← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 55

Sashe 24

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bakin ruwa wani ɗan ƙaramin ruwa ne a cikin garin dake bayan gidan Sarki, duk ranar asabar da yamma ƴan'mata da samari na taruwa a gurin a yi wasanni, har kid'a ake bugawa wasu su shiga su yi rawa, gefe guda kuma ga masu siyar da abubuwan siyarwa kala_kala. Yau ma kamar kullum an cika a gurin, wasu na tad'i wasu suna cikin ruwa suna wanka. Kallon abubuwan da suke faruwa Umar ya tsaya yana yi, dan duk zamansa a cikin garin bai taɓa zuwa gurin ba sai yau. A'isha dake cikin farinciki ta ce. "Ya Umar mu je mu shiga ruwa." Kallon ta ya yi ya ce. "Ruwa kuma Humairah? ke da ba gani kike ba sai kin je ya tafi dake?" Shagwab'e fuska ta yi ta ce. "Ruwan fa k'arami ne ba shi da zurfi, kuma ba shiga za mu yi ba ƙafafuwanmu kawai za mu saka a ciki." Bai ce komai ba ya ja ta zuwa bakin ruwan ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna. Fiye da rabin mutanen gurin kallon su suke yi, musamman ƴan'mata da ba ƙaramin tafiya da hankalinsu Umar ya yi ba. A hankali ya zarewa A'isha takalmin ƙafarta ta zira ƙafafuwan nata a cikin ruwa fuskarta ɗauke da murmurshin dake nuna tana cikin farinciki. Tana ta wasa da su a cikin ruwan shi kuma yana ta aikin kallon ta, cikin ransa yana yaba kyawun halittarta, babu abun da ya fi burge shi a tattare da ita kamar kalar fatarta da dara_daran idanunta. Lumshe idonsa ya yi yana jin yanda son ta yake ƙara mamaye ko'ina a cikin zuciyarsa. After 15 minutes ya ce mata su tashi su je su saya wani abun su ci, shago suka shiga ya siya mata choculate da drinks. Suna zaune a ɗan nesa da ruwan kaɗan A'isha tana shan choculate ɗinta ta ce. "Yaya Umar ka ga gurin akwai daɗin zama ko? Ina son zuwa tun daa Inna ce ba ta bari na." Umar ya ce. "Eh, dan gaskiya ina cin dariya tunda na zo gurin nan, musamman in naga an shiga filin rawa ana cashewa." Ya ƙarashe maganar cikin dariya. A'isha ta yi murmurshi ta ce. "Ko mu ma mu je mu yi ne?" Waro ido ya yi ya ce. "Ai ban iya ba, ni dai mu zauna a nan ki bani labari mai daɗi." A'isha ta ce. "Ni ba ni da labari, sai dai kai ka ba ni na ƴan'gidanku dama baka taɓa ba ni ba." Karɓar choculate ɗin hannunta ya yi ya ce. "Sai dai na baki na budurwata, kina so?" Ɓata fuska A'isha ta yi ta ce. "Bana so." Tare da ɗauke kanta gefe. Murmurshi Umar ya yi ya ce. "Shikenan ga choculate ɗinki cigaba da sha." A'isha ta ce. "Na ƙoshi." Karyar da kai ya yi yana kallon ta kawai, ita kuwa sai ƙare haɗe rai take tana turo baki gaba. Cikin sanyin murya ya ce. "Wai me ya faru na ga kina ɓata rai?" Kamar zata yi kuka ta ce. "Babu komai." A hankali ya ce. "I'm sorry, bana son na gan ki a irin wannan yanayin." Sakin fuska A'isha ta yi jin yanayin da ya yi magana ta ce. "Shikenan Yayana, ka san me?" Ya ce. "A'a." Ta ce. "Yau so nake ka mun waƙa mai daɗi." Da mamaki ya ce. "Waƙa kuma?" Ta ce. "Eh." Ya ce. "Ai ban iya ba." Cikin shagwab'a ta ce. "Ni dai kamun ko in yi kuka." Sauke numfashi ya yi ya ce. "Shikenan zan miki, amma ban iya na Hausa ba dan bana jin su." A'isha ta ce. "To ka mun ko ma wacce ce." Ɗan jim ya yi sannan ya yi gyaran murya ya fara rere mata waƙar cikin daddaɗar muryarsa.

"_*I'm in love with my Bestie and I don't know what to do.......*_

_*Sometimes I dey feel say She dey feel the same way I do.........*_

_*But she day call me brother I no dey bab that thing........*_

_*'Cause sometimes we dey act like lovers Wey we dey do more things........*_

_*My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie Eh........*_

_*If you dey hear this song just know sey somebody fall for you.*_

_*My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie Eh.......*_

_*I know sey I no for catch feelings but ebe too risky to loose you to another one oo.........*_

_*So somebody tell me wetin man for do*_
_*Cause I no wan lose wetin I get plus you.*_

_*So somebody tell me wetin man for do*_
_*Cause I no wan lose wetin I get plus you......*_

_*Is it my brain or my body? May be my heart no well.*_

_*Aw Bestie eh wherever you dey I say you for hear me today I don't care if I shy for your face........*_

_*So Bestie, you no dey wonder why The girls girls no dey come my way no more times your jealousy sef dey blow ma mind*_
_*But Edey give me whim so I dawg them all*_
_*Now as you then your guy Shon I hope say we go fit to go the next level.........*_

_*'Cause the feeling dey grow strong make we look sharp before we start to blame devil........*_

_*Somebody tell me wetin man for do*_
_*Cause I no wan lose wetin I get plus you......*_

_*Somebody tell me wetin man for do*_
_*(Somebody tell me wetin man for do)*_
_*Cause I no wan lose wetin I get plus you*_
_*(I'm in love with my Bestie yeah).*_"

A'isha dake sauraren sa ta lumshe ido jin ya yi shiru ta ce. "Amma wannan waƙar nan ta yi daɗi sosai, zaka dinga yi mun kullum?" Umar dake kallon ta ko ƙifta ido ba ya yi ya ce. "Why not? Zan dinga yi miki mana." Ta buɗe idonta ta ce. "Na gode sosai, yanzu mu je mu ƙara shiga cikin ruwa, daga nan sai mu tafi gida." Umar ya ce. "Magriba fa ta kusa, kuma Mama ta ce kar mu yi dare." Cikin marairaicewa ta ce. "Muna shiga fa za mu fito, kawai ɗan wasa zan yi da ƙafata a ciki." Umar ya ce. "Shikenan mu je." Ya kama hannunta suka tashi suka ƙarasa bakin ruwan suka zauna, kamar ɗazu ita kaɗai ta saka ƙafarta shi bai saka ba. A hankali ya kai ragowar choculate ɗin da ta rage bakinta, matsar da fuskarta ta yi ta ce. "Mene wannan?" Ya ce. "Buɗe bakin, choculate ɗinki zan baki." Za ta yi magana ya ce. "Please...!" Numfashi ta sauke ta buɗe bakinta a hankali ya saka mata ta gutsara ta fara sha cikin jin kunya, ƙasa ta yi da kanta tana jin kamar ta yi sab'o yau namiji ya ba ta abu a baki, ga wata irin kunya da ta ji ta lullub'e ta. Yalwataccen murmushi ya saki yana jin wani irin feeling a ransa a game da ita gami da wani irin nishad'i, damuwar da Mom ta saka masa ɗazu duk ya neme ta ya rasa. Can ƙasan mak'oshi ya ce. "Humairah...!" Ta ɗago kanta da niyyar amsa masa suka ji an musu wata irin hankad'a ta bayansu, lokaci ɗaya suka tafi za su faɗa cikin ruwan gaba-d'ayansu............✍️

```Barkanmu da shan ruwa, dafatan an sha ruwa lafiya? Allah ya karɓa mana.```

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*1️⃣3️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
Chapter 24 · 0% Book details