← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 55

Sashe 29

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daƙyar Umar ya iya kai kansa gidan Sarki saboda sarawar da kansa yake masa, yana zuwa ya buɗe ɗakin da yake ya faɗa kan katifa ya kwanta ruf da ciki. Wani irin zafi zuciyarsa take masa, bai shirya barin A'isha yanzu ba, be shirya yin nesa da ita ba, be shirya tafiya ya bar su a cikin wannan garin da ba'a k'aunar su ba, be shirya tafiya ya bar ta a cikin makanta ba, ya gama tsarawa a cikin watan nan zai ɗauke ta ya kai ta gidan k'anwar mahaifinsa ita da Inna su zauna kafin a gama zirga-zirgar zuwa asibiti ganin likita, dan ya san ita kaɗai ce zata yi masa wannan taimakon cikin ruwan sanyi. Amma Mom ta wargatsa komai, domin ba shi da zaɓi face ya bi umarninta ya koma gida a gobe. Wunin yau gaba-d'aya cikin damuwa ya yi shi, gaba-d'aya jinsa yake wani iri kamar mai cuta, Sallah ce kawai take fitar da shi waje. A ɓangaren A'isha ma haka ne, dan ita kuka ta sakawa Inna na babu gaira babu dalili, rarrashin duniya Inna ta yi mata amma ta ƙi yin shiru, ta kuma ƙi cin abinci, gashi ta ƙi faɗa mata abun da yake damun ta. Abun da ya ƙara tayarwa da A'isha hankali ganin yamma ta yi lokacin zuwan Umar ya yi amma bai zo ba, Inna ma ta yi mamakin hakan, amma sai ta ɗauka wani uzurin ne ya tare shi. Daren yau Umar bai rintsa ba, kwana ya yi yana tunanin mafita, bai taɓa tunanin ƙaddara makamanciyar wannan za ta riske shi ba a cikin rayuwarsa, abun da yake ƙara tayar masa hankali furucin Mom na ƙarshe, da ta ce ko bayan ya koma gida ya cigaba da mu'amala da su A'isha ba ta yafe masa ba. Tambayar kansa ya dinga yi wa ya faɗawa Mom wannan zancen? Shi dai ya san ba ta mu'amala da kowa a garin nan, kuma mahaifinsa ma haka balle ya ce ko shi ya samu labarin ya faɗa mata, ya san Sarki kuma ba zai taɓa faɗa masa ba. Koma waye bai yi masa adalci ba, domin kuwa ya saka ana ƙoƙarin yi masa katangar ƙarfe da farinciki a cikin rayuwarsa, dan matuƙar ya rabu da A'isha to tabbas ya san tausayin ta da k'aunar ta dake cike fal a cikin zuciyarsa ba zai bar shi ya cigaba da jin daɗi da walwala kamar kowa ba a cikin rayuwarsa, matuƙar ba cigaba da kasancewa da ita ya yi ba har ƙarshen rayuwarsa..........✍️

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*1️⃣5️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_

..........Washegari daƙyar Umar ya iya fita Masallaci da asuba, saboda wani irin sanyi da yake ji yana ratsa ƙasusuwan jikinsa, ga wata irin kasala da ta lullub'e shi. Bayan ya dawo ya shiga haɗa kayansa cikin ƙarfin hali, ganin abun yake tamkar a mafarki wai yau zai tafi ya bar A'isha. Bayan ya gama haɗa komai nasa ya yi wanka ya shirya cikin manyan kaya. Ƙarfe Bakwai da mintuna Mom ta kira sa, jiki a sanyaye ya ɗaga kiran. Ba tare da ta bi ta kan gaishe tan da yake yi ba ta ce. "Ina fatan ka gama shiryawa? Dan tun asuba driver ya taho ɗaukar ka." Cikin sanyin murya mai cike da damuwa ya ce. "Na gama." Mom ta ce. "Better, ka san kuma me zaka faɗawa Mahaifinka idan ya ga ka dawo dan ban sanar masa zaka dawo yau ba." Umar ya ce. "Zan kira shi yanzu in faɗa masa, ba zai ji daɗi ba idan ya ga kawai na dawo kuma ban sanar masa ba." Mom ta ce. "Kai ka sani kuma, saura ka yi kuskuren ambatar sunana a cikin zancen dawowar taka." Umar ya ce. "Na san me zan ce masa." Taɓe baki Mom ta yi ta kashe wayarta. Numfashi Umar ya ja ya fesar, Numbern Abbansa ya kira ya sanar masa zai dawo gida yau. Cikin mamaki Abba ya ce. "Yau yau ɗin nan kuma Faruƙ?" Umar ya ce. "Eh." Abba ya ce. "Wanne irin abu ne haka kamar yaƙi? Tafiya lokaci ɗaya, kuma sai a yau ɗin zaka sanar mun?" Umar ya ce. "Tun jiya nake ta ƙoƙarin kiran ka ya ƙi lafiya babu network, sai text na yiwa Mom na faɗa mata, ina jin mantawa ta yi ba ta sanar maka ba." Abba ya ce. "To ai shikenan, Allah ya kawo ka lafiya, bari na sanarwa Ado driver ya zo ya ɗauko ka." Umar ya ce. "Ai Mom ta faɗa masa ma har ya taho." Abba ya ce. "Alright, Allah ya kawo ku lafiya, amma Are You ok Faruƙ?" Umar ya ce. "Lafiya ƙalau Abba, me ka ji?" Abba ya ce. "Muryarka na ji kamar ta wanda ba shi da lafiya, ko wani abun ne ya faru?" Umar ya ce. "Babu komai Abba, yanzu na tashi daga bacci ne." Abba ya ce. "Okay, to Sai kun ƙaraso, Allah ya tsare hanya, kar ka manta da addu'a." Umar ya ce. "Insha Allah Abba, na gode." Daga haka suka yi sallama ya katse wayar. Miƙewa ya yi yana jin yanda kansa da ƙirjinsa suka yi masa nauyi saboda damuwa ya fice daga ɗakin ya nufi cikin gidan Sarki.

Da mamaki Sarki yake duban Umar bayan ya faɗa masa yau zai tafi, yana jinjina kai ya ce. "Ikon Allah, kuma Umar sai yau ɗin da zaka tafin zaka sanar mun?" Ɗan murmushi ya yi bai ce komai ba. "Sarki ya ce lafiya dai ko wannan tafiya haka kamar wahayi?" Umar ya ce. "Lafiya ƙalau, dama ka san already na gama abun da ya kawo ni garin nan, zama na yi kawai saboda ban gaji da garin ba." Cikin murmushi Sarki ya ce. "Yanzu kuma ka gaji kenan?" Umar ya ce. "A'a, na kusa komawa karatu ne, to ina son zan ɗan yi wasu shirye_shirye kafin na tafi." Sarki ya ce. "To ai shikenan, Allah ya taimaka, amma za mu yi kewar ka sosai." Murmusawa kawai ya yi bai ce komai ba. Sarki ya ce. "Bari na saka a haɗa maka tsaraba, duk da ma dai a ƙurarren lokacin ka faɗi tafiyar, da ko tun jiya ne ka sanar mun ai da an san abun yi." Umar ya ce. "An goge Allah ya saka da Alkhairi, bari na shiga ciki na yi musu sallama." Sarki ya ce. "To sai ka fito." Yana fita suka ci karo da Ɗan_juma ya fito daga cikin gida, wani irin kallon banza Ɗan'juma ya dinga bin sa da shi, shi kuwa tun kallon farko da ya yi masa bai ƙara kallon inda yake ba ya shige ciki.
Chapter 29 · 0% Book details