← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 55

Sashe 15

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau ta kama ranar Talata, da safe k'anin Innar Ma'u dake Kano ya zo. Bayan sun gama gaisawa da ita sun sha hirar yaushe gamo ya gyara zama ya ce mata. "Yaya ni fa abun da ya kawo ni na zo ɗaukar ku ne ku koma can Kano da zama tunda Allah ya nufa na kammala ginina." Cikin mamaki innar Ma'u ta ce. "Mu koma can kamar ya? Ina kake nufi? Ba dai Kano ba?" Ya ce. "Can mana gidana, sai ku fara shiri jibi za mu wuce tare." Innar Ma'u ta ce. "Haba Muntari, ya za'a yi mu koma gidanka mu ɗora maka nauyi bayan wanda yake kanka? Kuma ita Rakiyan ai kamar zamu takura ta idan muka koma gidanka gaba-d'aya da zama." Muntari ya ce. "Babu wani nauyi Yaya, ni fa na ce ku koma kuma na san zan iya ne, Rukayya kuwa ba ki da matsala da ita, da na faɗa mata ma murna tay ta yi." Shiru kawai Innar Ma'u ta yi ba ta ce komai ba, amma ko kaɗan ba ta so komawarta Kano ta bar garin da aka haife ta a ciki ba, gashi kuma ba ta son barin su Inna, amma saboda kar Muntari ya ga ta gwale shi sai ta amince, ta dinga yi masa godiya tare da tarin addu'oi. Jiki a sanyaye Innar Ma'u ta shiga ta sanar da inna batun tafiyarsu. Inna ta ce. "Jibi_jibin nan kuma? Ikon Allah" Innar Ma'u ta ce. "Wallahi Nima na ga abun ya yi kusa sosai, yaushe na gama zaga ƴan'uwa da abokan arzik'i na yi musu sallama? ga gari na damuna wataran ma sai ruwa ya hana ka fita. Amma ya zan yi tunda Muntari ya dage." Inna ta yi murmushi ta ce. "Ai da gaskiyarsa, ya san in ya tafi baza ki koma da wuri ba, Allah ya kai mu Jibin ya sanya Alkhairi." Innar Ma'u ta ce. "Amin, amma ko kaɗan ban so barinmu garin nan ba ko dan ku Asabe." Inna ta ce. "To ya za'a yi? Haka Allah ya yi, kar ki saka komai a ranki na damuwa saboda ni, Ubangiji yana tare da mu ai." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne kam." Inna ta ce. "Zan shigo anjima mu yi wata magana idan na gama abun da nake yi" innar Ma'u ta ce. "To sai kin zo."......... Kwana biyun nan zuciyoyinsu Inna babu daɗi saboda tashin da su Ma'u za su yi, ita kanta innar Ma'u ta shiga cikin damuwa, ga tunanin halin da za ta bar su Inna ga kuma kewarsu da za ta yi. A'isha ma sosai ta damu saboda rabuwa da Ma'unta, ita kaɗai ce ƙawarta duk cikin garin, idan ta tafi shikenan ba ta da kowa. Ranar Alhamis da safe wanda ya kama ranar tafiyar su Ma'u, Inna tana wankin uniform ɗin A'isha Hansai ta shigo zagayen nasu babu ko sallama, ta tsaya akan Inna cikin izgilanci ta ce. "Yau koma wasu sai kwanan baƙin ciki, wadda aka yi nasarar lashewa kurwa zata bar gari, sai mu ga kuma da wa za'a dinga yin mu'amala yanzu." Inna ta yi murmushi ta ɗago ta kalle ta ba ta ce komai ba. Hansai ta cigaba da yadawa Inna habaici cikin shewa, yau duk matan gidan zuciyarsu fari k'al suke jin ta, a ganinsu tunda innar Ma'u za ta bar gidan watan tagayyarar su Inna ya kama. Har ƙofar gida aka kawo Motar da su Ma'u za su tafi a cikinta, bayan an gama saka kayansu a ciki suna bakin Motar a tsaye matan gida duk sun fito yi musu rakiya. Inna tana tsaye hannunta riƙe da na A'isha wadda ke ta gunjin kuka ita da Ma'u, ita kanta innar dauriya kawai take yi amma yanda take jin zuciyarta kamar ta fashe da kukan, ganin abun take tamkar a mafarki, kamar za'a ce wasa ne su Innar Ma'un sun fasa tafiya. Innar Ma'u ta rungume A'isha tana hawaye ta ce. "Ki yi shiru A'isha ki bar kukan nan haka, kin ga idanunki dama ba lafiya ce da shi ba, ai zamu na zuwa muna ganin ku, kuma za ku na kawo mana ziyara, na bawa Innarki Lambar Muntari, idan kun tashi zuwa sai ta kira shi ya ba ta adreshin inda muke, ki yi hak'uri kin ji." A'isha dai tamkar ƙara zuga ta innar Ma'u ta yi, maimakon ta yi shirun sai ma ƙara volume ɗin kukan ta yi. Janye ta Inna ta yi, ta dubi Innar Ma'u tana murmurshin da ya fi kuka ciwo ta ce. "Allah ya kiyaye hanya ya kai ku lafiya, Na gode sosai da irin taimakon da kika ba ni a zamantakewarmu, Allah ya saka da miki da mafaficin Alkhairin sa, tabbas ke wani bango ce a cikin rayuwarmu." Ba ta jira cewar Innar Ma'un ba saboda wani kuka dake neman kufce mata ta shafa kan Ma'u ta ce. "To Asma'u, Allah ya tsare sai mun zo ko kuma ku kun zo." Ma'u ta riƙe Inna ta ce. "Ni na fasa tafiyar anan zan zauna tare da A'ishata, ni ba zan iya tafiya in bar ta ba." Inna ta ce. "Haba Asma'u, kar ki ce haka kin ji yarinyar kirki na, ki yi hak'uri." Ma'u ta saki Inna ta rungume A'isha suka fashe da kuka mai ban tausayi, hakan ya karya zuciyar innar Ma'u ta fara hawaye sosai ita ma, abun tausayi. Sabo da shak'uwa ba k'arya ba ne, tunda su A'isha suka taso tare suke yin komai da Ma'u, yau rana tsaka kuma Ubangiji ya raba su, abun da babu wanda ya yi tunanin faruwarsa nan kusa. Sosai suka bawa wasu daga cikin mutanen gari tausayi, shi kanshi Muntari dake tsaye yana kallon su sai da ya ji kamar ya fasa tafiya da su Ma'un, Malam ƙarami kuwa Mutumin Inna shi ma sai kuka yake yi. Dauriyar Inna ta ƙare, hawaye masu ɗumi ne suka shiga kwaranyowa daga cikin idonta, cikin matuƙar sanyin jiki ta d'agawa su Inna hannu sannan ta ɗaga ƙafafuwanta daƙyar ta yi cikin gida da sauri. Matan gidan suka bi ta da kallo suna sakin murmurshin mugunta. Daƙyar aka iya raba Ma'u da A'isha, ƴar Innar Ma'u ta shigar da A'isha gida Ma'u kuma aka tusa ta cikin Mota. Kuka sosai A'isha ta yi a yau, ko makaranta ba ta je ba, sai bayan Azhar bayan Inna ta saka ta, ta yi Sallah bacci ya ɗauke ta. Ita kanta Inna ta ci kukanta ta gode Allah. Sai yamma A'isha ta farka daga baccin, ta tashi da ciwon kai saboda kukan da ta sha. Tana farkawa abun da ta fara cewa shine. "Shikenan su Ma'u sun tafi sun bar mu, yanzu ba mu da kowa, ba ni da mai kama hannuna mu je makaranta, ba ni da mai yi mun rubutu." Inna ta ce. "Mu na da Allah A'isha, kuma shi zai yi mana maganin komai ya ba mu yanda za mu yi."

Sosai kewar su Ma'u take damun su Inna, gashi ita ba waya ba bare ta kira lambar Muntari su yi magana da su ko sa ɗan ji daɗi. Duniyar duk sai ta yi musu wani iri babu daɗi. Gaba-d'aya A'isha ta daina walwala, komai cikin sanyin jiki take yin sa, ta rage yawan magana, kamar ba ita ce a daa idan ta fara yiwa Inna surutu sai ta ce ta rufe mata baki ba. Satin da su Ma'u suka tafi gaba-d'aya ƙin zuwa makaranta ta yi, Inna ba ta takura mata ba akan hakan ta bar ta, ta huta. Ranar Lahadi da daddare suna cin tuwon masarar da Inna ta yi musu Inna ta cewa A'isha. "A'isha ki daure gobe ki koma makaranta, dan babu Ma'u kuma sai ki daina karatu? Ko ba kya son ki zama likitar ne yanzu?" A'isha ta ɓata fuska ta ce. "To Inna da wa za mu dinga tafiya tare?" Inna ta ce. "Ni zan dinga kai ki in na ɗauko ki." A'isha ta ce. "To wa zai dinga mun rubutu? Idan an fita Sallah wa zai na kama hannuna mu je mu yi?" Shiru Inna ta yi tana kallon A'isha na wasu sakanni, daga baya ta ce. "Mu je makarantar dai sai mu ji yanda za'a yi." Washegari ba dan A'isha ta so ba ta shirya suka tafi Makarantar tare da Inna. Allah ya haɗa su da wata Malama mai kirki mai suna Malama Hajara, Inna ta yi mata bayanin abun da yake tafe da ita, ta kwantarwa da Inna hankali ta ce, insha Allahu zata na kula da A'isha yanda ya kamata, ko da ranar da ba za ta zo makarantar ba zata yi waya ta faɗa a kula da A'ishan. Inna ta yi mata godiya sosai sannan ta dawo gida.
Chapter 15 · 0% Book details