← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 55

Sashe 47

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Asibitin Makkah suka je, aka yi wa A'isha gwaje-gwaje a idon bayan an buɗe mata File. 1 week aka ba su, su dawo don karɓar sakamakon gwajin. Daga nan gidan Aunty Ruƙayya suka zarce dake gadon ƙaya, Ummi ta bar ta a can, ta ce idan ta dawo daga school za ta biyo ta ɗauke ta. Sai yamma Ummi ta baro school a gajiye, hakan ya sa ta wuce gida tun da ya fi kusa. A Polytechnic ta matan fada take lecturing, department of Pharmacy. Su kuma suna zaune a unguwar Railway ne. Tana ƙoƙarin shiga wanka Khalifa ya shigo ɗakin, zama ya yi a gefen gado ya ce. "Sai yanzu kika dawo? Na ji da muka yi waya kamar kina hanya." Ummi ta ce. "Eh yanzu na shigo, dama kiran da na yi maka Nana za ka je ka ɗauko a gidan Ruƙayya, na gaji sosai ba zan iya driving har Gadon ƙaya ba, kuma zan yi girki anjima." Khalifa ya ce. "Okay, amma gaskiya Ummi ya kamata ki ƙara samo mai aiki, aikin gidan nan ya miki yawa ke kaɗai, ga shi ke ba zama kike ba." Ummi ta ce. "Zan saka a nemo mini ko dan Nana ta samu mai kula da ita idan bana nan, ba na son yara ne wanda sai an shaƙu su yi aure, har yanzu ban daina kewar Lami ba, shi ya sa ko zan kuma mai aiki na fi son dattijuwa." Khalifa ya ce. "Gaskiya kam, bari na je na ɗauko ta kar Magriba ta yi, Kin ji su Yaya jibi za su dawo ko?" Ummi ta ce. "Ya faɗa mini, ɗazu da muka fita Abbanku yake ƙara sanar mini, Allah ya kai mu ya kawo su lafiya." Miƙewa Khalifa ya yi ya ce. "Amin, na tafi." Ummi ta ce. "Allah ya kiyaye ya tsare, sai kun dawo." Ya amsa da Amin tare da ficewa.

A'isha tana parlour a zaune ita kaɗai Khalifa ya shigo. Juyar da kanta ta yi inda ta ji motsi, yadda ta ware daradaran idanunta ba za ka taɓa cewa makauniya ba ce. Ƙura mata ido ya yi cikin faɗuwar gaban da bai san dalilin ta ba. A hankali ya taka ya ƙarasa cikin parlour'n tare da yin sallama. Amsa masa ta yi cikin murmurshin jin daɗin zuwan shi.
"Indodo." Ya faɗa cikin tsokana. Murmushi ta ƙara yi tare da faɗin. "Ina yini?" Yana zama a kusa da ita ya ce. "Lafiya ƙalau, ya na gan ki ke kaɗai, ina Aunty da su Ihsan?"
"Suna ciki." Ta ba shi amsa cikin sanyin murya. Zai kuma magana Aunty Ruƙayya ta fito daga kitchen, da mamaki ta ce. "A'a, Babana yaushe ka zo?"
"Yanzun nan, Ina yini?"
"Lafiya ƙalau, ya aiki?"
"Alhamdulillah."
"Ka zo tafiya da ita ne?"
Ya ce. "Eh, Ummi ce ta ce na zo na ɗauko ta." Aunty Ruƙayya ta ce. "Ai na ɗauka za ta bar ta kwanar mana biyu a nan, Kodayake gobe Friday ba jimawa za ta yi ba a school." Khalifa ya ce. "Ai ummi ba za ta iya barin wannan tsohuwar ta kwana a wani gurin ba, ji take da ita kamar ɗanyen ƙwai." Aunty Ruƙayya ta ce. "Ta ma fi ƙwai ko Mamana?"
Murmushi kawai A'isha ta yi ba ta ce komai ba. Daidai lokacin Ihsan ta fito daga É—aki, da fara'a sosai ta dubi Khalifa ta ce. "Mun yi fushi Ya Khalifa gaskiya."
"Me kuma na yi?" Ya tambaya cikin marairaicewa. Ta ce. "Yaushe rabon ka da gidan nan, sai yau da ƴar gidanku ta zo muka gan ka." Ya ce. "A yi haƙuri tuba nake." Dariya ta yi tare da gaishe shi. Ko 10 minutes ba su ƙara ba Khalifa ya ce za su tafi kar dare ya yi, kayan cosmetics da turaruka Aunty Ruƙayya ta ba wa A'isha, ta yi mata godiya sannan Ihsan ta kama hannunta suka fita ta raka su bakin Motor. Sai da Khalifa ya tsaya a hanya ya yi wa A'isha shopping kafin su je gida.

Hankalin Mommy ya yi kan shirye-shiryen tarɓar ɗanta da Matarsa wadda ta kasance ƴa ga Kaltum ƙanwarta. Shi ya sa ta ajiye batun A'isha a gefe ba don ta haƙura ba. Yadda ake toye-toye da abubuwa sai ka yi zaton shugaban ƙasa ne zai dawo. Kasancewar shi ma'abocin tsafta da son ta ya sa tun saura kwana biyu su sauka masu aiki suke bautar gyaran part ɗinsa dake gidan, tamkar za su sauya masa halitta saboda ƙalƙala.

Yau tun safe Ihsan ta zo da yake weekend ne babu school, A'isha ta ji daɗin zuwan ta sosai, saboda ita ma kamar su Ummi take babu ruwanta, ga faran-faran da son jama'a. Bayan Sallar la'asar Ummi tana bedroom tana azkar, Khalifa kuma ya tafi airport ɗauko su Safwan. Hannun A'isha Ihsan ta kama ta ce. "Zo mu fita compound mu shaƙata." A'isha ta ce. "Wacce irin shaƙatawa kuma?"
"Ke dai ki zo mu je." Ihsan ta faɗa tare da jan ta suka fice. Suna zaune a kan kujerun roba wayar Ihsan ta yi ringing, dubawa ta yi ta miƙe ta ce. "Bari na ɗan leƙa waje na dawo, wani guy ne ya zo za mu gaisa, yanzu zan dawo." Gyaɗa mata kai kawai Aisha ta yi, ɗaga kiran ta yi tare da barin wajen.

Buɗe makeken gate ɗin gidan tare da shigowar wata rantsatstsiyar mota, ya saka Mommy dake tsaye a gaban window sakin murmushin farinciki dawowar ɗanta Namiji tilo a duniya, wanda take gani da jin duk duniya tamkar babu ɗan da ya kai shi. Sakin labule ta yi ta koma ta zauna tana jiran shigowar shi. Bayan Khalifa ya yi parking Safwan ya sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa ya buɗe. A hankali ya buɗe motar ya fito yana kallon harabar gidansu da ya shafe watanni ba a cikinsa ba. After some seconds ya buɗe bayan Motar tare da ja baya. Wata farar matashiyar mace siririya ce ta fito tana yamutsa fuska tare da kare fuskarta da hannunta. Yanayin shigar jikinta ba za ka ce matar aure ba ce idan ba faɗa maka aka yi ba. Kanta ta ɗora a kan kafaɗarsa, cikin marairaicewa ta ce. "I'm so tired mine." Gefen fuskarta ya shafa cikin kulawa ya ce. "Sorry." A taƙaice. Ba ta ce komai ba ta bar jikinsa jin wayarta dake hannunta na ringing. Picking ta yi tare da nuna masa hanya alamun ya yi gaba za ta taho. Bai ce komai ba ya juya ya fara tafiya cikin nutsuwa, a ransa yana mamakin daga saukar su har ta saka sim ɗinta na Nigeria an fara kiran ta. Khalifa dake kallon su ya taɓe baki tare da buɗe murfin motar ya fito shi ma. A'isha ta fara gajiya da jiran Ihsan, ga iska sai ƙadawa take sanyin la'asar yana ratsa ta. Ganin iskar na takura ta ya sa ta miƙe ta fara tafiya a hankali cikin laluben hanya. Ba zato ta ji ta yi karo da wani abu, taga-taga ta yi za ta faɗi ya yi saurin ruƙo ta yana yatsina fuska, ko kaɗan bai lura da mutum yana tahowa ba saboda ba ta gabansa take ba ta gefen shi take. Ita kuwa Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi jin ba ta kai ƙasa ba, siririn tsaki ya ja ya zare ta daga jikinsa tare da yin gaba ba tare da kuma kallon inda take ba. Tsayawa ta yi cak ta kasa cigaba da tafiya, saboda tsoron kar ta kuma karo da wani abun. Mamakin wanda suka yi karo da shi ne ya cika mata zuciya, su yi karo da mutum amma ya ƙi magana sai ka ce kurma. Ta san ba Ya Khalifa ba ne ko Abba, don in su ne ba za su taɓa wucewa su bar ta ba, kuma ƙamshin da ta ji a jikin mutumin ba irin nasu ba ne, ba ta taɓa jin irin ƙamshin ba tunda ta zo gidan sai yau. Lumshe ido ta yi saboda yadda daɗin ƙamshin yake ratsa ta, duk da ya bar gurin amma ƙamshinsa bai daina ratsa ƙofofin hancinta ba. Jin ƙarar taku ya sa ta sakin ajiyar zuciya, a tunaninta Ihsan ce ta dawo, tana shirin yin magana ta ji an wanke ta da wani gigitaccen mari, ba ta gama fita daga ɗimuwar marin ba ta ji an damƙi wuyanta tare da lailayo mata narkekiyar ashariya gami da faɗin. "Dabbar ina ce ke da za ki bari ki yi karo da mijina har ki gogi jikinsa? wallahi sai na kashe ki tunda kika haɗa jiki da mijina!" Ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji.........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖

*_Zeey Kumurya_*

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*2️⃣8️⃣*
Chapter 47 · 0% Book details