Sashe 27
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
.........Bayan fitar Haulatu Uwa ta ɗauki wayarta ta yafa mayafinta ta fita zuwa turakar Mijinta. Sarki yana kishingide a k'aton falonsa da yake hutawa a cikin gida Uwa ta yi sallama, ya amsa tare da ba ta izinin shigowa. Bayan ta zauna a gabansa ta ce. "Ranka ya daɗe barka da yamma." Sarki ya ce. "Yawwa." Uwa ta gyara zama fuskarta ɗauke da murmurshi ta ce. "Dama zuwa na yi in yi maka tsokaci akan wani abu da yake gudana a cikin gidan nan." Sarki ya ce. "Me kenan Uwa?" Ya ƙarashe zancen tare da tashi zaune sosai. Uwa ta ce. "Wato ranka ya daɗe yaron nan Umar yaron kirki ne irin Albarka, mutuncin da yake yi mana a gidan nan da girmama mu ba zai faɗu ba, ga Alkhairi akai_akai." Sarki ya yi murmushi ya ce. "Allah Sarki Ummarul Faruq, ai indai ya yo halin mahaifinsa to kaɗan ma kika gani, dan ni ban ma san ya zan misalta miki karamci da kirki irin na Alh. Aliyu ba." Uwa ta washe baki ta ce. "Masha Allahu, haka ake son mutane su dinga kasancewa masu kyawawan d'abi'u wanda za'a dinga yabon su da shi, ni yanzu daka ganni wani babban Alkhairi ya yi mun da na ji daɗinsa sosai, har na kasa jurewa na ce gaskiya sai na karb'i Lambar Mahaifiyarsa na kira ta na gaishe ta darajar abun da ɗanta ya yi mun." Jinjina kai Sarki ya yi ba tare da tunanin komai ba ya ce. "Hakan yana da kyau, dama kamata ya yi a ce tun da kuna gaisawa da juna." Uwa ta ce. "Haka ne Ranka ya daɗe, yanzu ma ai ba ta ɓaci ba sai mu fara ɗin." Sarki ya ce. "Sai dai kuma ba ni da lambar mahaifiyar tasa, amma abun da za'a yi bari na kira Alh. Aliyun na yi masa bayani sai ya tura mun." Uwa da jikinta har ɗan rawa yake saboda zumud'i ta ce. "To..to Ranka ya daɗe." Sarki ya ɗauko wayarsa ya kira Alh. Aliyu, ringing kaɗan ya daga, suka gaisa tare da tsokanar juna cikin barkwanci sannan Sarki ya yi masa bayanin dalilin kiran sa da ya yi. Cikin jin daɗin abun da Sarki ya faɗa masa ya ce zai tura masa lambar suna gama wayar. Mintuna biyu da gama wayar tasu ya tura masa lambobin har guda biyu, Sarki ya kwafarwa Uwa a cikin wayarta ya ba ta. Cikin tsananin farincikin ta dinga yi masa godiya, har abun ya so ya bawa Sarki mamaki, amma sai ya danganta hakan da may be duk cikin jin daɗin Alkhairin da ta ce Umar ya yi mata ne. Cikin sauri ta ƙarasa ɗakinta ta tarar Haulatu ta dawo, Haulatu ta ce. "Uwa ina kika je? tun ɗazu na dawo nake jiran ki." Uwa ta cire mayafinta ta cillar ta ce. "Ina katin da kika siyo? bani_bani in saka da sauri, yau da sa'a na tashi, abun da na shirya a cikin ƴan mintuna har na samu nasara an wuce gurin." Haulatu ta karb'i wayar Uwa ta fara saka mata katin ta ce. "Me kika shirya?" Uwa ta ce. "Lambar mahaifiyar Umar na je samuwa a gurin Sarki, kuma wallahi cikin ruwan sanyi na samu, ban yi tunanin hakan ba ma." Haulatu ta ce. "Me zaki yi da Numbern ta ke kuwa? bayan kin ce ba ta da kirki." Uwa ta zauna ta ce. "Ke dai kira mun Lambar farko a gurin kira, ita ce tatan, zaki ga abun da zan yi da ita." Babu musu Haulatu ta yi dialling numbern, cikin sa'a bugu ɗaya ta shiga ta fara ringing, saka wayar ta yi a hands-free ta miƙawa Uwa, sai da ta kusan katsewa sannan aka ɗauka. Cikin kwantar da murya Uwa ta ce. "Assalamu alaikum, Ranki ya daɗe barka da yamma, dafatan an wuni Lafiya?" Cikin izza irinta Mom ta ce. "Yawwa, wake magana?" Uwa ta yi murmushi mai sauti ta ce. "Uwa ce matar Sarkin Kumurya abokin mijinki." Ɗan jim Mom ta yi tana tunani, lokaci ɗaya ta haɗe rai cikin ƙyama ta ce. "To ya aka yi?" Uwa ta ce. "Uhm dama akan yaronki ne Uwar na kira in faɗa miki wani muhimmin abu." Tsaki Mom ta yi wani irin takaici na cika mata zuciya, Umar ya ja mata yau tana waya da matar ƙauye. Cikin ƙagauta ta ce. "Ina jin ki." Uwa ta gyara zama ta ce. "Hajiya ba gulma ba ko wani abun, amincin dake tsakanin mijina da naki ne ya saka zan faɗa miki wannan abu....." Cikin hasala Mom ta ce. "Malama ki faɗi abun da zaki faɗa da'Allah cikin sauri, dan ina da abun yi." Ta ƙara jan tsaki cikin takaicin kanta da ta tsaya ma tana sauraren wannan yar ƙauyen, har za ta katse wayar ta tsinkayi muryar Uwa tana cewa. "Hajiya wata mata ce a cikin garin nan irin zuwau ɗin nan ba ƴar asalin garin ba ta lashe kurwar Umar tun zuwansa garin nan, da yake mayya ce ita, in tak'aice miki zance kullum yana gidanta gurin makauniyar ƴarta yana faman yin wahala da su, shine cinsu, shansu, suturarsu da komai nasu. Ta yi masa siddabaru irin nasu na mayu ta mallake shi ta cusa masa son ƴarta, kuma yarinyar ma fa makauniya ce, ba......" Cikin tsananin kad'uwa Mom ta ce. "What? Wanne Umar ɗin? Ba dai Faruq ɗina ba ko?" Uwa ta ce. "Shi mana, ko ba da matar Alh. Aliyu Kaduna nake magana ba?" Mom ta ma rasa me za ta ce saboda tsabar firgici, Son ɗinta ne Mayya ta kama shi ya tare a gindinta? Wato shi yasa ya ƙi barin garin? Tsabar ya raina mata hankali shine ya ce mata shukar da suka yi ce ta lalace sai da aka sake wata? ashe wata sabuwar shukar da zai tozarta ta ya bak'anta mata rai ya dasa? To kuwa wallahi zai san ita ce ta haife shi ba shi ya haife ta ba. Katse Wayarta ta yi ba tare da cigaba da sauraren soki burutsun zancen da Uwa ta cigaba da yi mata ba. Jiki a sanyaye Haulatu ta dubi Uwa ta ce. "Na shiga uku, haka dama matar nan take? Ji yanda take magana fa kamar irin da bayin nan nata take yi." Uwa ta ce. "Ai tafi ma haka, amma ni ko ajikina, yanzu plan ɗinmu na farko zai yi aiki sai mu tafi na biyu, dan na san a yau sai ta raba Umar da waccan makauniyar Yarinyar, ai ina sane na kunna ta, na san hankalinta ba ƙaramin tashi zai yi ba." Haulatu ta ce. "To amma idan mun ci nasara kina ganin wannan uwar tasa zata bari a yi auranmu da Umar kuwa?" Uwa ta ce. "Ki saka a ranki tamkar an yi gama, auranki da Umar ba, ni kaɗai na san ta inda zan ɓullowa al'amarin." Murmurshi Haulatu ta saki cikin jin daɗi, a ranta na hango ranar da za'a ce an aura mata aure da Uwar, wayyo daɗi, ta auri ɗan birni ɗan gayu kyakkyawa ɗan masu kuɗi, ranar ta san sai farinciki ya kusa hallaka ta.