← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 55

Sashe 48

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Khalifa da ya tsaya yana magana da ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ya yi saurin ƙarasowa inda suke yana faɗin. "Salma! Mene haka? Ba ki da hankali ne za ki mata irin wannan shaƙar?" Ya ƙarashe maganar cikin fusata tare da ƙoƙarin ɓanɓare hannunta daga wuyan A'isha, amma ta ƙi sakin ta sai ma ƙara cakumar ta take cikin bala'i. Marin da Khalifa ya sauke mata ne ya sa ta sakin A'isha ba shiri tare da dafe kuncinta da take jin tamkar ba ya jikinta, saboda tsabar zaraɗaɗi da zafin marin da ya ratsa ta.
"Ni ka mara Khalifa?" Ta tambaya cikin tsantsar mamaki da ɓacin rai, idanunta cike da ƙwallar takaici.
Khalifa bai kula ta ba ya riƙo A'isha dake numfarfashi gami da hawaye.
"Are You okay?" Ya tambaye ta a ruɗe ta cikin damuwar halin da take ciki. Ganin yadda take kuka ya ƙara ɗaga masa hankali. Daidai lokacin Ummi da ta fito parlour ba ta ga sun ba ta duba ko'ina duk ba ta gan su ba ta fito compound ɗin. Hango su a tsaye Khalifa na riƙe da A'isha ya sa ta ɗaga murya ta ce. "Khalifa Lafiya? Me yake faruwa?" Numfashi ya sauke mai zafi yana jifan Salma da wani mugun kallo wadda ta yi suman tsaye, a kufule ya ce. "Shaƙe ta ya yi tana ƙoƙarin kashe ta."
"Subhanallahi, shaƙa kuma kamar ya? Akan me?" Ummi ta tambaya a ɗimauce tare da ƙarasowa ta janye A'isha tana faɗin. "Me ya faru ne wai? Ina Ihsan ɗin?" A'isha za ta yi magana amma ta kasa saboda kukan da take, har yanzu jikinta bai daina rawar firgici ba, don ba ƙaramar shaƙa ta sha ba. Khalifa da yake jin tamkar ya rufe Salma da duka ya juya ya bar wajen, saboda idan ya cigaba da tsayawa yana kallon ta zai iya yi mata abin da ya fi mari.
"Wallahi sai ka yi nadamar mari na da ka yi, zan nuna maka kai ƙaramin ɗan iska ne." Salma ta faɗa a zuciye tare da wucewa ta nufi ciki a matuƙar fusace. Da kallo kawai Ummi ta bi ta ta kama hannun A'isha suka shiga ciki.

Direct part ɗinsu ta wuce a maimakon na Mommy da ta yi niyya, Upstairs ta haye ta buɗe bedroom ɗinsu ta shiga, zuciyarta har wani huci take saboda zafin da take ji a cikinta, an daɗe ba a yi mata abin da ya yi ƙoluluwar ɓata mata ran da Khalifa ya yi ba yau.
"Ni zai mara yana ƙanin mijina akan wata SHEGIYA? Wacece ita da har wani mahaluƙi zai kai hannunsa jikina saboda ita?" Ta yi maganar cikin ɗaga murya tare da cillar da wayarta kan gado ta fara kai kawo a cikin ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin tare da wanzuwar ƙamshinsa a cikinsa ya sa ta juyawa cikin sauri ta fuskanci shi. Ƙura mata ido ya yi cikin faɗuwar gaba saboda ganin yanayinta, a duniya idan akwai abin da yake gudu da tsoron faruwar shi to ɓacin ran matarsa abar ƙaunar shi ne. Cikin damuwar da ta kasa ɓuya a ransa ta bayyana a fuskarsa ya ce. "Lovely what happened to you? Wa ya taɓa mini ke?" Ya ƙarshe maganar tare da ƙoƙarin riƙe ta.
"Don't touch me!" Ta faɗa cikin tsawa. Tsayawa ya yi cak tare da runtse idonsa, don ba ƙaramin ratsa shi tsawar ta yi ba. Cikin kakkausar murya ta ce. "Ƙaninka ya mare ni saboda na mari wata aba da ba ta kai in saka ta a jerin mutane ba, ka je ka rama mini yanzu-yanzu ba sai ya lokaci ya ƙure ba, don da zafi-zafi ake dukan ƙarfe." Cikin ɓacin rai ya ce. "What? Khalifa ne ya mare ki ko wa?"
"Kana da wani ƙanin ne bayan shi?" Ta tambaye shi cikin tarar numfashi. Bai ce komai ba ya juya ya fice da sauri cikin ɓacin rai. Ajiyar zuciya ta sauke ta zauna a bakin gado, sai yanzu ta ji ta fara hucewa saboda sanin babu abin da zai hana Safwan rama marin da Khalifa ya mata, ko da kuwa a gaban Ummi da Abba ne, ko da yana sauke hannunsa daga fuskar Khalifa za su ba shi nasa marin, shi dai tunda ta ce ya je ya rama mata sai ya yi.

Ummi tana zaune a kan kujera A'isha na jikinta tana rarrashin ta bayan ta faɗa mata abin da ya faru da ƙyar cikin kuka ya shigo cikin parlour'n tamkar an cillo shi yana kiran sunan Khalifa. Ɗago kai ta yi ta kalle shi, ganin yadda yake huci ta haɗe rai ta ce. "Khalifa ba ya nan, sai ni uwarsa idan za ka rama mara marin a kaina, tunda kai ma uwarka ya mara." Kallon ta ya yi kamar zai magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice daga parlour'n. Tsaki Ummi ta yi cikin takaici, a ranta tana masa addu'ar Ubangiji ya kawo ranar da zai bar wannan rayuwar ta raƙumi da akala da Salma ke jan shi. A'isha kuwa cak ta tsayar da kukanta tare da ƙara ƙanƙame Ummi, ba ta san waye ya shigo ba, ba ta taɓa jin muryarsa ba tunda ta zo gidan, amma yadda ya shigo yana kiran sunan Khalifa cikin ƙaraji da masifa ya sa tsoron shi ya dirar mata a zuciya lokaci ɗaya.

Mommy da ta ga gilmawar su ta window ta miƙe cikin sauri ta nufi part ɗin nasu, Upstairs ta hau don ta san suna can, ganin ba sa parlour ta nufi bedroom ɗin Salma ta shiga.
"Lafiya na ga my son ya wuce a firgice? Ke ma kamar wadda ranta ke ɓace." Mommy ta faɗa cikin mamaki ganin yanayin Salma. A shagwaɓe ta ba ta labarin duk abin da ya faru. Ashariya Mommy ta lailayo ta narka ta ce. "Khalifan ne ya mare ki? Yana cikin hankalinsa kuwa? Ko ya fara shaye-shaye ne?" Taɓe baki Ta yi cikin ƙara jin zafin abun a cikin ranta ta ce. "Wa ya san masa, amma wallahi bai mari banza ba, bayan Mine ya rama mini sai na kuma ɗaukar mummunan mataki a kan shi, sai ya gane kurensa, zai san da ni yake zancen." Mommy ta ce. "Gaskiya wannan yarinyar annoba ce, babu Alkhairi kwata-kwata a tattare da ita, daga saukar ku har ta yi sanadin abin da ya ɓata muku rai?" Ƙwafa Salma ta yi cikin ɗacin rai, har yanzu ba ta daina ganin lokacin da A'isha suka yi karo da Safwan a idonta ba. Runtse idonta ta yi jin kamar an saka mashi an soki zuciyarta, a yadda zuciyarta take tafarfasa lokacin da ta shaƙe A'isha ba don Khalifa ba da za ta iya kashe ta har lahira.
Chapter 48 · 0% Book details