Sashe 49
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da ransa a ɓace yake amma a nutse yake tafiya, da sallama ya shiga bedroom ɗin amma ba su amsa masa ba, sai ido da suka zuba masa suna jiran jin irin matakin da ya ɗauka akan Khalifa. Sanin halin miskilancinsa ba lallai ya yi magana ba ya sa Mommy ta ce. "Da fatan ka masa dukan mutuwa dai?" Idanunsa a kan Salma da ta tsare shi da ido ya ce. "Ban same shi ba."
"Uwarsa ta ɓoye shi kenan." Mommy ta faɗa a harzuƙe. Bai ce komai ba ya ƙarasa ya zauna a kusa da Salma tare da ƙoƙarin kama hannunta. Wani kallo ta wurga masa tare da miƙewa tsaye ta ce. "Babu abin da za ka ce mini Safwan, ai komai ya faru lefin ka ne, yarinyar ta rungume ka amma ka kasa ɗaukar mataki a kanta, sai kawai ka tafi ka bar ta, maimakon ka ture Shegiya ka yar da ita ta faɗi ka tattake cikinta? Amma ka ƙi saboda ba ka kishin kanka bare...." A tsawace Mommy ta katse ta faɗin. "Ya isa haka Salma, kin san bana son wannan tsiwar taki da rashin ɗa'ar da kike masa ko? Sai ka ce ba mijinki ba." Kuka ta fashe da shi tare da faɗin. "Amma Mom rungume shi fa wata ta yi a gabana, don na nuna ɓacin raina laifi ne? Mijina ne fa, kuma kin san ina tsananin kishin shi."
"Shikenan ya isa, mu je ƙasa ku ci abinci sai ku yi wanka ku huta, kar ki saka damuwar wasu sakarai a cikin ranki ki ɓata mood ɗinki, ki bar komai a hannuna za ki ga matakin da zan ɗauka." Mommy ta faɗi haka tare da juyawa ta fice. Da sauri Safwan ya miƙe ya janyo Salma jikinsa, kukan nan da take ji yake tamkar ana watsa masa garwashi a cikin ransa, yadda kukan yake taɓa ransa ba ya jin zai iya ƙara sakanni bai rarrashe ta ba, ko da a gaban Mommy ne kuwa. A ruɗe ya ce "Please stop crying My one, kin san babu abin da tsana a rayuwata sama da zubar hawayenki." Ƙara fashewa da kukan ta yi cikin son ta ƙara ɗaga masa ta ce. "Dole na yi kuka Mine, wata ce fa ta taɓa jikinka a gaban idona." Numfashi ya sauke mai zafi yana jin da zai ƙara ido huɗu da yarinyar sai na lahira ya fi ta jin daɗi, saboda sanadin zubar hawayen sanyin idaniyarsa da ta yi. Cikin rikicin da kukan nata ya ƙara saka zuciyarsa ya ce. "Taɓa jikina da ta yi ba ya nufin wani ba ne Lovely, kin fi kowa sanin ni naki ne ke kaɗai, wallahi duk macen da na gani kallon Namiji kamata nake mata, ke kaɗai idanuna suke gani a cikin mata, don Allah ki daina mini asarar hawayenki akan wata kucaka, Please Lovely kar zuciyata ta tarwatse." Ganin yadda ya rikice sai ta ɗan saki fuskarta tare da ƙara lafewa a jikinsa. Da ƙyar ya rarrashe ta, ta haƙura suka sauka ƙasa don cin abinci. Sai lallaɓa ta yake tamkar ɗanyen ƙwai, ita kuma tana ta ƙara botsarewa. Bayan ya ja mata ɗaya daga cikin kujerun dinning ta zauna ya ce. "Let me serve you dear, me kike son ci?" Yadda ya yi maganar tamkar bawa da Uwargijiyarsa ya sa Mommy da ta dawo parlour'n tsayawa cak cikin bugawar zuciya.
'Me take shirin gani haka? ÆŠanta Safwan tsayayyen mutum da ba ya É—aukar wargi tamkar mahaifinsa shi yake shirin zama mijin ta ce ko ma ya zaman?' Ta faÉ—i haka a ranta cikin tashin hankalin ganin irin kallon zallar rainin da Salma take bin shi da shi.
"Impossible!" Ta furta cikin sauke numfashi gumin firgici na tsatstsafowa a jikinta........âœï¸
*Rashin comment ya sa ba ni da karsashin yin dogon typing, idan kun gyara ni ma zan ƙara.*
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2ï¸âƒ£9ï¸âƒ£*
Jijjiga kai ta yi ta ƙarasa dinning area ɗin cikin ƙoƙarin ɓoye halin da take ciki. Fatanta da addu'arta Allah ya sa kar zarginta ya zama gaskiya, tana fatan a ce laifi Safwan ɗin ya yi wa Salma shi ya sanya yake mata haka don ta yafe masa. Saboda sanin da ta yi masa mutum ne wanda ba ya son ɓatawa kowa rai, ko da a cikin rashin sani ne, idan hakan ya faru ba ya jin kunya ko nauyin ya ba ka haƙuri don ka yafe masa, ko da kuwa kana ƙasan shi ne ya girme ka, ko kuma kana aiki a ƙarƙashinsa. A kodayaushe yana faɗa ba ya son mutuwa da alhakin kowa a kansa.
Wannan tunanin ya É—an sassauta zuciyar Mommy daga tsananin razanin da ta shiga lokaci É—aya. Idanunta a kansa ta ce. "Son ya kake zuba abincin da kanka? Ka bari yanzu Atine za ta zo ta zuba muku." Ba tare da ya bari ba ya ce. "Na ga tana jin yunwa ne sosai shi ya sa nake zuba mata."
"Ka bar shi na ce, tana matarka ita ba ta zuba maka ba sai kai za ka zuba mata?" Satar kallon Salma ya yi kamar mai jiran umarnin sai ta ce ya bari sannan zai bari, ɗauke kanta ta yi tana ƙeɓe fuska. Ba don ya so ba ya zauna still looking at her, so yake su haɗa ido ya rarrashe ta da idon amma ta ƙi. Mommy dake lura da su ta sauke numfashi mai tattare da ɗunbin takaici, da akwai matsala kenan? Don ta san wannan rawar jikin da Safwan yake yi ba na banza ba ne, dole sai da wani abun a ƙasa.
"I'm sorry Dear, ki ci abincin please."
Muryar Safwan da ya faɗi haka ƙasa-ƙasa ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Ganin yadda yake rawar jikin ɗebo abincin a spoon zai kai bakin Salma ya sa ta juyawa ta bar musu parlour'n cikin sauri tana haɗa hanya. Da kallo Salma ta bi ta tare da sakin wani shu'umin murmushi.
Zarya Mommy ta shiga yi a parlour cikin tashin hankali, me yake shirin faruwa da ita ne? Salma ta asirce mata ɗanta ne ko yaya? Girgiza kai ta yi da sauri tare da faɗin. "Hakan ba zai taɓa faruwa ba, na san Kaltum ba za ta taɓa cin amanata ba ko ta bar Salma ta ci."
'Amma kuwa rawar jikin da Safwan yake akan Salman fa? Wadda a da ba ya mata' Zuciyarta ta faɗa mata haka. Hannunta ta ɗora a kan goshinta ta shiga bubbugawa. Tabbas ta ga wani abu mai kama da tsoro a tattare da ɗanta da yake yi wa Salma. Zama ta yi ɗabas a kan kujera tare da haɗiyar wani yawu mai ɗaci. Tunanin yadda Salma take masifar tsoron Safwan a da ta tuna, amma yau ba ta ga hakan ba ko kaɗan a tattare da ita, sai ma zallar fitsara da isa gami da gadara ta gani. Jijjiga kai ta yi cikin ƙanƙance ido ta ce. "Babu shakka idan har khaltum cin amanata ta yi sai na nuna mata asalin kalata, don ba zai yiyu in shafe shekaru ina gini lokaci ɗaya wata ta zo ta rusa mini shi ba, zan cigaba da saka ido a kansu har na gano bakin zaren."
Ummi tana ƙoƙarin tashi ta ɗauko wa A'isha maganin ciwon kai da ta yi mata complain yana damun ta Ihsan ta shigo parlour'n kamar munafuka tana rarraba ido. Kallon da Ummi ta bi ta da shi ne ya sa ta shan jinin jikinta. Cike da tsoro ta ƙaraso ciki ta zauna kanta a ƙasa.
"Daga ina kike?" Ummi ta tambaye ta a kaushashe.
Cikin inda-inda ta ce. "Wani class mate ɗina ne a nan unguwar, muna chat ɗazu na ce masa ina unguwarsu, shi ne ya ce zai zo mu gaisa." Fuska babu walwala Ummi ta ce. "Shi ne ba za ki sanar mini ba kika fita a munafunce ko?" Shiru ta yi tare da yin ƙasa da kanta. A fusace Ummi ta ce. "I'm talking to you."
"I'm sorry Ummi."
"Sorry for yourself, kin fita ba da izinina ba sannan kin bar yarinya ita kaɗai a waje, kuma kin san ba gani take ba. Lefi biyu kenan." Ummi ta faɗa tare da yin ƙwafa.
Kamar za ta yi kuka ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri Ummi b...."
Hararar da Ummi ta wulga mata ya sa ta haÉ—iye sauran maganarta. Ummi ba ta kuma magana ta miÆ™e ta haye sama. Ajiyar zuciya Ihsan ta sauke ta miÆ™e ta koma kusa da A'isha. Kallo É—aya ta yi mata ta gane ta yi kuka, da damuwa ta ce. "Me ya faru Nana na ga kamar kin yi kuka?" Æata fuska ta yi ba ta ce mata komai ba, saboda haushin ta take ji tunda ita ce sanadiyyar faruwar komai.
"Allah ya sa ba faɗuwa kika yi ba ko wani abu ne ya same ki?" Ihsan ta faɗa tana dudduba jikinta. Ganin yadda ta damu sai A'isha ta faɗa mata abin da ya faru in brief. Cikin takaici da ɓacin rai ta ce. "Kan Uba! Mari fa kika ce da shaƙa? Taɓɗijan! Da ma fa matar nan Mahaukaciya ce, Shegiya mai kama da fatalwa." Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki. Sai kuma ta sassauta murya ta ce. "Ki yi haƙuri Please Nana, na yi sanadin da aka taɓa lafiyar jikinki kina zaman-zamanki, wallahi ban san zan jima ba, da ba zan tafi na bar ki ba." Gyaɗa mata kai kawai ta yi tare da lumshe idonta, har yanzu wuyanta bai gama saki ba daga shaƙar da ta sha.