← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 55

Sashe 3

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.........Wata ƙundular baƙar yarinya ce ta yi tsalle ta dire a gaban su A'isha, ta ce. "K'arya kike mu Baba Malam ɗinmu ba shine Babanki ba, ki je can ki nemi Ubanki a wani gurin." Hindu za ta kuma magana Ɗan_Juma ya katse su cikin tsawa da faɗin. "Ubanwa ya ce ku sako mun ƙazamin bakinku da ya jik'u da miyar kuka a cikin maganata?" Tsit su Hindu suka yi suna hararar A'isha ta ƙasan ido tare da jijjige_jijjigen jiki. Wata tsawar Ɗan_Juma ya ƙara daka musu ya ce su b'ace masa daga gani, sum_sum suka juya suka bar wajen. A'isha da har lokacin kuka take yi ta juya ta yi hanyar gida da gudu. Inna tana cikin wankin uniform ɗin A'isha ta gan ta, ta shigo kamar an jefo ta tana gunjin kuka. Kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kanta ta cigaba da abun da take yi. Shigewa ɗaki A'isha ta yi ta faɗa kan gadon ƙarfen dake ɗakin ta ƙara fashewa da kuka. Tun tana ƴar mitsitsiyarta take jin ana jifan su da miyagun kalamai ita da Innarta, tun bata san ma'anar kalaman ba har ta sani ta hanyar tambayar wani malaminsu a makaranta ya yi mata bayani, dan idan zata kwana tana tambayar Inna baza ta taɓa ce mata komai ba akan al'amarin. Bayan Inna ta gama wankin ta zira Hijabinta ta je ta ɗauko ruwan ta dawo. Ɗaki ta shiga dan taso A'isha wadda ke kuka har lokacin. Tana kallon ta, ta ce. "Taso ki yi wankan kar lokaci ya ƙure." Bata ce komai ba ta miƙe tana goge hawayen fuskarta ta fara cire kayan jikinta. Inna ta bi ta da kallo, kamar zata yi magana sai kuma ta fasa. Bayan A'isha ta yi wankan ta wanke bakinta da gawayi ta yi alwala ta yi Sallah ta shirya ta tafi gidan wata mata wadda suke karatun addini a gurin ta. A can ma yara sun so tsokanar A'isha tare da neman ta da faɗa kamar yadda suke mata kodayaushe amma sai Malamar ta tsawatar musu. Bayan an tashi daga karatun Malamar bata bar A'isha ta tafi ba sai da sauran yaran suka jima da tafiya, gudun kar su tsokane ta su yi faɗa a hanya.

Washegari bayan Sallar Asuba A'isha tana zaune a inda ta yi Sallah tana bitar karatun Alkur'anin da aka yi musu jiya kamar yadda ta saba kodayaushe, Inna kuma tana kan Sallaya tana lazimi. A zahiri carbin hannunta take ja, amma a cikin zuciyarta tunani take yi, tunanin abun da zata bawa A'isha ta ci kafin ta tafi makaranta take yi, domin yau ta tashi bata da komai a gidan kuma bata da ko sisin kwabo wanda zata bata ta siyo abun karyawa. Jiya da yamma ma haka ta wuni cikin wannan tunanin da zullumin, sai kuma Ubangiji yasa Innar Ma'u ta aiko mata da rama mai ɗan yawa bayan ta dawo daga unguwar da ta je, ita ta samu ta kwad'anta musu suka ci da daddare ita da A'isha. Ganin gari ya fara haske A'isha ta dubi Inna ta ce. "Inna zan je fa makaranta yau." Dogon numfashi Inna ta sauke ta ce. "Na sani A'isha, me ya faru?" A'isha ta ce. "Na ga baki hura wuta ba ne." Inna ta ce. "Yanzu zan hura, ki share ɗakin kafin na gama." A'isha ta ce. "Toh." Miƙewa Inna ta yi ta cire hijibin jikinta ta fice daga ɗakin. Bayan A'isha ta gama gyaran ɗakin ta fito ta tarar Inna har ta haɗa mata ruwan wanka. Da mamaki ta dubi Inna ta ce, "Inna har kin dafa ruwan zafi?" Inna ta ce. "Zama zan yi in jira ki ai ki gama ƙailularki, gyaran ɗaki kawai kin shafe kusan mintuna talatin." A'isha ta turo baki ta ce. "Kai Inna duk saurin da na yi amma ki ce na dad'e?" Inna ta ce. "Kar ki shiga wankan tsaya zance." Bata kuma cewa komai ba ta shige ɗan ƙaramin bayin nasu. Inna tana zaune ta yi tagumi da hannu bibbiyu cikin rashin sanin mafita, ta san A'isha tana fitowa daga wanka abinci zata fara buƙata. Shawara ta yanke zata je gurin Innar Ma'u ta ari Naira Ashirin ta siyowa A'isha koko kafin ta fito daga wanka. Kafin ta kai ga miƙewa Ma'u ta shigo zagayen nasu bakinta ɗauke da sallama. Inna ta amsa mata, Ma'u ta ce. "Ina kwana Inna." Inna ta ce. "Lafiya ƙalau, mun tashi Ma'u ya Innar taki?" Ma'u ta ce. "Tana nan ƙalau." Tana ajiye kofin robar hannunta da wani ɗan k'ullin leda ta ce. "Gashi in ji Innata wai babu yawa." Inna ta kalli kayan sannan ta kalli Ma'u ta ce. "Kai, Ladidi bata gajiya da abun arzik'i dai, to ki ce mata na gode sosai kin ji Ma'u, Allah ya saka da Alkhairi." Ma'u tana murmushi ta ce. "Indo ce take wanka?" Inna ta ce. "Ita ce." Ma'u ta juya tana faɗin, "Bari na je nima na shirya kar ta riga ni." Inna ta ce. "To Ma'u ki ce mata na gode sosai." Ta ƙarashe zancen tare da sakin ajiyar zuciya tana yin hamdala ga Ubangiji a cikin zuciyarta. Ita kam babu abun da zata ce da Innar Ma'u akan irin taimakon su da take yi sai dai Allah ya saka mata da Alkhairin sa kawai. Kayan ta shiga dubawa ta ga kunun tsamiya ne a cikin kofin, k'ullin ledar kuma fanke ne. Dai-dai nan A'isha ta fito daga wankan, tana duban Inna ta ce. "Inna kamar murya Ma'u na ji da ina Wanka." Inna ta ce. "Ita ce ta shigo." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ba ta shirya ba ko? Salon ni na gama shirina ta makarar da Ni?" Inna ta ce. "Sai ta shirya ma kina nan kina shirita ke baki shirya ɗin ba, ga kunu da fanke nan Innarta ta aiko mana, idan kin biyawa ma'u makaranta sai ki yi mata godiya." A'isha ta yi murmushi ta ce. "Toh Inna, bari na wanke bakina na zo na ci."

Ƙarfe takwas da mintuna su A'isha suka fito daga ɓangaren su Ma'u dan tafiya makaranta. Suna sanye cikin uniform ɗinsu white and blue, wanda ya kasance fess da shi babu datti, duk da babu guga a jikinshi amma bai yamutse ba. Suna tafe A'isha tana ta yiwa Ma'u mitar ta makarar da su. Ma'u ta ce. "Kai Indo, yanzu ma fa idan mun je makarantar nan babu kowa, duk ba'a fara zuwa ba, kullum fa mu muke fara zuwa kin sani." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Wai bana ce miki bana son Indon nan da kike ce mun ba, ni sunana A'isha, ki daina ɓata mun suna, ehe." Ta ƙarashe zancen tana hararar Ma'u. Dariya Ma'u ta yi ta ce. "Ai na faɗa miki kema sai kin daina ce mun Ma'u kin koma ce mun Asma'u sannan nima zan daina ce miki Indo." A'isha ta ce. "To aike haka kowa yake ce miki dama, ni kuwa ke kaɗai kike ce mun Indo, wai Indo? Sai ka ce wata tsohuwa." Dariya kawai Ma'u ta yi bata ce komai ba. Dai_dai nan suka ƙaraso ƙofar gidan Mai_ gari, Ɗan_juma dake tsaye a cikin soron gidan da waya a hannunsa yana latsawa ya fito ya sha gaban su, dama ita yake jira ta zo wucewa. Wani uban tsaki A'isha ta ja ta kama hannun Ma'u da nufin su sauya hanya amma sai ta ji an fizgo hijabinta. Ta juyo a fusace tana ƙoƙarin k'wace hijabinta daga hannun Ɗan_juma ta ce. "Me ne haka?" Ɗan_juma ya ce. "Na lura yarinyar nan kullum ƙara raina ni kike yi saboda na ce ina son ki ko?" Cikin tsiwa A'isha ta ce. "An raina ka ɗin, kuma ni ka sakar mun Hijab ɗina, dan ni ba ƴar iska ba ce da Namiji zai riƙe mun Hijabi." Ɗan_juma yana bin ta da wani shegen kallo ya ce, "Hmm yaro man kaza." Sannan ya yi wani murmushi ya sakar mata Hijabin. Da sauri Ma'u ta ja ta suka yi gaba, A'isha ta juyo ta ce masa. "Kuma Allah ya isa na." Sannan ta juya suka cigaba da tafiya. Murmushi Ɗan_juma ya ƙara saki yana bin bayan ta da kallo tare da lasar leb'ensa na ƙasa, zuciyarsa na ƙara tunzura shi akan mummunan k'udirinsa akan A'isha. A fili ya ce. "Ki jirayi ranar da zan fanshe dukkan wulaqanci da tsiwar da kike mun A'isha, Ni Ɗan_juma kaf cikin garin nan babu wanda ya isa ya taba ni ya zauna lafiya, balle kuma ke mara asali da galihu, wadda ko me na yi miki baki da wanda zai ɗaukar miki matakin komai." Yana gama faɗin haka ya juya ya shige cikin gida still fuskarsa ɗauke da murmurshin da shi kaɗai ya san ma'anarsa...........✍️

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*0️⃣3️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951
Chapter 3 · 0% Book details