← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 55

Sashe 10

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

..........Kusan a tare Matan gurin suka saki shewa tare da faɗin. "Yau za mu yar da ƙwallon Mangoro mu huta da ƙuda." Innar Ma'u wadda ta bi Inna da kallon tausayi ta sauke numfashi tare da runtse idonta. A ranta tana faɗin, komai zai faru ba za ta taɓa bari Innar Ma'u ta bar gidan nan ba, saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko ta san ba ta da inda zata je idan ta bar nan ɗin, dalili na biyu kuma alƙawarin da ta yiwa Malam mijinsu kafin ya rasu, na taimakon Inna da ba ta kariya a gidan bayan ransa. Fakar idonsu Iya ta yi ta fice daga ɓangaren cikin sauri ta aiki Ma'u ta je ta sanar da mai gari halin da ake ciki. Inna tana cikin ɗaki tana ta harhad'a kayayyakinsu cikin sauri saboda jarabar mitar da Iya ta azalzale ta da ita, A'isha dake kwance wadda duk maganganun da aka yi a cikin kunnanta cikin sanyin murya ta ce. "Inna wai haɗa kayan kike yi? Ina zamu je idan mun bar nan ɗin to? Ko gurin ƴan'uwanmu da kika ce mun muna da su za mu?" Inna ba ta tanka mata ba ta cigaba da abun da take yi, hakan yasa A'isha fashewa da kuka. Inna ta fara kai kayansu tsakar gida saboda cigaba da azalzalar ta da Iya ke yi mata akan ta yi sauri ta zo su tafi, su Hansai na ƙara zuga ta tare da yadawa Inna Habaici, sallamar da suka ji ana kwad'awa yasa su juyawa suna kallon mai sallamar, Malam Garba ne, ɗaya daga cikin bafadan garin. Inna ce kawai ta amsa masa sallamar. Cikin ɗaga murya Malam Garba ya ce. "Mai_gari yana son ganin Asabe da Iya Mari a fada yanzu_yanzu." Bai jira amsar kowa ba ya juya ya fita. Wulwulga idanuwa iya ta fara yi, ganin ba ta ga Innar Ma'u ba ta shiga tafa hannuwa tare da faɗin. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, yanzu Ladidi ƙara ta, ta kai gurin Mai_gari? Idan uwarta ce ai baza ta kai ta ba, to mu je gurin Mai_garin sai me? Bai dai isa yasa na janye abun da na yi niyya ba, ato." Wata k'ak'k'arfar ajiyar zuciya Inna ta sauke lokacin da ta ji sak'on Malam Garba, ko ba komai zuciyarta ta samu nutsuwa akan zullumin tunanin inda za su dosa in sun bar nan. Dama da hijabinta a jikinta, takalmi kawai ta zura bayan ta kamo hannun A'isha ta kulle ɗakinta suka rab'a ta gefen matan gidan suka fice, gaba-d'aya suka raka su da kallon banza zukatansu fal baƙin ciki, domin sun san Mai_gari ba zai bar Iya ta kori su A'isha ba.

Iya ce duƙe gaban Mai_gari sai zazzare ido take tana sauraran nasihar da yake yi mata, Inna na gefenta a zauna kanta a ƙasa ita da A'isha. Bayan Mai_gari ya kai aya Iya ta fashe da kuka ta ce. "Ranka ya daɗe ba wai ban ji abun da ka faɗa mun ba ne, amma ina so a duba abun nan da idon basira, Matar nan fa tunda ta zo cikin garin nan ba mu taɓa ganin wani nata ko da kaza ya zo gurinta ba, haka ita ma ba ta taɓa zuwa gurin wani nata ba, ai kuwa ka san da akwai ayar tambaya, domin duk abun da ya koro bera daga rami to tabbas ya fi ramin zafi. Mu da ma tsoron mu ɗaya ne, kar ta janyo mata abun tirrr a cikin zuri'a." Mai_gari ya jinjina kai ya ce. "Iya Mari tun zuwan matan nan garin nan kuke jifan ta da kalmar Maita, kuma idan ban manta ba Marigayi Malam Yusuf har Sarkin Mayu ya taɓa ɗaukowa akan sanin Mayya ce Asaben ko ba Mayya ba, duk da shi ya san ba Mayyar ba ce, sai dan kawai ku ku tabbatar. Sarkin Mayun kuma ya tabbatar ba Mayyar ba ce, amma duk da haka har yau ba ku daina dangantata da Maitar ba, akan me? Yanzu tsakani da Allah idan ƙaddara ta kai naku wani gurin da ba'a san shi ba aka dinga yi masa abun da kuke yiwa wannan baiwar Allah zaku ji daɗi? Rayuwa ba haka take ba, ɗan_Adam Ubangiji ma da kansa ya daraja shi, bai kamata mu kuma yan'uwansa mu dinga wulak'anta shi ba, wannan ba dai_dai ba ne, ban taɓa zaton abun da kika yiwa wannan baiwar Allah daga gare ki ba Iya mari, da girmanki da hankalinki? Maganar Barin Asabe gida kuwa kar na kuma jin ta, indai ba ita ta so hakan da kanta ba, saboda Malam Isuhu shi ya gina gurin da take zaune, kuma ya ce ya bar mata halak_malak, ko bayan ransa ta cigaba da zama a cikinsa, dan haka kar na ƙara jin makamanciyar wannan maganar, duk wanda ya kuma zan kira a zo a kama shi tun daga Kano, a kulle shi a can a koya masa hankali." Mai_gari ya ƙarasa Maganar cikin kaushin murya. Cikin Iya fa ya kad'a jin ta ji an ce za'a kai mutum a kulle, cikin hanzari ta ce. "Insha Allahu ba za'a kuma ba ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, wannan ɗin ma ɓacin rai ne ya saka." Inna ta share ƙwallar data tarar mata a ido cikin ladabi ta ce. "Godiya nake ranka ya daɗe, Allah ya ƙara girma." Mai_gari ya ce. "Amin Asabe, a cigaba da hak'uri, ita kuma wannan yarinya Allah ya ba ta lafiya." Inna ta amsa da Amin. Daga haka Mai_gari ya sallame su.

Su Inna na gaba Iya na bin su a baya tana mitar da girmanta tsofai_tsofai da ita an saka ta fitowa da hantsin nan, kamar ba ita ta zubar da girman nata ba. Sai tsinewa Inna take yi tare da zagin Mai_gari, dama duk maganganun da ta faɗa kurin kawai take yi, haka take yi kodayaushe, ana zuwa gaban Mai_gari kuma sai ka ji ta shiru kamar ba ita ce mai tijarar ba. Suna shiga gida direct ɓangaren Innar Ma'u ta shiga ta dinga zazzaga mata masifa da bala'i, akan kai ƙarar ta gurin Mai_gari da ta yi. Ita dai ba ta kula ta ba, tunda Allah yasa Mai_gari ya yiwa tufkar hanci shikenan. Bayan Iya ta gama yi mata tijarar ta tafi ta shiga ɓangaren su Inna ta tarar tana mayar da kayan da ta fiffito da shi, hak'uri ta shiga ba ta akan abun da ya faru, Inna ta yi murmushi wanda ya fi kuka ciwo ta ce. "Ni fa duk abun da su Iya suke mun bana ganin laifinsu ko kaɗan, domin da gaskiyar su tunda......" Da sauri Innar Ma'u ta katse ta, ta ce. "Na sha faɗa miki ki dainar faɗar haka, dan ba su san asalinki ba bai kamata su dinga yi miki kage da sharri ba, bayan wulak'anci da tozarci gami da tsangwama da kike fuskanta daga gurinsu, idan ba za su iya mu'amala dake ba sai su daina shiga cikin rayuwarki, ba wai su dinga yi miki irin wannan ɗiban albarkar ba." Inna ta ce. "Haka ne, Allah yasa mu dace." Innar Ma'u ta amsa mata da Amin, zuciyarta cike fal da tausayinta. Lokuta da dama tana son ta yiwa Inna tambayoyi a game da rayuwarta, tana son sanin wacece ita? Mene ne dalilin barowar ta cikin danginta ta zo nan tana rayuwa cikin k'unci da k'untata? Amma ganin duk tsawon shekarun da suka yi tare da Innan ko da wasa ba ta taɓa yi mata magana makamanciyar wannan ba yasa take dannewa ba ta tambayar ta_ta.
Chapter 10 · 0% Book details