← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 55

Sashe 50

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankali kwance take cin abincinta, tana ci tana latsa wayarta, lokaci zuwa lokaci tana sakin murmushi alamun tana enjoying abin da take. Shi kuwa ya kasa cin abincin na kirki saboda ɓacin ran Khalifa da ya cika masa zuciya. Miƙewa ta yi tare da kara wayarta a kunnenta, tana goge bakinta da tissue ta ce. "Mine bari na shiga ciki na huta kafin ka gama." Da sauri ya miƙe ya ce. "I'm ok ni ma." Ɓata fuska ta yi tana kallon plate ɗin abincin nasa ta ce. "Ka zauna ka ƙara ci, wannan ai babu abin da ka ci." Zai kuma magana ta ɗaga masa hannu, cikin bayar da umarni ta ce. "Ka yi abin da na ce kawai, make sure ka cinye duka kafin ka hawo sama, and you already know idan ba ka cinye ba ma ka ce mini ka cinye zan gane." Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi ya ce. "Shikenan Lovely zan cinye." Hannu kawai ta watsa ta yi gaba. Da kallo ya bi ta har ta ɓacewa ganin shi.

"Hello Mama ina jin ki yanzu, ban san kin ɗaga ba ɗazu, muna magana da Mine ne." Salma ta faɗa lokacin da take murɗa key ɗin ƙofar bedroom ɗinta ta rufe. Daga ɗaya ɓangaren Kaltum ta ce. "Okay Daughter, kun sauka lafiya? Ya hanya?"
"Lafiya ƙalau Alhamdulillah, Ina Daddy? Shi ne ko ya kira ni ya ji ya na sauka?" Ta yi maganar a shagwaɓe.
"Yana nan ƙalau, kin san yana Abuja, wannan weekend ɗin bai dawo ba sai next week."
"Allah Sarki Daddyna na yi kewar ku sosai Mama, na ɗauka zan tarar da ke a gida kin zo tarɓar ta."
Kaltum ta ce. "Kin san na yi accident last week, Har yanzu ƙafata ba ta gama warkewa ba."
"Ayya sannu, har na manta fa kin faɗa mini, ya ƙafar?"
"Ta yi sauƙi. Ya kuka yi da surukar taki ne? Na san yanzu tana can zuciyarta ta kusa bugawa."
Dariya Salma ta ƙyalƙyale da ita ta ce. "Ai in ma ba ta buga ɗin ba kenan, kin ga yadda ta ruɗe lokaci ɗaya? Daga ganin mood ɗinta ba ƙaramin shock ta shiga ba." Cikin dariya Kaltum ta ce. "Na sani dama, yadda take tinƙaho da alfahari da ɗan nan nata kamar a kanta aka fara haihuwa ko ita kaɗai ce mai ɗa namiji a duniya. Kaɗan ma ta fara gani, duk wulaƙanci da jan ran da ta yi mana kafin ki auri ɗanta duk sai mun fanshe shi a yanzu, dukiyar tasa ma da take taƙama da ita da sannu duk za ta zama tamu." Salma tana murmushin jin daɗi ta ce. "Gaskiya I'm lucky da samun ki a matsayin Uwa Mamata, ni fa yadda nake juya Ya Safwan kamar waina ya fi komai yi mini daɗi a yanzu. Duk wannan miskilancin da tsare gidan ya daina yi mini, yadda kika san zai mini sujjada fa don rawar jiki idan na ce ya mini abu."
"Good ɗiyar arziƙi, da fatan kin faɗa masa zancen mota da gold ɗin da na ce ki ce ya siya miki."
"Na faɗa masa, sarƙar ma gata nan a jakata na taho da ita, motar kuma ya ce ya yi order."
"Da kyau shu'umar Æ´a kamar uwarta."
Salma ta yi dariya ta ce. "Ai kin san barewa ba za ta yi gudu É—anta yay rarrafe ba."
Sun daÉ—e suna wayar kafin su yi sallama bayan Salma ta tabbatar mata tana nan tafe anjima kaÉ—an.

Tana cikin wanka ya shigo ɗakin, kayan jikinsa ya fara cirewa, yana ƙoƙarin shiga toilet ɗin ta fito tana goge jikinta da ƙaramin towel. Ba ta kalli inda yake ba ta nufi gurin mirror.
"Lovely." Ya kira ta cikin kamilalliyar muryarsa.
Juyowa ta yi tana kallon shi tana jin yadda son shi ke ƙara mamaye ko wane saƙo dake cikin zuciyarta. Takowa ya yi a hankali ya mannata da jikinsa tare da faɗin. "Me ya sa kika yi wanka ba ki jira ni ba?" Ɗan yamutsa fuska ta yi tare da raba jikinta da nasa ta ce. "Ina sauri ne zan fita."
"Fita kuma?" Ya faÉ—a cikin mamaki.
GyaÉ—a masa kai ta yi tare da zama ta É—auko wani tsadadden lotion ta fara shafawa a jikinta. A raunane ya ce. "Ina za ki?"
"Gidan Mama." Ta ba shi amsa a taƙaice alamun ya fara takura mata.
"Okay, lemme take shower sai na kai ki."
"No need." Ta faÉ—a cikin haÉ—e rai.
Sororo ya tsaya yana kallon ta, zai kuma magana ta ɗaga masa hannu tare da faɗin. "Tunda na ce bana buƙata ka ƙyale ni mana, ka fiya naci fa sometimes."
"I'm sorry." Ya faɗa tare da shigewa toilet. Tsaki ta ja tare da tashi ta ƙarasa wardrobe ɗinta dake cike da kaya ta zaɓo wata doguwar riga mai bin jiki ta saka. Kafin ya fito daga wanka har ta kammala shiryawa ta fice daga ɗakin.
Part ɗin Mommy ta je ta yi mata sallama tare da karɓar car key. Har ta juya za ta fita Mommy ta ce. "Da kanki za ki yi driving har Gandu Salma? Ina Safwan ɗin?"
"Yana kwance, wai ya gaji ba zai iya fita ba, ni kuma gaskiya na ƙagu na ga Mama, that is why zan tafi ni kaɗai." Gyaɗa mata kai kawai Mommy ta yi tana jin zuciyarta ta fara samun sassauci a game da fargabar tunanin ta shanye mata ɗa da ya hana ta sukuni tun ɗazu. Da alamun abun da ta zarga ba gaskiya ba ne, tunda ga shi Salman za ta gurin mahaifiyarta ya ƙi bin ta, kuma ta haƙura dole za ta tafi ita kaɗai. Da ta asirce shin ai za ta masa dole ta ce sai ya raka ta, kuma dole ya yin. Salma kuwa murmurshi ta yi ta juya ta fita. Ta san yanzu ta saka mata wasi-wasi a cikin ranta kamar yadda Mama ta ce mata ta dinga raba mata hankali biyu, yadda abin zai fi ɗaga mata hankali ta rasa tudun dafawa ta kasa samun mafita. Har zuwa lokacin da duk wani shirinsu zai kammala, lokacin da ɗan da take taƙama da shi ɗin ganin shi ma sai ya yi mata wahala..........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖

*_Zeey Kumurya_*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*3️⃣0️⃣*

Maimakon ta yi hanyar da za ta kai ta Gandu kamar yadda ta ce sai ta yi cikin Nasarawa G.R.A. Tafiyar mintuna kaɗan ta kai ta bakin ƙofar gidan da ta nufa, bayan ta danna horn mai gadi ya buɗe mata gate ta tura hancin motarta ciki zuciyarta cike maɗaukakin farinciki.

Mata ne su huɗu zaune a cikin wani ɗaki cikin shigar da ba ta da maraba da tsirara. Biyu daga cikinsu na kan gado sun ba je suna zuƙar shisha. Sauran kuma suna kwance a kan carpet ɗin gaban gadon suna kallo a system. Jin shigowar mota ya saka su ɗago kai a tare gabaɗayansu. Ɗaya daga cikinsu mai suna Ramcy ta ce. "Salma Baby an ƙaraso kenan?" Ta ƙarshe maganar tare da tashi ta ɗaga labulen window tana leƙen waje. Shigowar ta ya saka su fasa ihu gabaɗayansu tare da nufar ta cikin murna suka ruƙunƙume ta suna faɗin. "Welcome." Dariya ta yi cikin matuƙar jin daɗi ta ce. "My babies I missed you so much."
"Kin ga yadda kika canza kika yi kyau kuwa?" Ramcy ta faÉ—a lokacin da take zaunar da ita a bakin gado. Murmushi ta yi cikin daÉ—in yabon ta da Ramcy ta yi ta ce. "Ba dole ba tunda ina tare da Mine."
Fadeela tana zama a kusa da ita ta ce. "Okay, ko kewar mu ma ba ki yi ba kenan?" Kuncinta ta shafa ta ce. "Faɗar irin kewar ku da na yi ɓata baki ne my guys, kawai dai kun san yadda nake tsananin son Mine kasancewa tare da shi ba ƙaramin abin farinciki ba ne a gare ni." Ba su kuma mata magana akan Safwan ba suka cigaba da murnar ganin ta. Daga nan suka zarce da abin da suka saba aikatawa na neman junansu.

Tunda ya fito bai gan ta a ɗakin ba ya san ta tafi, maimakon ya ji haushi akan abin da ta aikata na ƙin yi masa sallama sai ya ba ta uzurin may be sauri take ta je ta ga Mahaifiyarta. A gaggauce ya shirya ya fito ya shiga part ɗin Mommy. Tana zaune a downstairs Atine na mammatsa mata ƙafa ya shiga parlour'n bakinsa ɗauke da sallama. Cikin fara'a Mommy ta ɗaga kai tana kallon shi tare amsa masa. Ƙarasawa ya yi ya zauna a kusa da ita. Kallon Atine ta yi cikin isa ta ce. "Ke tashi ki fita." Cikin girmamawa ta miƙe jiki na rawa ta fice bayan ta gaishe da Safwan. Kansa Mommy ta shafa tana murmushi ta ce. "Yanzu Abbanka ya kira ni ya tambaye ni ka sauka lafiya, ya kira sim ɗinka na Nigeria ba ya tafiya." Lumshe idonsa ya yi ya buɗe ya ce. "Ban saka sims ɗin a cikin waya ba ne har yanzu." Mommy ta ce. "Haka na ce masa." Ya numfasa ya ce. "Bari na je masallaci Mom."
"Toh shikenan, idan ka dawo ina son magana da kai." GyaÉ—a mata kai ya yi tare da tashi ya fice.
Ganin ba a fara kiran Sallah ba ya nufi part ɗin Ummi. A'isha na zaune ita kaɗai tana cin abincin da Ummin ta tilasta mata kamar ba ta so ya shigo. Ƙarar Tv da yadda ya yi sallama a hankali ya sa ba ta ji shigowar shi ba. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa ya nufi bedroom ɗin Ummi.
Chapter 50 · 0% Book details