Sashe 55
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Kafin 8 sun je asibitin, Abba ya biya kuÉ—in aikin, ba a saka ranar aikin da nisa ba, Monday za a yi mata da safe.
Tunda suka dawo gida A'isha take kwance a É—aki, ta rasa me ya sa tsoro mai tsanani ya kamata akan aikin.
Misalin ƙarfe ɗaya Ummi tana kitchen tana girki Muneefah ta shigo parlour'n da gudu tana ƙwala wa Ummi kira, ta manta da wani langwaɓewa na pretending ɗin cuta da take. Ganin babu kowa a parlour'n ta nufi kitchen ta rungume Ummi ta baya.
Ummi ta ce. "Mene haka? Bana son shashancin nan naki fa?" A shagwaɓe ta ce. "Kai Ummi, duk murnar ganin ki ce fa." Ummi ta ce. "To patient, cutar kenan?" Murmushi ta yi ta ce. "Ina ganin ki na warke Ummita."
"Allah ya shirye ki Muneefah, da kin yi haÆ™uri ma jibi za a yi hutu." Æata fuska ta yi ta ce. "Ni fa bana son boarding school É—in nan ko kaÉ—an, Abba yana dawowa zan faÉ—a masa a mayar da ni Day." Ummi ta ce. "Zan fi kowa murna da hakan, dama aikin gidan nan ya mini yawa, in kina nan kuwa sai dai na miÆ™e Æ™afa." Ta ce. "Toh shikenan, bari na Æ™arasa na ga É—akina, na yi kewar shi."
A'isha tana kwance ta ji an shigo ɗakin, Muneefah ba ta lura da ita ba har ta ajiye trolley ɗinta. Sai da fara cire kayan jikinta ta lura da A'isha. Da mamaki ta ce. "Ihsan ko Mufeedah?" Miƙewa zaune A'isha ta yi don ta fahimci autar Ummi da ake yawan zancen ta ce ta dawo.
"Sannu da zuwa."
Muneefah ta ce. "Yawwa." Tare da juyawa ta fice daga ɗakin da sauri. Gurin Ummi ta koma tana faɗin. "Ummi wace ce waccan a ɗakina mai kama da ni?" Ummi ta ce. "Yar'uwarki ce." Cikin jin daɗi ta ce. "A gidan nan take?" Ummi ta ce. "Eh." Da murna ta ce "Na samu abokiyar hira, Allah ya sa kar ta tafi, mu yi ta zama tare." Ta ƙarashe maganar tare da juya cikin sauri ta koma ɗakin.
Bayan ta zauna a kusa da A'isha ta ce. "Ya sunanki?"
"A'isha."
"Sunan Maman Ummi da Abba da Ya Maamah."
A'isha ta yi murmurshi kawai.
Muneefah ta ce. "Ni kuma sunana Khadija, sunan ƙanwar Ummi ne shi ya sa ake ce mini Muneefah." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Ba ta damu ba ta cigaba da magana. "Kina da kyau Masha Allah, ga kalar fatarki ma mai kyau, ana ganin kyan tawa amma taki ta fi, idanunki ma masu kyau irin na Yayanmu, ai kin san shi ko?" Girgiza mata kai A'isha ta yi alamun a'a.
Da mamaki ta ce. "Kuma Ya Khalifa ya ce mini ya dawo, shi ne babban Yayanmu, duk ya fi kowa kyau a gidan nan, Likita ne, yana da Hospital ɗinsa na kansa a bayan layin nan mai suna *S.S.GIƊAƊO*, sunansa da sunan Abba ya haɗa *Safwan Sa'id Giɗaɗo*." Ta taɓe baki sannan ta ce. "Amma matarsa sai ta dinga cewa S.S ɗin wai sunanta da nasa ya haɗa, wai Salma and Safwan, ko daɗi ma babu." Murmushi kawai A'isha ta yi, a ranta tana mamakin surutu irin na Muneefah, daga ji ita ma babu ruwanta. Ummi ce ta shigo ɗakin tana faɗin. "Kina nan kina cika ta da surutu ko?" Ta ce. "Hira fa muke yi Ummi."
"Ya yi kyau, ki kama hannunta ku je toilet ku yi alwala, idan kun yi sallar sai ku fito ku ci abinci, ki yi mata a hankali kuma saboda ba ta gani." Waro ido Muneefah ta yi ta ce. "Makauniya ce?" Ummi ta ce. "Ban sani ba, ki yi abin da na ce kawai." Cikin mamaki da tausayawa ta kama hannun A'isha tana faÉ—in. "I'm sorry sis, ban sani ba."
Da yamma Ummi ta dawo daga gidan rasuwa ta shiga ɗakin Muneefah ta tarar da ita tana shirya kaya a wardrobe. Daga bakin ƙofa ta ce. "Ina Nana na gan ki ke kaɗai?"
"Tana parlour a kwance."
Ummi ta ce. "Wanne parlour'n?"
"Parlour'n ƙasa."
Ummi ta ce. "To ni ban gan ta ba, mu je ki nunan inda take." Babu musu ta miƙe suka fita.
Ganin ba ta parlour'n a ruÉ—e Muneefah ta ce. "A nan fa na bar ta na shiga É—aki yanzun nan." Wani kallo Ummi ta wurga mata ba ta ce komai ba ta shiga duddubawa.
Wasa-wasa Æ™aramar magana ta zama babba, duk inda suke tunanin za su ga A'isha sun duba ba su gan ta ba. Hankali a tashe Ummi ta fita ta duba compound da bayan gidan amma ba ta gan ta ba. A ruÉ—e ta nufi gurin masu gadi ta tambaye su ko sun ga fitar A'isha? Suka ce mata ba su gani ba, kuma tunda ta fita har ta dawo babu wanda ya shigo gidan ko ya fita.........âœï¸
*Anan na kawo ƙarshen littafin KOMAI NISAN DARE part one, kamar yadda na faɗa kuma part two na kuɗi ne, mai so ya tuntube ni a 09047871750, sai na ji ku masoya.*