Sashe 32
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da Magriba A'isha tana kwance akan gado zazzaɓi mai zafi ya rufe ta Inna ta shigo ɗakin dan yin Sallah, kallon inda take ta yi ta ce. "Za ki iya ki yin Sallah kuwa?" Girgiza mata kai ta yi. Inna ta ce. "Allah ya ƙara sauƙi, bari na yi Sallah na baki magani ki sha, sai ki daure ki yi Sallar." Hawaye kawai A'isha take yi, wani irin zafi da ciwo take ji a ƙirjinta, ga ciwon kai da ciwon ciki da ya bijiro mata lokaci ɗaya, ga sanyin da take ji yana shiga cikin ƙasusuwan jikinta, ga idanuwanta dake mata zafi saboda kukan da ta sha, ta rasa ina ma za ta saka ranta ta ji daɗi. Ajiyar zuciya kawai take saukewa akai_akai. Bayan Inna ta idar da Sallah ta zo ta ɗaga ta, ta zaunar da ita tana yi mata sannu, ragowar wani yoghurt da Umar ya kawo mata ta ɗauko. Cikin lallami ta ce. "Ki sha wannan sai ki sha maganin." Kawar da kai ta yi ta ce. "Ba zan iya sha ba Inna, cikina ciwo yake mun." Inna ta ce. "Yunwa ce, yau fa kwata_kwata ba ki ci abinci ba, ki sha wannan ɗin zaki ji daɗi." Daƙyar Inna ta samu A'isha ta ɗan kurb'i yoghurt ɗin ta koma ta kwanta. Inna tana shafa kanta ta ce. "A kullum ina faɗa miki ki dinga hak'uri da rayuwa a duk yanda ta zo miki A'isha, ki yi hak'uri ki cire damuwar tafiyar yaron nan daga cikin ranki, kar wani ciwon ya kama ki." Cikin rawar murya ta ce. "Shikenan fa ba mu da kowa a cikin garin nan, yanzu za'a cigaba da zaginmu da yi mana rashin mutunci tunda mai tare manan ya tafi." Inna ta ce. "Muna da Allah, a lokacin da su Ma'u suka tafi haka kike ce, bayan tafiyarsu babu jimawa kuma sai Allah ya aiko mana da Umar, to yanzun ma shi zai taimake mu ya ba mu yanda zamu yi, ki daure zuciyarki ki cire komai na damuwa daga cikinta, ko zaki samu ki ɗan yi bacci zuciyarki ta huta." Lumshe ido kawai ta yi, amma ta san yau duk iya satar bacci ba zai ɗauke ta ba, dan ba ta da nutsuwar yin sa ko kaɗan. Washegari ta tashi jikin nata da ɗan sauƙi, ta kuma daure iya iyayinta dan ganin ba ta yi kuka ba, saboda kar ta tayarwa da Inna hankali. Tun safe Matan gidan suke zarga a ɓangarensu suna yada musu maganganu da habaici akan tafiyar Umar, daga mai shigowa da shewa sai mai shigowa tana gud'a. Inna dai ko kallon inda suke ba ta yi, balle kuma A'isha da ta ji zaman garin gaba-d'aya ya ƙara fice mata a rai. Jiya wajen goma na dare haka Iya ta zo ta ƙarewa Inna zagi tass akan kwakwazon da Hansai ta yi na A'isha ta rungume Umar, har sha biyun dare ba ta bar Inna ta huta ba...... Kusan sati A'isha ta yi tana jinya kafin ta samu sauƙi, bayan ta sha allurai har da ƙarin ruwa. Ta ji sauƙin zazzaɓin da ciwon kai, ciwon cikin ne dai ya ƙi yi mata sauƙi, dan cikin dare haka za ta tashi ta kasa bacci tai ta juye_juye tana hawaye, sai Inna ta yi mata tofi a ruwa ta ba ta, ta sha sannan yake lafa mata.
Yau da yamma A'isha tana kwance a tsakar gida idanunta a lumshe amma ba bacci take yi ba, tunanin Umar take yi da moment É—insu da suka gudana masu tsayawa mutum a zuci, lokuta da dama sai Æ™amshinsa yay ta mata gizo a cikin hancinta, ta ji kamar yana kusa da ita za ta ji daddaÉ—ar muryarsa. A hankali ta saka hannu ta share hawayen da ya zubo mata, sannan ta juyar da kanta inda take jiyo sautin muryar Inna tana karatun Alkur'ani, cikin muryar marasa lafiya mai cike da damuwa ta ce. "Inna har yau bai kira ba ko?" Inna ba ta amsa mata ba sai da ta kai Æ™arshen aya, ta dube ta cikin rashin jin daÉ—i ta ce. "Ke da wayar kodayaushe take hannunki da ita kike kwana kike komai ai inda ya kira zaki ji." A'isha ta ce. "Ki kai wurin Abba mai caji anjima ya duba dai, ko an kira gani ne baki yi ba." Inna ta ce. "Amma ai da za'a ji Æ™arar kiran ko?" A'isha ta ce. "To ki kai a duba lambobin cikin wayar a kira, na san baza'a rasa tasa ba, idan ma babu sai mu cewa wanda mu kira dan Allah ya turo mana lambarsa muna son kiran sa ne." Inna ta ce. "Toh." A'isha ta lalubo wayar da kodayaushe tana kusa da ita tana jiran tsammanin kiran Umar a cikinta, amma har yau sati guda da tafiyarsa bai kira ba, abun da yake Æ™ara É—aga mata hankali kenan, ta kasa samun nutsuwar zuci. Daddanna wayar ta shiga yi ba tare da ta san inda take dannawar ba. Inna ta ce. "Ki ajiye wayar kar ki shiga wani gurin da za ta samu matsala kuma." Ba ta ce komai ba ta ajiye wayar. Duk maganganun da ta yi cikin dauriya ta yi su, dan ba Æ™aramin ciwo cikinta yake yi mata ba, lokaci É—aya ta ji ya yi mata wata irin murd'awa, da sauri ta tashi zaune tana salati hannayenta duka akan cikin nata. A kid'ime Inna ta yi kanta ta riÆ™e ta tare da tambayar ta lafiya? Babu bakin amsawa saboda aman da ta ji ya taso mata, a hanzarce ta miÆ™e da nufin ta Æ™arasa bakin rariya, sai dai bai fi taku uku ta yi ba ta tsugunna ta fara kelaya aman, Inna dake bin inda ta tashi da kallo ganin abun dake gurin ta É—ago ta kalle ta cikin wani irin yanayi..........âœï¸
*Ban yi edit ba*
*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*1ï¸âƒ£7ï¸âƒ£*
..........Sosai ta yi aman, hakan ya ƙara galabaitar da ita. Taimaka mata Inna ta yi ta wanke fuskarta ta cire kayan jikinta ta sauye wani ta koma ta kwanta tana numfarfashi. Inna tana gyara mata kwanciya ta ce. "Sannu, bari na je chemist na karɓo miki magani da audiga." Ɗaga mata kai ta yi duk da ba ta fahimci audugar me take nufi ba. Murɗawar cikin nata ya yi mata sauƙi, hakan ya sa take ta sauke ajiyar, wani irin abu take ji yana fita daga jikinta wanda ya kasance baƙo a gurinta, tunani ta dinga yi akan hakan amma ba ta fahimci komai ba har Inna ta je ta dawo.
Bayan ta yi wanka Inna ta ba ta pant É—in da ta saka mata pad a jiki kamar yadda Nurse É—in dake zaune a chemist É—in ta yi mata bayani. Cikin mamaki A'isha ta ce. "Inna mene wannan na ji shi a jikin wandon?"
"Auduga ce, wadda za kina amfani da ita har jinin al'adar da kika fara ya É—auke, ai kin san mene ne shi ko?"
Gabanta ne ya faɗi, jikinta ya yi wani irin sanyi ƙalau, ta san me jinin haila yake nufi, Malamar da suke zuwa gurin ta karatu ta yi musu bayani a kan shi sosai, ba tare da ta san dalili ba ta ji hawaye ya zubo mata.
"Ki saka wandon kar ki kuma ɓaci mana."
Cikin tsananin jin kunyar Inna ta fashe da kuka tare da saka wandon. Umarni inna ta ba ta akan ta zauna za su yi magana, ba ta yi musu ba ta zauna tana sharar hawaye. Cikin nasiha Inna ta ce. "Mene na kukan kuma? Abin da ba kanki farau ba, duk macen da kika gani a duniya tana yin jinin al'ada in dai ta kai munzalin farawa, wanda ba sa yi kuma yawanci ciwo ne, a yanda aka ce ma zai yi wahala su haihu in ba wani ikon Allah ba." Ita dai ba ta ce komai ba sai kukanta ta cigaba da yi. Nasiha sosai Inna ta yi mata akan yanzu girma ya hau kanta, an fara rubuta mata zunubi da lada kamar kowa, don haka ta ji tsoron Allah a duk inda take tare da tsare mutuncinta, ita dai ba ta tanka ba, kunya da yanayin da take ciki ya hana ta magana. Bayan ta ci abinci ta sha magani ta kwanta bacci.
Hayaniyar Iya da ta shigo tana yi wa inna tijarar da ta saba ce ya tashe ta daga baccin, lokacin har an yi Sallar Isha'i. Tsaki ta ja tare da tashi ta fito tsakar gida cikin lalaben hanya. Duk da yanda take jin rashin ƙwarin jikinta da cikinta da ya ɗaure mata, amma ta daure ta cewa Iya. "Wai don Allah Iya me muke tsare miki ne a gidan nan da kullum kike zuwa ki ishe mu da masifa?" A ƙufule Iya ta ce. "Ban sani ba, wato wuyanki ya yi kauri ko? Yar mitsitsiya dake amma har za ki faɗa mini wannan maganar? Ki ji da rashin ganin da ba kya yi mana, masu idon ma sun yi shiru sai ke makauniya ce mai bakin magana."
"Ai Allah ne ya yi Ni a haka ba ni na yi kai ba..."
"Ke! Rufe mini baki, me ya fito dake ma daga É—aki?" Inna ta katse ta cikin tsawa.
Kuka ta fashe da shi ta ce. "Toh Inna kullum sai ta zo ta dinga zagin ki kuma ba ki yi mata komai ba?" Ta yi maganar cikin tsantsar takaici.
"Ki cigaba da magana, tunda ban isa in ce ki yi shiru ki yi ba."
Ƙwafa iya ta yi ta juya ta fita tana cigaba da masifa.
Duban A'isha Inna ta yi ta ce. "Kar ki kuma yi mini haka A'isha, ko sa'ar ki ce Iyan da za ki dinga mayar mata da magana?" A raunane ta ce. "Ki yi haƙuri ba zan kuma ba."
"Shikenan, bari na haÉ—a miki ruwa ki yi wanka, dama yanzu nake shirin tashin ki."