Sashe 35
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin karkaÉ—a Æ™afa da muzurai Yawale ya ce. "Abin da ya sa na aika a kira ku ba komai ba ne sai don na sanar da ku cewa na karÉ“i kuÉ—in baikon A'isha daga hannun Tsoho Makawo É—azu da yamma, mun kuma tsayar da ranar É—aurin Aure ni da shi sati biyu masu zuwa, ranar juma'a bayan an sakko daga masallaci za a É—aura auren, don haka sai ku fara shiri." Ya yi maganar cikin sigar bayar da umarni.........âœï¸
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*1ï¸âƒ£9ï¸âƒ£*
Cikin rashin fahimta Inna ta ɗago kai ta dube shi ta ce. "Ban gane ba Yaya? Wacce A'ishan kake nufin ka karɓi kuɗin Auren ta?"
"A'isha nawa muke da su a gidan nan da kike da iko da su wanda zan saka a kira ki don na sanar miki batun auren su? Wannan dai makauniyar dake gabanki ita nake nufi."
"TabÉ—ijan! Tatsuniya ma kenan, to wallahi ba zan aurar da Æ´ata ba a yanzu, kuma babu wanda ya isa...."
"Ke Asabe saurara!"
Iya ta katse ta cikin tsawa sannan ta cigaba da magana. "Don ma kin samu Tsoho makahon ya taimake ku ya ce zai aure ta shi ne za ki yi wa mutane iskanci? Ƴar taki Shegiya mara asali za ki yi wa mutane firfita a kan ta? To wallahi wannan auren tamkar an yi an gama."
Cikin bushewar zuci da tsantsar ɓacin rai Inna ta ce. "Ni kuma babu wanda ya isa ya aurar mini da ƴa ko wanene." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannun A'isha suka miƙe, wadda kukan da take na marin da Iya ta yi mata ya sa ba ta fahimtar abun da suke cewa. Wata dariya Yawale ya yi ya ce. "Me za ki iya in an aurar miki da ƴar? Wa kike da shi? Ƙarƙari ki ce za ki kai ƙara gurin Sarki ko? To Sarkin baya nan ya tafi umra, sai mu ga wa zai tsaya miki."
"Allah, shi ne zai mini katangar ƙarfe da duk wani mummunan ƙudirin ku a kan mu."
Inna ta faɗa a fusace, yau kam sun kai ta bango, duk haƙuri da kawaicin da take musu a yanzu ta ji ba za ta iya ba.
"Ni kuma in dai sunana Yawale sai an yi auren A'isha makauniya da Tsoho makaho."
Sai a yanzu A'isha ta fahimci abin da ake magana akai, da wannan kalaman na Yawale. Wata irin bugawa zuciyarta ta yi, ƙara volume ɗin kukanta ta yi cikin rawar murya ta ce. "Inna me na ji Baba Yawale yana cewa? Ni za a yiwa Aure?" Hawayen fuskarta Inna ta fara share mata tare da faɗin. "Ki kwantar da hankali, in dai ina raye babu wanda ya isa ya miki Auran dole, tunda babu wanda ya haifar mini ke." Ba ta jira sauraren tijarar Iya da Matan Yawale suke taya ta ba, ta ja A'isha suka fice daga ɓangaren.
"Inna don Allah mu bar garin nan, mu bar musu gidansu, kin san tunda Baba Yawale ya dawo rashin mutuncin da ake mana sai ya ƙaru."
A'isha ta faÉ—i haka cikin kuka.
Girgiza kai Inna ta yi cikin ɗacin rai ta ce. "Na fi ki gajiya da zaman gidan nan A'isha, dan dai babu yadda zan yi ne, kuma ina tunanin idan mun bar nan ba mu san ina za mu ba, ba mu san da waɗanda Allah zai ƙara haɗa mu ba."
"Ƴan'uwanmu mana, ko da gaske ba mu da su?"
"Muna da su, amma wani babban dalili ya sa ba zan koma gare su ba."
"Wanne dalili ne? Don Allah Inna ko sau ɗaya ne ki kai ni na gan su, tun ina ƴar ƙarama ake mini gorin rashin asali, tun bana damuwa har na fara damuwa duk da ban san me hakan yake nufi ba, yanzu na gane me ake nufi da rashin asali, na fuskanci me kalmar SHEGIYA take nufi, kamar yadda na gano ba Baba Malam ne ya haife ni ba."
Cikin tsantsar mamaki da damuwa Inna take kallon A'isha, a shekarunta ba ta yi tunanin za ta iya gane waɗan nan abubuwan ba a yanzu, musamman da har yanzu ɗabi'un yara sun fi yawa a tattare da ita a kan na manya, cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Wa ya faɗa miki ba Malam ne ya haife ki ba? Na ce ki daina mini wannan zancen ko, don ba gaskiya ba ne, Malam shi ne mahaifinki." Cikin matsanancin kuka ta ce. "Ki daina ɓoye mini Inna, na riga na gane gaskiya, amma don Allah ko ba za ki kai ni na ga ƴan'uwanmu ba ki taimaka ki ba ni labarin su, da dalilin baro su da kika yi."
"Zan faɗa miki, amma ba yanzu ba, domin har yanzu ke yarinya ce, ƙwaƙwalwar ki ba za ta ɗauki labarin ba balle har ta ba ki damar fuskantar shi, amma da sharaɗin ba za ki kuma tambaya ta ba har sai lokacin da na ga ya dace na faɗa miki da kaina."
GyaÉ—a mata kai kawai ta yi tare da kifa kanta a kan cinyarta ta cigaba da kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar duk mai sauraren shi.
Washegari da ciwon kai ta tashi, hakan ya sa Inna ta ce ta zauna kar ta je makaranta, ranar Monday idan ta kai ta sai ta sanar da Malaman ba ta da lafiya ne ya sa ba ta zo ba. Da Yamma Inna tana ramuwar baccin da ba ta yi ba daren jiya ta ji muryar Namiji yana magana a kanta.
A firgice ta tashi tare da rarumar hijabinta dake kusa da ita ta saka, Yawale ta gani ya ƙura mata ido yana bin ta da wani irin kallo. Haɗe rai ta yi cikin ɓacin rai ta ce. "Mene ne haka Yawale? Ya za ka shigo mini har ɗaki babu neman izini, a kan me?"
"Saboda gidanmu ne ina da ikon shiga duk inda na ga dama."
"Ko kai ka gina sashen nan ka ba ni haya ba ka hurumin faɗo mini har cikin ɗaki ba tare da neman izini ba, don haka kar ka ƙara yi mini irin wannan ba na so, idan kuma ba haka ba wallahi hukuma ce za ta raba mu!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Dariyar rainin hankali ya yi ya ce. "To hukumar ta raba mu mana Asabe?"
Tsaki Inna ta ja tana ƙara gyara hijabin jikinta ta ce. "Ka tashi ka fitar mini daga ɗaki Yawale." Gemunsa ya shafa cikin shigar duniyanci tare da faɗin. "Ba ke kika saka na shigo ba, don haka ba ki isa kin sa na fita ba, A'isha na zo kira dama, Tsoho makaho ne yake jiran ta a soro za su yi taɗi."
Kallon ba ka da hankali Inna ta yi masa ta ce. "Dama a kan wannan shirmen ka shigo mini har cikin É—aki ina bacci? ban da, da wata manufar a ranka da ka shigo gidan ba ka ga A'ishan kwance a tsakar gida ba? Yawale ka ji tsoron Allah, ka tuna za ka mutu fa, duk abubuwan da kake yi Ubangiji yana kallon ka."
"Har kura ce za ta ce wa kare maye? Ke har kin isa ki yi mini wa'azi Asabe? Ke da kike tattare da abin kunya, SHEGIYA fa kika ajiye, ai ke kika cancanci wa'azi ba ni ba."
Miƙewa Inna ta yi ba ta kuma magana ba, don ta fuskanci neman magana kawai yake da ita. Ficewa ta yi ta bar masa ɗakin zuciyarta na mata wani irin zafi, ta gaji da cin zarafin mutanen gidan nan, rashin dajarar ta har ya kai ƙaton mutum ya shigo mata ɗaki ba excuse tana bacci ya gama ƙare mata kallo, Gaskiya dole ta san abin yi, ba za ta ɗauki wannan akuyancin da jahilcin ba, musamman da ta daɗe da gane ƙudirin Yawale a kanta.
"Ke A'isha tashi mu je tsoho makaho yana jiran ki, ko ba kya ji ne? Ƴar bantan Uba kawai."
Yawale da ya fito daga É—aki ya faÉ—i haka cikin masifa.
Ko motsi A'isha ba ta yi ba, duk da tana jin shi sarai, Hararar shi Inna ta yi ta ce. "Babu fa inda za ta, Yawale tun wuri ina shawartarka da ka ruguje wannan maganar Auren mara ma'ana, ban da zalunci yarinyar da ko shekara goma sha biyar ba ta cika ba ita ake ƙoƙarin aurawa Tsohon da ko ni ba zan aure shi ba? Tsohon ma mara mutunci da rashin sanin darajar ɗan Adam, ya mayar da aure ba a bakin komai ba, waye bai san Auri saki yake ba kaf garin nan, wato yanzu an gane halinsa an daina ba shi Auren shi ne zai zo nan, ni kuma da ban san ciwon kaina ba sai na ɗauka na bayar, to wannan ɓatan basiran ba da ni za a yi ba."
"Duk rashin mutuncin shi amma ai yana da asali ko?"
"Wannan ku ta shafa ba ni ba."
Jinjina kai Yawale ya yi ya ce. "Kuma yarinya tunda tana zaune a cikin gidanmu tana cin arziƙin mu muna da ikon aurar da ita ga duk wanda muka so."
"Tunda wata tsiyar kuke tsinana mata ba, gata nan ga ka, ka daura mata Auran mu gani."
"To mu zuba mu gani, ni da ke ɗan halak ka fasa." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa da sashen, Inna ta raka bayansa da harara.
Cikin jin daÉ—in yadda Inna ta yi wa Yawale tatas A'isha ta ce. "Gwara da kika yi masa haka, gobe ba zai dawo ba."