Sashe 36
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai maganar A'isha ba ta tabbata ba, don kullum sai Yawale ya zo kiran A'isha akan ta fita gurin tsoho makaho, Inna kuma ta murje idonta ta ce bai isa ba, ba za ta je ba. Tun mutanen gidan ba sa fuskantar abin da yake Faruwa har suka fara fuskanta, nan fa suka yi caa a kan Inna, suna cewa don ma sun samu Tsohon ya taimake su ya ce zai auri ƴar tata take ƙi? Har da masu cewa ba ƙaramin jihadi Tsoho makahon ya yi ba da ya ce zai auri A'isha. Ba ta kula su, ta dage da kaiwa Ubangiji kukanta, don zuciyarta cike take da fargaba da tsoro, sanin halin Yawale ta san dagaske yake zai aura wa A'ishaTsoho makaho, a haka har kwanaki goma suka shuɗe.
Da yamma Inna ta É—auko A'isha daga makaranta, suna tafiya tana ba wa Inna labarin wani sabon Malami da aka kawo musu daga Kano.
"Yawwa ga su nan ma sun dawo."
Muryar Yawale ta doki dodon kunnansu da faÉ—in haka lokacin da suka shiga zauren gidansu. Su tsoro ma ya ba su, saboda yadda ya yi maganar a hanzarce.
"Sannun ku da zuwa, ina A'ishushuwan tawa?"
Tsoho makaho dake zaune a kan tabarma ya faÉ—i haka yana shafa tumbinsa.
Tsaki Inna ta ja cikin takaici ta kama hannun A'isha suka yi gaba.
"A'a, Asabe ya za ki ja ta ku tafi kuma? Kin san daɗewar da muka yi muna jiran ku kuwa? Ki zo magana Malam Tsoho ya zo mu yi fa." Ko waigowa Inna ba ta yi ba balle ya saka ran za ta tsaya. Giwa a saɓule ya ce. "Ka yi haƙuri Malam, haka nake ta fama da su, daga uwar har ƴar taurin kai gare su, amma bari na je na saka su fito." Murmushi tsoho makaho ya yi, cikin washe dafaffun haƙoransa ya ce. "Babu komai ka ƙyale su, rashin fahimta ne, da zarar mun fahimci juna komai zai wuce, wuyarta a ɗaura mana Auren a kawo ta gidana." Ya ƙarashe maganar yana lalubar sandarsa. Bayan ya miƙe ya zira hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙa wa Yawale, hannu na rawa ya karɓa tare da washe baki ya ce. "Malam ba ka gajiya da abin arziƙi, Allah ya saka da Alkhairi ya ji ƙan mahaifa."
"Amin, babu komai, ai ni ka gama yi mini komai tunda ka ba ni Auren yarinyar nan, don yadda na ji ana faÉ—ar kyawun surarta na san zan mori kuÉ—ina."
Cikin dariya Yawale ya ce. "Za kuwa ka mora, don yarinyar a dire take dumurmur, sai dai an kai mata ita za ka tabbatar da abin da nake faÉ—a." Murmurshi Tsoho ya yi ya ce. "Madalla, haka ake so, yanzu bari na wuce gida, anjima su Nalami za su kawo kayan lefen, su kuma masu jere za su iya zuwa gobe, an gama gyara gurin amaryar."
"Toh Allah ya kai mu, bari na kira maka Mamman ɗin ko?" Yawale ya faɗa tare da fita ƙofar gida, inda ɗan jagoran Tsoho yake zaune yake jiran shi.
Tunda suka shiga gida A'isha take kuka, cikin kwanakin nan ta mayar da shi sana'arta, gabaɗaya ta lalace ta yi baƙi saboda damuwa da saka a ranta, a kodayaushe cikin rarrashin ta Inna take da nuna mata wannan Auren ba mai yiyu ba ne, amma ta kasa yarda da hakan, saboda ta san in dai suna cikin gidan nan to babu abin da zai hana Yawale aiwatar da abin da ya yi niyya, dama da Sarki yana nan ne zai iya tsawatar masa, shi kaɗai ne suke da tabbacin zai hana shi kaf cikin garin ya hanu.
Da daddare kamar yadda Tsoho makaho ya faɗa sai ga kaya an kawo a cikin leda Viva, atamfa Leda guda biyu da shadda wanke kuɗinka guda ɗaya, pant da shimi bibbiyu, da takalmi soso guda ɗaya, sai ƙullin su powder da man shafawa a wata baƙar leda daban. Yadda aka zube kayan a tsakar gida matan gida na gani haka Inna ta tashi ta bar su a gurin cikin tsananin baƙin ciki, ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba da ganin kayan, don hakan ya tabbatar mata dagaske fa Yawale yake aurar da A'isha zai yi. A'isha kuwa tsabar kuka har shiɗewa ta dinga yi, yadda suka ga rana haka suka dare, don jikinta rikicewa ya yi da zazzaɓi mai zafi gami da ciwon kai.
Washegari ta tashi jikin nata ya tsananta, hakan ya Æ™ara tayar da hankalin Inna, ga ba ta da kuÉ—in siyo mata magani, abun ya taru ya yi mata yawa, so take ta samu space É—in da za ta yi tunanin mafita akan ganin auren nan bai yiyu ba, amma yanayin jikin A'isha ya sa ba ta da nutsuwar hakan.......âœï¸
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2ï¸âƒ£0ï¸âƒ£*
_*Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Allah ya yiwa mahaifiyar ɗaya daga cikin member ta ƙungiyarmu Elegant rasuwa, MOMMYN MUS'AB, muna barar addu'ar ku a gare ta.*_
Haka suka yini ranar, ko ruwa A'isha ba ta kai bakinta ba, ita kanta Inna dauriya kawai take, amma jikin nata kamar mai cuta haka take jin shi. Da ruwa bokiti É—ayan da ta dauko ta tsakura ta dinga shafa wa A'isha a jikinta da tsumma, hakan ya rage zafin jikin nata, har ta samu bacci ya É—auke ta. Sharar da ba ta samu nutsuwar yi tun safe ba ta shiga yi, duk da a galabaice take saboda yunwa dake É—awainiya da ita. Tana farawa Hansai da sauran matan gidan suka yi sallama, ba yabo ba fallasa ta amsa musu. Cikin izgili Ramatu ta ce. "Asabe tun jiya muke jiran mu ga an shigo kayan gado don mu je mu yi jere amma shiru, shi ne muka ce bari mu zo mu ji ko kafinta ne ya yi tsiyar, idan ba zai samu yau ba mu bari sai gobe."
"Gaskiya kam, mu bari kawai sai goben, don tunda yarinyar ƴar gata ce ita ɗaya jal mun san ba ƙaramin kaya za a narka a ɗakinta ba, yanzu kuma yamma ta yi muna farawa dare zai yi."
Cewar Hansai tana wani murmushi.
Sarai Inna ta gane Habaici suke mata, murmushi ta yi ta ce. "To na gode da kulawa." Kallon juna suka shiga yi, cikin mamaki uwargidan Yawale ta ce. "To ai ba ki ce mana komai ba game da maganar kayan jeren, mu jira yau É—in ko mu bari sai gobe."
"Allah ya kai mu lafiya."
Inna ta faɗa a taƙaice, cikin ƙoƙarin danne damuwar dake cikin ranta. Duk yadda suka so su ji Inna ta ce wani abu akan maganar jeren na za a yi ko ba za a yi ba amma ta ƙi ba su tabbaci. Haka suka tattara ƙafafuwansu suka koma, zuciyoyinsu cike da gulma da farincikin ganin su A'isha a cikin baƙin ciki. Fitar su babu jimawa wata yarinya ƴar ajinsu A'isha ta zo gidan sanye da uniform. Bayan sun gaisa Inna ta ce. "Atika lafiya dai ko?"
"Lafiya ƙalau, wani malaminmu ne ya ce na rako shi gurin A'isha, tare muke ma yana ƙofar gida."
"To, wani abu ya faru ne? Ko laifi ta masa?"
"Gaskiya dai ban sani ba."
"To bari na É—auko hijabina mu je."
Yana tsaye jingine da bangon gidan yana kallon cikin soro suka fito, cikin girmamawa ya tsugunna har ƙasa ya gaishe da Inna. Da fara'a ta amsa masa duk da cikin ranta cike take da fargabar Allah ya sa ba wani abun A'isha ta yi ba. Shiru ta yi cikin sauraren abin da ya zo da shi. Cikin nutsuwa ya fara magana. "Na ga A'isha ba ta zo school ba yau, shi ne na ce bari na zo na ji ko lafiya?" Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Ba ta jin daɗi ne, yau ta tashi da zazzaɓi." Cikin damuwa ya ce. "Allah Sarki, Allah ya ba ta lafiya, zazzaɓin bai yi zafi ba dai sosai ko?" Inna ta ce. "Sai godiyar Allah dai jikin nata."
"Subhanallahi, Allah ya ba ta lafiya, amma kun je asibiti ko?"
"Za mu dai je insha Allahu."
Gyaɗa kai ya yi tare da yin shiru na wasu sakanni sannan ya ce. "Mama don Allah da gaske ne aurar da A'isha za ku yi?" Cikin raunin murya Inna ta ce. "Eh." Cikin damuwa sosai ya ce. "Amma saboda me? Na ga yarinya ce ƙarama, kuma tana da ƙoƙari a makaranta, da kun bar ta ko secondary school ta gama, kuma na ga ita ma kamar ba ta son auren, saboda jiya an fita break na gan ta ita kaɗai a class tana ta kuka, da na tambaye ta me ya faru shi ne take sanar mini an ce aure za a mata, ita kuma ba ta so." A sanyaye Inna ta ce. "Ni ma ba na so, an fi ƙarfi na ne kawai."
"Kamarya? Su waye suke son aurar da ita É—in to?"
Ya tambaya a hanzarce.
"Kawunnanta ne."
"Ba ma mahaifinta ba?"
"Eh, shi Allah ya masa rasuwa."
Jinjina kai ya yi bai ce komai ba ya zaro kuÉ—i ya ajiye a gaban Inna ya yi mata Sallama ya tafi, Inna tana kiran shi akan ya zo ya É—auki kuÉ—in amma bai tsaya ba. Da kallo ta bi shi tare da yi masa addu'a a cikin zuciyarta, ko tantanma ba ta yi shi ne sabon malamin da A'isha take labarin an kawo musu. ÆŠaukar kuÉ—in ta yi ta koma gida. Bayan A'isha ta tashi Inna take labarta mata zuwan malamin. Murmushi ta yi cikin muryar marasa lafiya ta ce. "Shi ne wanda nake ba ki labari, sunansa Malam Faisal, yana da kirki sosai da tausayi." Inna ta ce. "Allah Sarki, Allah ya saka masa da Alkhairi, dubu biyar fa ya ba ni, dama ina ta tunanin abin da zamu ci da wanda zan kai ki asibiti gobe."
Bayan kwana uku A'isha ta ji sauƙi sosai, ta sha allurai da magunguna. A kwana ukun kullum Malam Faisal sai ya zo ya duba ta tare da yi musu Alkhairi, hakan ya janyo tarzoma tsakanin Inna da Yawale. Ya dinga masifa da faɗin kar ya ƙara ganin Faisal ya zo, tunda dai yarinya yanzu ɗaya take da matar aure don ya karɓi sadakinta, rana kawai suke jira a ɗaura Auren.