← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 55

Sashe 39

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ban sani ba ni ma, amma mu fita daga cikin tashar nan, kamar yadda direban ya ce anjima mu samu wata wayar mu ƙara kira ko za a yi sa'a ta kunna wayar. Yanzu kasuwar da ake siyar da wayoyi kawai zan ce ɗan sahu ya kai mu, tunda da kuɗaɗe a jikina gara na siyi ƙaramar waya kawai, kar na rasa mai ba ni aron ta kiran."
Cikin gamsuwa A'isha ta ce. "Ya fi kam." Wani mutumi Inna ta tambaya inda za su bi su samu motar zuwa kasuwar sayar da waya ya ce musu su tsallaka titi za su samu. Godiya ta masa tare da ƙara damƙe hannun A'isha ganin titin babba ne, sun hau kan titin kenan aka ba wa b'arin da suke hannu, kasancewar ba ta saba da ganin motoci na gudu akan titi haka ba duk sai ta ruɗe, ta rasa gaba za ta yi ko baya, sai ta tsaya cak ta kasa ɗaga ƙafafunta, ga horn ɗin da ake musu duk ya ƙara ruɗar da ita.

Duk yadda ya so ya taka burki kafin ya ƙarasa inda suke amma abun ya ci tura, saboda tazarar dake tsakaninsu babu yawa. Jin sun tsaya A'isha ta buɗe baki za ta yi magana amma bugar ta da Motar ta yi tare da cilli da ita gefe ya hana ta maganar. Cikin matuƙar tashin hankali dattijon ya taka burki tare da buɗe Mota ya fito a ruɗe yana kiran "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Duk wani mai abun hawa dake gurin tsayawa ya yi tare da fitowa hankali a tashe, Inna dake kwance ba ta motsi saboda taka gefen kanta ta tayar Motar ta yi aka fara janyewa, ganin jinin dake zuba ya ƙara tayar da hankalin wanda ya buge su. Ba tare da ɓata lokaci ba aka zuba su a cikin Motar mutumin, wani ɗan karota ya shiga front seat, suka tafi zuwa asibiti police da aka kira su a lokacin na biye a bayan su.

Wani babban Private Hospital dake kusa suka je, cikin gaggawa aka karɓi su A'isha aka yi emergency room da su. Ƙarshen tashin hankali mutumin nan ya shiga, don gani yake kamar gazawar shi ce accident ɗin da ya faru, ya kasa zaune ya ƙasa tsaye sai kaiwa da komowa yake cikin ransa yana kiran sunan Allah, tare da addu'ar Ubangiji ya tashi ƙafaɗun su.

Bayan wani lokaci wani likita ya fito daga ɗakin da su Inna suke, da sauri mutumin ya nufe shi tare da faɗin. "Doctor yaya? Suna raye dai dukan su ko?" Daga yanayin fuskar Likitan ya san da matsala, hakan ya ƙara tsananta bugun zuciyarsa. Cikin son kwantar masa da hankali likitan ya ce. "Yarinyar babu abin da ya same ta, buguwa kawai kanta ya yi, mun yi mata duk abin da ya dace, yanzu ta samu bacci sakamakon allurar da muka mata." Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin. "Alhamdulillah, ita kuma matar fa?" Cikin damuwa Doctor ya ce. "Sai haƙuri Alhaji, ita Ubangiji ya karɓi abarsa.".........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖

_*Zeey Kumurya*_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*2️⃣2️⃣*

Tamkar saukar aradu a ka haka kalaman likitan suka daki zuciyarsa, yadda ya ƙura wa likitan ido za ka yi zaton suman tsaye ya yi, bakinsa dake rawa alamar yana son ya yi magana amma ta ƙi fita shi zai ba ka tabbacin bai suman ba. Ganin halin da yake ciki Likitan ya kama shi ya zaunar da shi a ɗaya daga cikin kujerun dake reception ɗin.

"Take it easy Alhaji, komai muƙaddari ne daga Ubangiji."
Likitan ya faÉ—a cikin rarrashi.
Numfashi ya sauke cikin sanyin murya kamar wanda ya ci kuka ya ƙoshi ya ce. "Doctor, please ku ƙara duba ta, wataƙila dogon suma ta yi za ta farfaɗo." Girgiza kai likitan ya yi ya ce. "Ba a mutuwa a dawo ai, sai da muka tabbatar ta mutu sannan muka fito don mu sanar maka, ka yi haƙuri tare da yi mata addu'ar ganawa da Ubangijinta lafiya, Allah ya sa mu dace." Ya ƙarashe maganar tare da barin wajen. A raunane ya ce. "Allah ya ji ƙan ki, ya gafarta miki." Ya daɗe yana juya abun a cikin ransa, tamkar mafarki haka yake kallon al'amarin, bai taɓa tunanin cikin ƙaddarorin rayuwarsa akwai sanadin ran wani ba. Cikin mutuwar jiki tamkar wanda aka yiwa mugun duka ya lalubo tsadaddiyar wayarsa ya latsa tare da karawa a kunne.

Kyakkyawar farar mace ce doguwa ƴar dumaduma zaune a wani rantsatstsen parlour tana kallon SUNNA TV, kyawawan idanunta sanye cikin farin glass ɗin da ya ƙara haska ƙawatuwar fuskarta. Wayarta dake gefenta ce ta fara vibration, a hankali ta kai hannunta da ya sha jan lalle ta ɗauki wayar. Ganin sunan mai gidanta na yawo a kan screen ɗin wayar ya sa mamaki bayyana a kan fuskarta, saboda sanin da ta yi idan ya fita ba ya amsa kira ko shi ya yi kiran a irin wannan lokacin, sai da wani babban dalilin. Numfashi ta sauke tare da ɗaga kiran ganin yana ƙoƙarin katsewa ta kara a kunne tare da yin sallama cikin kamilalliyar murya mai tattare da nutsuwa.

"DR."
Ya ambata cikin matuƙar raunin murya.
Gabanta ne ya yanke ya faɗi, don daga jin muryarsa kamar ta wanda ya tashi daga bacci ko ya ci kuka ya ƙoshi ta san ba ƙalau.
"Na'am Nurul ƙarbi, lafiya na ji muryar haka?" Ta tambaya a hanzarce. Numfashi ya sauke ya ce.
"Babu lafiya Dr, ina asibiti yanzu haka. A ruÉ—e ta ce. "Subhanallahi, mai ya faru?"
"Ki zo kawai, maganar ba za ta yiyu a waya ba."
Ƙara shiga cikin rikici ta yi, cikin ƙarfin hali ta ce. "Okay gani nan zuwa yanzu, wanne asibitin ne?"
FaÉ—a mata ya yi sannan ya katse kiran.

Mintuna ƙalilan suka ƙarasa asibitin saboda gudun da ta ce driver ya yi. Cikin sassarfa ta ƙarasa emergency ward ɗin. Hango mai gidan nata zaune cikin ƙoshin lafiya ya sa ta sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi. Kasancewar kansa yana ƙasa ya sunkuya ya sa bai san da isowar ta ba, sai da ta zauna a kusa da shi sassanyan ƙamshinta ya bugi hancinsa sannan ya ankare ya ɗago kansa. Ganin yanayin mijin nata ya sa damuwar ta ƙaruwa. Hannunsa ta kama a raunane ta ce. "Me yake faruwa Abbansu? Ka saka ni a zullumi da faɗuwar gaba, duk da na gan ka lafiya ƙalau amma zuciyata ba ta daina bugawa ba."

"Accident muka samu, na kaÉ—e wasu mata har É—aya daga cikinsu ta rasu.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'jiun, garin yaya haka ta faru Abbansu?"
Tsautsayi ne kawai Dr." Ya ba ta amsa cikin karaya. Dafe kanta ta yi cikin tsantsar tashin hankali, lokaci ɗaya ƙwalla ta ciko a cikin idanunta. A sanyaye ta ce. "Yanzu mene abin yi? Ina gawar da ɗayar marar lafiyar?"
"Duk suna ciki, da jira nake yarinyar ta farfaɗo sai a tambaye ta daga inda suke a kai gawar can, na kira Khalifa da Alhaji Abubakar duk na sanar musu, na san yanzu haka suna hanya insha Allahu." Gyaɗa kai ta yi ta ce. "Amma mu fara karɓar gawar mu kai can gida, idan muka jira sai yarinyar ta farfaɗo za a ɗauki time, tunda ba mu san tsawon lokacin da za ta ɗauka ba."
"Haka za a yi."
Cikin sauke numfashi mai tattare da damuwa ta ce. "Mu je mu ga yanayin jikin yarinyar." Bai ce komai ba ya miƙe ya nufi ɗakin da ya ga an shiga da A'isha.

A kwance suka tarar da ita an saka mata drip a hannunta. Cikin tsananin tausayawa Dr ta ƙarasa ta shafa fuskarta tare da yi mata addu'ar samun lafiya.
"Ko ya yarinyar nan za ta ji idan ta samu labarin mutuwar matar can? Wataƙila ma mahaifiyarta ce."
Abba ya faɗa a raunane. Kallon shi Ummi ta yi ta ce. "Haƙuri za ta yi, haka Ubangiji ya ƙaddaro." Girgiza kai Abba ya yi ya ce. "Haka ne, Allah ya sa mu dace."
"Amin, mu ƙarasa mu ga gawar matar mu yi wa likitocin maganar tafiya da ita."
Gyaɗa kai Abba ya yi ya ce. "Ya kamata a samu mai zama tare da yarinyar, bai dace mu bar ta ita kaɗai ba, matsalar babu komai a tare da su wanda za mu samu information na inda suke ko numbern wani nasu, don ko waya ba a gani ba a tare da su." Numfashi Ummi ta sauke ta ce. "Zan zauna da ita, har zuwa lokacin da za ta samu lafiya." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Na gode sosai DR da wannan karamcin naki, Allah ya saka da Alkhairi." Tana miƙewa ta ce. "Babu godiya tsakani na da kai Mijina, ko da wanda ban sani ba ne zan iya yin jinyar shi idan ba shi da me yi masa, balle wannan da alhakin hakan yake kanmu, duk abin da ya shafe ka ai ya shafe mu." Cikin jin daɗi ya ce. "Ubangiji ya yi miki albarka, ya biya ki da gidan aljanna." Idanunta a kan A'isha ta amsa da "Amin."
Cikin awa É—aya aka ba su gawar Inna da kanta ke ta zubar da jini, har lokacin A'isha ba ta farka ba.
Chapter 39 · 0% Book details