ƙoƙarin kai hannu tana dukan iska alamar son k'watar kai. Cikin tausayawa ya riƙe hannunta, so cool ya ce. "Sorry." A'isha ta fizge hannunta tare da ja baya ta fashe da kuka ta ce. "Su waye ku? Me yasa kuke son cutar da ni? Me na yi muku?" Ta ƙarashe maganar tare da tashi zaune. Lumshe ido ya yi ya buɗe saboda a yanzu A'isha ta buɗe idonta wanda ke cike da zallar firgici da tsoro, kallon idanun nata kuwa ya ƙara masa saurin bugun zuciyarsa gami da faduwar gaban da ta fi ta ɗazu. Cikin rarrashi ya ce mata. "Ki kwantar hankalinki, because by now ba kya hannun masu son cutar da ke, Ubangiji ya kub'utar da ke." A'isha ta ƙara volume ɗin kukunta ta ce. "Waye kai? Ni ka kai ni gurin Innata." Tana yin maganar ne cikin tsananin tsoro da firgicin da yake tabbatar da a cikin razani take, sai dunk'ule jikinta take yi guri guda. Bai kuma cewa komai ba ya miƙe ya fita ya lek'a waje ya ga har lokacin ruwa aka yi, amma an fara ɗaukewa. Tsayawa ya yi yana kallon ɗakin Ɗan_juma, zuciyarsa cike mamakin sa ba ɗan kaɗan ba, bai taɓa tunanin hakan daga Ɗan_juma ba, fyaɗe fa? Har su uku akan ƙanƙanuwar yarinya, wannan wanne irin zalunci ne haka? Ya manta rabon da ya yi tozali da abun da ya tayar masa da hankali kamar wannan. Yana nan tsaye har ruwan ya ɗauke ya koma sai yayyafi kaɗan_kaɗan saboda gabatowar lokacin Sallar Magriba. Juyawa ya yi ya koma cikin ɗakin, a tsakar ɗakin ya tarar da A'isha tana laluben hanya cikin kuka, riƙe ta ya yi ya ce. "Sorry, ruwa ake yi ne sai yanzu ya ɗauke, mu je in raka ki gidan." Wata k'ak'k'arfar ajiyar zuciya A'isha ta sauke tare da kallon fuskarsa kamar mai iya ganin sa, haka kawai ta ji zuciyarta ta ɗan nutsu da shi, murmushi ya sakar mata sannan ya cika ta ya ɗaukar mata Jakarta ya nuna mata ƙofa ya ce. "Mu je ko?" A'isha dake jin duk jikinta na yi mata wani irin ciwo ga juwa dake ɗiban ta, ta kai hannu ta lalubi bango ta dafa, cikin muryarta da ta ci kuka ta ƙoshi ta ce. "Ba na gani, sai dai a riƙe mun hannuna." Cak ya tsaya yana kallon ta cikin shock yana maimaita abun da ta faɗa a cikin zuciyarsa, ba ta gani? What she meant? Ita makauniya ce ko me? Ya faɗi haka a cikin zuciyarsa. Numfashi ya sauke a hankali ya ce. "Ok." Sannan ya kama hannunta suka fice daga ɗakin, ko rufe dakin bai yi ba suka yi waje. Suna fita ana fara kiran Sallah, Allah ya haɗa su da wasu yara suka nuna masa gidansu A'isha daga nan, kamar yadda ta ce masa ya tambayi wani ya nuna masa da ya tambaye ta ina ne gidansu.