← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 55

Sashe 38

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhamdulillah rayuwa ta sauyawa su Inna, don harkar turo kaya nan ba ƙaramin taimakon su ta yi ba, don a yanzu sun fi ƙarfin ci da sha da wasu buƙatun. Ƙalubale da ƙuncin rayuwa sun ci karanci a gare su, duk da ba su daina fuskantar tsangwama da tsana daga mutane ba, amma hakan ba ya damun su, sun toshe kunnuwansu tare da miƙa komai ga Ubangiji. A'isha ta ƙara girma da zama ƴanmata, kasancewar tana da garin jiki da diri Masha Allah. Har wannan lokacin ta kasa mantawa da Umar a cikin ranta, musamman idan ta kalli zobensa dake sanye a ɗan'yatsanta wanda ya ba ta. Yanzu tana J.S.S 3, suna daf da zana jarabawar junior WAEC. Har wannan lokacin Inna ba ta ba ta labarin asalinsu ba, ita ma ba ta kuma tambayar ta ba, amma kullum da son jin hakan take kwana take tashi.

Yau da yamma Inna tana yanke mata farce ta ce. "Insha Allahu wani watan dai za mu je asibiti a duba idon nan naki." Cikin farinciki A'isha ta ce. "Allah ya kai mu." Inna ta ce. "Amin, don ma kuɗin ya ƙi taruwa ai da tuni mun je, kullum da rashin ganin nan naki nake kwana nake tashi, abun yana damuna sosai, sai dai babu yadda muka iya da ikon Allah, haka ya so da mu." A'isha ta ce. "Ni fa Inna har na saba da rashin ganin yanzu, gani nake ma kamar idon ba zai buɗe ba." Cikin tausayawa Inna ta ce. "Zai buɗe da yardar Allah, ai ba a cire rai da rahamar Ubangiji."

"Allah ya sa Innata, ni ma ina so ya buɗe ko don na ƙara ganin ki a rayuwata, na ga ya kika koma yanzu."

Murmushi Inna ta yi ta ce. "Yadda kika san ni haka nake, ba abun da na ƙara sai tsufa." Ita ma murmushin ta yi, cikin ranta tana addu'ar Allah ya amsa addu'arsu idonta ya buɗe.

Cikin dare suna cikin bacci A'isha ta ji ana lalubar ta cikin wata irin siga da ta kasance baƙon al'amari a gare ta, a firgici ta farka jin ana ƙoƙarin danne ta tare da ƙwala kiran sunan Inna.........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*2️⃣1️⃣*

Kamar an saka iska an janye mutumin haka A'isha ta ji ya tashi daga jikinta cikin sauri, kuka ta fashe da shi tana ƙara kiran sunan Inna.

"A'isha! A'isha! Lafiya? Me ya faru?"
Inna ta tambaya a gigice bayan ta farka tana laluben fitila.

Cikin rawar murya da na jiki A'isha ta ce. "Wa...wani ne ya shigo mana Inna." Haske ɗakin Inna ta shiga yi cikin matuƙar tashin hankali, tabbas cikin bacci ta ji kamar mutum ya taka ƙafarta, har tana shirin tashi ta yi wa A'isha faɗa, a zatonta ita ce ta tashi fitsari. Babu kowa a ɗakin, alamun wanda ya shigo ɗin ya yi nasarar tserewa. Ganin yadda A'isha take kuka da rawar jiki wanda ke nuna ba ƙaramar firgita ta yi ba, Inna ta tashi ta ƙarasa kan gadon ta rungume ta. Ƙanƙame Inna ta yi tare da sakin ajiyar zuciya. A ruɗe Inna take haska jikinta tare da faɗin. "Me aka yi miki? Ta yaya kika san wani ya shigo?" Cikin ƙunar rai ta ce. "Ji na yi ana tattaɓa ni tare da ƙoƙarin hawa kaina."

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."
Inna ta ambata cikin bugawar zuci, wani irin juyawa ta ji kanta ya mata, lokaci ɗaya jiri na neman kwasar ta. Kamar wadda ƙwai ya fashewa a jikinta ta zauna a kan gadon tana jin kamar jini ya daina dawo a jikinta, har lokacin A'isha tana jikinta tana cigaba da kuka. Sunayen Allah da duk addu'ar da ta zo bakinta take karantawa, har ta fara dawowa cikin nutsuwar ta. Cikin sauke numfarfashi ta ce. "Wai me muka yi wa mutane ne? Me ya sa kullum cikin ƙoƙarin saka mu a ƙuncin rayuwa da son cutar da mu ake? Waye wannan ya zo yake ƙoƙarin ɓata miki rayuwa?" Sai ta fashe da kuka, wanda ya ƙara tsinka zuciyar A'isha, ta ƙanƙame ta sosai tare da tsananta kukanta. Ganin kuka ba shi ne mafita ba Inna ta rarrashi kanta ta miƙe ta fara haɗa musu kayansu da abubuwa masu amfani a gare su, ta kai maƙura kuma, abubuwan da ake musu a garin nan ya ishe ta, ko garin gwal ne yau za ta bar shi, ba don dare ba ne da ko awa ba za ta ƙara a cikinsa ba. Ana yin Sallar Asuba ta fito da komai nasu tsakar gida ta kulle ɗakin tana jiran gari ya fara haske su tafi. A'isha da take jin ta tamkar mai cuta ta kama hannun ta, cikin muryar da ta ci kuka ta ƙoshi ta ce. "Don Allah Inna mu koma gurin danginmu, kar mu kuma zuwa inda ba mu alaƙa da su a wulaƙanta mu." Hawaye mai zafi ne ya zubo daga idon Inna, cikin raunin murya mai tattare da ɗimbin damuwa ta ce. "Duk abin da kika ga ya koro ɓera daga rami ya faɗa wuta, to ya fi wutar zafi, ban taɓa tunanin rayuwa za ta zo mini a haka ba, ban taɓa tunanin zan bar rayuwa a cikin ƴan'uwana da dangina ba, amma wani dalili mai ƙarfi ya sa na aikata hakan." Zuciyar A'isha ta sauke, cike da kwaɗayin son jin labarin asalinsu ta ce. "Mene ne dalilin?"

"Ke ce."

"Ni kuma Inna? Me ya faru da ni? Ta tabbata gaskiya ne Baba Malam ba shi ne mahaifina ba?"

Cikin kuka Inna ta ce. "Gaskiya ne, ba shi ba ne."

Runtse ido A'isha ta yi cikin tsananin tashin hankali, duk da zuciyarta ta daɗe da ba ta tabbacin hakan, amma da Innan ta ƙara tabbatar mata sai damuwar ta akan hakan ta ninku, domin kodayaushe cikin fatan Inna ta ƙarya mata hakan take yi. Cikin magana da ƙyar ta ce. "Waye mahaifina to? Don Allah ki sanar mini kar zuciyata ta fashe." Janyo ta Inna ta yi ta rungume tare da faɗin. "Akwai lokacin da nake jira kafin na sanar miki da labarin komai, ki ƙara haƙuri. Ki kuma sani rayuwa cike take da tarin ƙalubale, duk halin ƙuncin da kake ciki wani yana cikin fiye da naka, a kullum ina faɗa miki ki karɓi rayuwa a duk yadda ta zo miki, duk abin da kika ga ya same ki rubutacce ne daga Ubangiji tun fil azil, ki kasance mai gode wa Allah a duk halin da kika tsinci kanki a ciki. Duk wannan abubuwan da suke faruwa za su wuce su zama tarihi watarana da yardar Allah, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, mu ci gaba da addu'a kawai." Ɗaga mata kai ta yi tare da ƙara damƙe hannunta a cikin nata, cikin sanyin murya ta ce. "Ke ce komai na rayuwata Inna, kin sha wahala sosai a kaina, Allah ya biya ki da gidan Aljannah, ina son ki fiye da kowa da komai a duniyar nan." Murmushi Inna ta yi mai haɗe da hawaye ta ce. "Babu wahalar da nake sha a kanki, ki daina faɗar haka." Jan majina Aisha ta yi ta ce. "Wataƙila da ke kaɗai kika zo garin nan babu ni ba za ana yi miki cin fuska kamar wanda ake yi miki yanzu ba."

"Hmmmm" Kawai Inna ta ce tare da sauke numfashi.

"Tashi mu tafi, na ga garin ya fara haske."

"Wai ina za mu je?"

"Kano gurin Innar Ma'u, idan muka sauka a tasha zan nemi waya na biya kuÉ—i a kira mini ita tunda muna da lambarta."

Nunfasawa A'isha ta yi ta ce. "Amma Inna sai nake ganin kamar in muka je za mu ɗora musu nauyi ne." Inna ta ce. "Ba zaman dindindin za mu yi a gurinsu ba, gidan aiki zan nema ko wanke-wanke da shara da wankau ne na dinga yi ana biya na, ko a washegarin ranar da muka je na samu gidan aikin sai mu tafi." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke ta ce. "Allah ya sa a dace." Inna tana miƙewa ta ce. "Amin."

Sai da suka daɗe a tasha kafin mota ta cika su ɗauki hanya, kallon ƙarshe Inna ta yi wa garin KUMURYA cikin wani irin yanayi, ranar da ta zo garin ce ta faɗo mata a rai. A'isha ta rasa me ya sa ta ji zuciyarta wani iri, ta daɗe tana fata da addu'ar Allah ya kawo ranar barin su garin, amma kuma ga ranar ta zo ta kasa yin farinciki. Sai ma faɗuwa da ta ji gabanta yana yi. Kwantar da kanta ta yi a jikin Inna tare da lumshe idonta. Cikin kulawa da ƙauna Inna ta ɗora hannunta a bayanta ta ƙara shigar da ita cikin jikinta. Ƙarfe goma da mintuna na safe suka sauka a garin Kano a tashar KANO LINE. Sai a lokacin Inna ta tuna ko sunan Unguwar su Innar Ma'u ba ta sani ba, direban da ya tuƙo su ta roƙa ya ba ta aron wayarsa ta kira ta. Bayan ya ba ta, ta saka lambar ta kira aka ce akashe. Ƙara kira ta yi still nan ma switch up. Jiki a sanyaye ta miƙa masa wayar tare da yi masa godiya ta kama hannun A'isha suka fara tafiya.

"To yanzu Inna ina za mu je?"
Chapter 38 · 0% Book details