← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 55

Sashe 25

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........Cikin gigita A'isha ta ƙwalla ƙara tare da sakin kuka, hankali a tashe Umar ya riƙo ta kafin su kai cikin ruwan ya rungume ta da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya dafa wani dutse dake bakin ruwan, amma duk da haka sai da ƙafafuwansu suka shige cikin ruwan ya kawo har gwiwoyinsu. Mutanen gurin gaba-d'aya suka yo kansu suna salati tare da kallon Ɗan'juma wanda shine ya hand'aka sun. Cikin sauri aka zaro su daga cikin ruwan, innalillahiwa'inna'ilaihirra'un kawai Umar yake maimaitawa cikin kid'ima, dan shi ba ma ta kansa yake yi ba ta A'isha yake ita da ba ta gani. Ita kuwa ta ƙi sakin shi sai kuka take, dan ta tsorata ba kaɗan ba. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Umar ya saki ya yiwa mutanen da suka ciro su godiya. Sannan ya juya ya kalli Ɗan'juma dake tsaye yana ta muzurai shi kaɗai, ji ya yi kamar ya damk'o shi ya naɗa masa na jaki, amma darajar Mahaifinsa yasa ba zai iya aikata hakan ba. Ɗauke idonsa ya yi daga kansa ya zare A'isha daga jikinsa a hankali sannan ya tsugunna dai_dai tsayinta ya shiga share mata hawayen fuskarta, so cool ya ce. "Sorry Dear, ki bar kukan nan haka Please, ko kina jin wani ciwon a jikinki ne?" Hannunsa ta riƙe gam cikin kuka ta ce. "Mu tafi gida ni dai ka kai ni gurin Inna." Gabad'ayanta a tsorace take, sai ajiyar zuciya take saki akai_akai. Cikin lallashi ya ce. "Yanzu za mu tafi, amma Please ki bar kukan kin ji?" Gyaɗa mata kai kawai ta yi amma ba ta bar kukan ba. Miƙewa ya yi ya kama hannunta suka tafi bayan ya ɗauko mata takalmanta ta saka. Kafin su shiga gida sai ya rararrashe ta, ta bar kukan da take yi gudun kar hankalin Inna ya tashi. Suna shiga tana jin muryar ta tafi ta faɗa jikinta ta fara hawaye. Inna dake kallon su cikin mamaki ganin duk rabin jikinsu a jik'e ta ce. "Lafiya kuwa?" Cikin son kwantar mata da hankali Umar ya ce. "Lafiya lau Mama, a bakin ruwa muka zauna muka zira ƙafafuwanmu a ciki." Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Na san ita ta takura maka kuka shiga, dan na san ta da maitar hakan, to kuma me aka yi mata take wannan kukan?" Shafa kai Umar ya yi ya ce. "Wai dan mun taho gida yanzu ne." Tsaki Inna ta yi ta ture ta daga jikinta ta shige ɗaki tana faɗin. "Ki rufe mun baki ko jikinki ya faɗa miki, idan ba ku taho ba kwana kike son ku yi a can?" Kama hannunta ya yi ya zaunar da ita akan kujera ya shiga share mata hawaye, a hankali ya ce. "Dan Allah ki bar kukan nan Humairah ko kina so nima in yi?" Girgiza kai ta yi. Ya ce. "To ki daina, ba ki san yanda nake ji ba ne a cikin raina idan na ga kina kuka." Barin kukan ta yi cikin sanyin murya ta ce. "Na tsorata sosai Yaya Umar, na ɗauka za mu faɗa cikin ruwan ne, kuma na san da mun faɗa mutuwa za mu yi." Yana goge mata hancinta da handkerchief ɗinsa ya ce. "Ki bar zancen nan kar Mama ta ji, kuma ko na tafi kar ki faɗa mata ki ce mun kusa faɗawa ruwa." Ta ce. "Me yasa?" Ya ce. "faɗa zata yi miki mana, kuma ba za ta ƙara barin ki ki fita ko nan da soro ba, kin sani." Gyaɗa masa kai ta yi a hankali. Ya shafi kuncinta ya ce. "Good Girl, bari na tafi Magriba ta kusa." Ɓata fuska ta yi ba ta ce komai ba. Murmurshi ya yi ya ya miƙe ya yiwa Inna sallama ya tafi. Bayan Fitar sa A'isha ta cewa Inna za ta yi wanka dan wari iri take jin jikinta, sai da ta yi Sallah ta ci abincin da Inna ta matsa mata ta ci kaɗan sannan ta yi wankan ta kwanta. Bayan Sallar isha'i Umar ya je shop ya yiwa A'isha siyayyar kayansu Biscuits da choculates da sweets masu yawa. Lokacin da ya je kai mata ta yi bacci sai Inna ya bawa ta ajiye mata. Inna tana duban ledar da aka zubo kayan cikin mamaki ta ce. "Umar wannan fa na mene ne?" Kansa a ƙasa ya ce. "Na A'isha ne Mama." Inna ta ce. "Haba Umar, wannan siyayyar ai ta yi yawa." Bai ce komai ba. Inna ta ce. "Toh an gode, Allah ya saka da Alkhairi ya biya ka da gidan aljannah, amma ba dan ba da na baka ka mayar da kayan nan inda ka siyo su ko ragewa ne a yi, wahalar ai ta yi yawa." Murmurshi ya yi ya amsa da Amin sannan ya yi mata sallama ya tafi. Ita kam Inna har cikin ranta ba ta son kashe_kashen kuɗin da Umar da yake yiwa A'isha, dan kwanaki haka ya kawo mata sabulan wanka masu ƙamshi da na wanki da toothpaste da man wanke gashi. A ganin ta d'awainiyar da yake yi da su ta yi yawa.

Wajen ƙarfe goma na dare Umar yana kwance yana operating system kira ya shigo cikin wayarsa, ɗaukar wayar ya yi ya duba, Abbansa ne yake kiran, d'agawa ya yi ya kara a kunnensa tare da yin sallama. Daga ɗaya ɓangaren bayan Abban ya amsa ya ce. "Umar ya aikin? Da fatan komai lafiya babu matsalar komai?" Umar ya ce. "Alhamdulillah Abba komai lafiya." Abba ya ce. "To Masha Allahu, Allah ya taimaka.... ɗazu Mamanka take sanar mun wai ka ce a cikin satin nan zaka dawo? Har ka gama abun da ka je yi ne?" Ɗan jimm Umar ya yi sannan ya ce. "Ban gama ba Abba da ɗan saura, ita ce dai ta ce sai na dawo ɗin." Abba ya ce. "Me yake damun Amina ne? Ni ban san mene matsalarta da zamanka a garin nan ba, ta bi duk ta damu kanta kullum cikin zancen take yi, na faɗa mata ba inda za'a cutar da kai na tura ka ba, dan na san halin abokina mutumin kirki ne." Umar ya ce. "Ka yi hak'uri Abba, amma zan taho cikin satin nan ɗin Insha Allah tunda haka take so." Abba ya ce. "Ba zai yiyu ba, ka tsaya ka yi abin da ka je yi a tsanake, idan ka gama sai ka dawo, ita kuma ka barni da ita." Umar ya ce. "Tom shikenan Abba Na gode, Allah ya ƙara girma." Abba ya ce. "Yawwa, ka ci gaba da kula dai, Allah ya taimaka ya yi Albarka." Umar ya ce. "Amin Abba." Daga nan suka yi sallama Abba ya katse kiran. Wani kiran ne ya ƙara shigowa cikin wayarsa, kallon wayar ya tsaya yana yi, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya d'aga tana gaf da katsewa ya kara a kunnensa bai ce komai ba. Ɗaga ɗaya ɓangaren aka ce. "Ya Faruq me na yi maka ne duk ka canza mun?" Umar ya ce. "Chanji kuma? Wanne iri Khausar?" Cikin damuwa ta ce. "When last rabon da ka kira ni ko ka mun magana a chat? Ina ga tun kafin ka yi tafiyar nan fa." Numfashi Umar ya sauke ya ce. "Toh shikenan ki yi hak'uri abubuwa ne suka shamun kai, Ya kike ya su Mommy?" Khausar ta ce. "Kowa lafiya ƙalau, amma ban da ni da nake cikin kewar ka, yaushe zaka dawo?" Umar ya ce. "Nan da 1 month insha Allah." A sanyaye ta ce. "Allah ya kai mu, amma kamar ya yi yawa ya Faruq, har 1 month zan ƙara ban gan ka ba, bayan kwanakin da na yi a baya?" Umar ya ce. "Ba wani yawa, kamar yau ne zaki ga kwanakin sun wuce har na dawo." Khausar ta ce. "To, Allah ya kai mu, baka ji daɗi da farincikin da nake ji ba yau na ji muryarka." Umar ya ce. "Haka ake so, yanzu ina ɗan yin wani aiki ne, I will call you later." Bai jira cewarta ba ya katse wayar ya cigaba da abun da yake yi. Washegari Umar ya je gidansu A'isha kamar yadda ya saba zuwa, ya tarar Inna tana yiwa A'isha tsifar kai. Bayan sun gaisa da Inna ta tufkewa A'isha gashin da aka tsefe ta ce mata ta ɗaure kanta idan Umar ya tafi ta cigaban mata, sannan ta tashi ta shige ɗaki.
Chapter 25 · 0% Book details