← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 55

Sashe 20

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan fitarsa Inna ta rafka tagumi tana tunani, ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba da ta ji Ɗan'juma ne ya yi ƙoƙarin ke ta haddin A'isha, ko kaɗan tunaninta bai taɓa kawo mata Ɗan'juman ne ba. Ta san da Ubangiji ya ba shi nasara akan A'isha shikenan ya ci bulus, domin babu matakin da za'a iya ɗauka a kansa. Duk da kasancewar Sarki adalin Mutum ne kuma yana iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin ya bawa iyalansa tarbiyya ingantacciya, amma shi kansa Ɗan_juman ya gagare shi, domin mahaifiyarsa ba ƙaramin ɓata shi ta yi ba, duk abin da ya yi ita take ɗaure masa gindi, ta shagwab'a shi ba kaɗan ba saboda shi kaɗai ne ɗanta a duniya. Hakan yasa Sarki ya zuba musu ido kawai ya ce indai duniya ce za su gani, tunda ya yi iyakar ƙoƙarinsa akan ganin rayuwar Ɗan_juma ta saitu amma hakan ya gagara, sai dai duk da haka bai fasa bin sa da addu'ar shiriya ba. A'isha ce ta fito daga ɗaki cikin laluban haya ta zauna a tsakar gidan ta ce. "Inna wannan mutumin ya iya magana, maganarsa irin ta ƴan gayu a hankali, me yasa ba ki tambayar mana shi sunansa ba?" Inna ta ce. "Da kin sani ai kin fito kin tambaye shi da kanki, uwar magana kawai, ba ki da lafiyar ma ba za ki bar ni in ji da abun da yake damuna ba sai kin ishe ni da surutu."  Turo baki A'isha ta yi ba ta kuma magana ba, cikin ranta kuwa cewa take yi, 'Dama tana gani ta ga wannan ɗan gayun mai daɗin ƙamshi ya yake.'

Bayan an sauko daga Masallacin Juma'a Sarki ya gama gaggaisawa da Jama'a Matashin nan ya same shi ya zayyane masa duk abun da ya faru jiya Na ƙoƙarin cutar da A'isha da su Ɗan_juma suka yi. Sosai ran Sarki ya ɓaci, cikin takaici ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, wannan Mata Asabe ita da ƴarta suna ganin tashin hankali da taskun rayuwa kala_kala a cikin garin nan, daga wannan sai wannan, ba don Allah ya kawo ka ba UMAR da tuni wannan shashashan yaron sun ɓata mata rayuwar yarinya. Allah ya biya ka bisa wannan ceto da ka yi, shi kuma Ɗan_juma da sauran abokanan shashancin nasa zan ɗauki mataki mai tsauri a kansu Insha Allahu, a yau ba gobe ba." Godiya Umar ya yi masa ya tashi zuciyarsa cike da son sanin abubuwan tashin hankalin da Sarki ya ce suna samun su Inna, ya rasa me yasa zuciyarsa ta damu da al'amarin waɗan nan bayin Allah, daga juya zuwa yau kaɗai tausayinsu ya cika masa zuciya, sai kuma wani abu daban da yake ji a cikin ransa bayan tausayin da bai san mene ba a game da A'isha...........✍️

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*1️⃣1️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_

..........Daga Masallaci direct cikin gida Sarki ya wuce sashen Matarsa ta uku wato mahaifiyar Ɗan_juma. A lokacin Ɗan_juma yana kwance ya yi matashi da cinyarta tana lallab'a shi akan ya ci abinci, shi kuma sai taɓara yake zuba mata. Muryar Sarki suka tsinkaya a kausashe yana faɗin. "Rabi! Rabi! Yaron nan yana ciki?" Dan ɓata fuska Rabi ta yi tana duban da Sarki ta ce. "Ranka ya daɗe lafiya kake mun wannan kiran haka murya a sama?" Sarki ya ce. "Ban sani ba." Sannan ya dubi Ɗan_juma ya ce. "Kai! taso." Tashi zaune Ɗan_juma ya yi yana b'ab'b'ata fuska. Cikin tsawa Sarki ya ce masa. "Ba da kai nake ba ne? Ka zauna kana kallo na." Miƙewa tsaye Rabi ta yi ta ce. "Wai me ya faru ne Yallabai na ga kamar ranka a b'ace? kuma sai magana kake yi cikin hargagi, wato an zigo ka akan Shalele an maka masa wani sharrin ko?" Wani kallo ya wurga mata bai ce komai ba ya tasa Ɗan_juma a gaba suka fice ya bar ta tsaye baki buɗe. Da dogarai guda biyu Sarki ya haɗa Ɗan_juma da su ya ce. "Ka je ka raka su duk inda za'a samu sauran abokanan shashancin naka da kuka yi yunk'urin yiwa Yarinyar mutane fyaɗe jiya." Wani murmushi Ɗan_juma ya yi irin idon't care ɗin nan sannan ya yi gaba, dogaran suka bi shi a baya.
Chapter 20 · 0% Book details