Sashe 28
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Umar ne zaune akan kujera ƴar tsugunno yana kallon A'isha dake zaune akan tabarma, sanye take cikin atamfa mai kyau ɗinkin doguwar riga, ɗinkin ya yi dass a jikinta kasancewar yanzu ta ƙara murjewa sanadiyyar cima mai kyau da kuma kwanciyar hankali da suka samu. Atamfar da Innar Ma'u ta ɗinka musu ce Sallar da ta wuce, Inna ta yi mata d'auri duk da ba wani na gayu ba ne amma ya yi mata kyau, fuskarta ta sha powder da Umar ya siya mata, ɗan ƙaramin lips ɗinta sai k'yalli yake na white lipstick. Kallon ta yake yi cikin wani irin yanayi ko ƙifta idonsa ba ya yi, zuciyarsa na bugawa a hankali a hankali, wani irin son A'isha da tausayinta na ƙara mamaye ko'ina a cikin zuciya da gangar jikinsa, har mamakin kansa yake yi yanda a cikin 5 months ya faɗa cikin irin wannan zazzafar soyayyar akan ƴar ƙanƙanuwar yarinyar da ko autarsu ta girme ta, ko a mafarki bai taɓa tunanin hakan zai kasance da shi ba. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, cikin kulawa ganin yanayin A'isha ya ce. "Me ya faru kika yi shiru Humairah? And yanayinki ya nuna mun kamar akwai abun da yake damunki, tell me what happened?" Idanun A'isha akan fuskarsa kamar mai ganin sa cikin sanyin murya ta ce. "Ban san me yake damuna ba nima, kawai ina jin jikina babu daɗi ne." Umar ya ce. "Ko ba ki da lafiya ne?" Girgiza masa kai ta yi ta ce. "Lafiyata ƙalau, kawai gabana ne yake ta fad'uwa." Umar ya ce. "Subhanallahi, ki dinga maimaita innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, ko kina ambatar sunan Allah, za ki ji sauƙin abun." Ta ce. "Toh, Insha Allahu." Numfashi Umar ya sauke dan shi ma haka kawai ya ji jikinsa da zuciyarsa wani iri, bai kuma san dalili ba. Kamar A'isha za ta yi kuka ta ce. "Ni fa Yaya Umar a rayuwata so nake kawai in gan ka, in ga ya kake, amma na san daƙyar idan hakan za ta faru." Hannunta Umar ya kama ya ce. "Watarana za ki ganni Insha Allahu Humairah, a cikin watan nan nake so mu tafi Kano a duba miki idonki a yi miki magani, ki daina damuwa Insha Allahu zaki warke ki cigaba da gani kamar kowa." A'isha ta ce. "Allah ya yarda." Murmurshi Umar ya yi ya ɗauko key ɗinsa ya gogawa A'isha a gefen wuyanta, ɗan zabura ta yi ta sosa wurin tana ɓata fuska, kan ƙafarta Umar ya kai key ɗin ya ƙara goga mata, da sauri ta janye ƙafar a tunaninta wani k'waron ne yake bin jikinta. Murmurshi Umar ya yi mai sauti ganin yadda ta zama uncomfortable a gurin sai juye_juyen kai take yi. Turo baki ta yi ta ce. "Kai kake saka mun wani abun a jikina ko?" Umar ya ce. "Ba ni ba ne, Ni wayata ma nake kallo." Ta ce. "Na san kai ne, ai ba yau ka saba mun haka ba." Uwar ya ce. "Ba fa ni ba ne." Shiru ta yi alamar ta yi fushi. A hankali ya ce. "Sorry Dear na daina." A'isha ta ce. "Ai na san baka daina ba, kullum sai ka tsokane ni ka tsorata ni, ranar nan har kuka ka saka ni dan ka ga bana gani." Cikin shigar rarrashi ya ce. "Na ce fa ki yi hak'uri na daina daga yau." A shagwab'e ta ce. "Ba zan hak'ura ba ni dai, kuma ba ruwana da kai." Umar ya marairaice ya ce. "Please... Ni ne fa, dan Allah ki yi hak'uri." A'isha ta ce. "Tom shikenan na hak'ura." Ya ce. "Yawwa Darling, kawo hannunki ki ga wani abu. Ba ta ce komai ba ta miƙa masa hannun damanta. A hankali ya zare wani ring ɗin azurfa mai kyau dake ƙaramin finger ɗinsa ya zira mata a babban ɗan'yatsanta yana kallon cikin idonta. Zare hannunta ta yi daga cikin nasa a hankali ta shiga murza zoben da ya saka mata da murmurshi ɗauke akan fuskarta. Umar ya ce. "Wow ba ki ga yanda ya yi miki kyau ba." Ta ce. "Ka bar mun ne?" Ya ce. "Eh mana, dan ma sauran sun miki yawa ne da duka na hannuna zan baki." Ta ce. "Saboda me? Kai baka so ne?" Ya ce. "Zuciyata ce kawai ta bani umarnin in bar miki su." A'isha ta ce. "Na gode, amma na ji ya ɗan mun yawa fa, ba zai faɗi ba." Umar ya ce. "Ba zai faɗi ba, ai ba sosai ya yi miki yawan......" Vibrate ɗin da wayarsa ta fara ne ya katse masa maganarsa. Zaro wayar ya yi daga aljihun gaban rigar sa ya duba, Mom ce take kiran sa, haka kawai ya ji gabansa ya yanke ya faɗi. Jiki a sanyaye ya ɗaga kiran ya kara a kunnensa tare yin sallama.
Cikin kaushin murya ba tare da ta amsa masa sallamar ba ta ce. "Sannu Faruq." Cikin ladabi ya ce. "Me ya faru Mom?" Dan jin yanda ta yi magana ya san ba ba ƙalau ba. Cikin tsantsar ɓacin rai ta ce. "Ban sani ba, na kuma gode da abun da ka yi, ka kyauta mun ka kyautawa kanka, amma ba lefinka ba ne, laifin mai ɗaure maka k'ugu kake abun da ka ga dama ne. To bari ka ji, wannan karon komai zai faru sai dai ya faru, ka shirya gobe da safe za'a zo a ɗauke ka, ka gama zaman nan ƙauyen nan, kai da garin kuma har abada ." Cikin damuwa Umar ya ce. "Mom Please listen to me, na faɗa miki fa shukar da muka yi ce aka samu matsala amma...." A fusace ta ce. "Shukar Ubanka? ka tsaya dai kana shuka abun da ka san baza ka taɓa girba ba, ka je ka tare a jikin matar da ba'a san asalinsu ba kana kashe musu uban kuɗi ko? to tatsar ta isa haka, ta samu iya rabonta, kai kuma zaka zo ka same ni ne har inda nake, wallahi sai na nuna maka ɓacin raina irin wanda ba ka taɓa gani ba." Dafe kai Umar ya yi ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Mom wa ya faɗa miki wannan maganar?" Mom ta ce. "Ban sani ba, ashe shi yasa sai inji mahaifinka yana ta cewa ya tura maka kuɗi, in rasa uban me kake yi da kuɗin ashe ga inda suke tafiya, Khausar ma kullum cikin yi mun complain ɗin irin wulaqancin da kake yi mata take, ashe shi ma da dalili." Sosai hankalin Umar ya tashi da jin Mom ta samu labarin yana tarayya da su A'isha, domin bai san hukuncin da za ta ɗauka akan hakan ba. K'wafa Mom ta yi ta ce. "Wallahi, wallahi, wallahi Faruq na yi rantsuwa sau uku idan ba ka baro garin nan a gobe ba sai dai ka nemi wata Uwar ba ni ba, kuma ko da wasa bayan ka dawo ka cigaba da mu'amala da faƙiran mutanen nan ban yafe maka ba." Tana gama faɗin haka ta katse wayar. Sunan Allah kawai Umar yake maimaitawa a fili cikin tsantsar damuwa. A rud'e A'isha ta ce masa. "Yaya Umar me ya faru? Wa ya kira ka a waya? Me aka ce maka?" Duban ta Umar ya yi da idanunsa da suka fara sauya kala saboda jin kalaman Mahaifiyarsa masu tsauri a gare sa, cikin sanyin murya mai cike da damuwa ya ce. "Babu komai Humairah, zan je gida in dawo, tashi mu je in raka ki ɗaki, idan Mama ta tashi ki ce mata na wuce." Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ko mutuwa aka yi muku?" Girgiza kai kawai ya yi dan ko magana ba ya son yi, kama hannunta ya yi ya kai ta ƙofar ɗakin, sai ta kasa shiga ta tsaya kawai cikin yanayin damuwa. Shi ma kasa tafiyar ya yi ya tsaya yana kallon ta, yana jin kamar ba zai iya rayuwa ba idan babu ita. A hankali ya juya ya fice daga cikin gidan, dan kallon ta ma ba ƙaramin ƙara karyar masa da zuciya yake ba. Jin ya fice A'isha ta ja ƙafarta daƙyar wadda ta ji ta yi mata nauyi ba tare da san dalili ba ta shige ɗakin, wasu hawaye masu ɗumi suka kwaranyo daga cikin idonta ba tare da ta shirya musu ba.