Sashe 52
Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin daren jiya Allah ya yi wa wani maƙocinsu rasuwa, hakan ya sa Abba da sassafe ya kira Ummi ya ce mata idan sun shirya driver zai kai su asibitin, shi zai zauna a yi jana'iza da shi. Lokacin da suke wayar Mommy tana kwance a gadonsa, da yake ita ce da girki. Duk da faɗan da suka yi kaca-kaca ba ta fasa zuwa part ɗinsa ta kwana ba. Ba tare da ta ce masa komai ba ta tashi ta fita. Jikinta har rawa yake gurin nemo lambar Kaltum ta kira ta. Sai da ta yi mata kira uku sannan ta ɗaga cikin muryar bacci. A zaƙe Mommy ta ce. "Ina kika shiga ne haka?" Khaltum ta ce. "Bacci nake, me ya faru kike mini wannan kiran da sassafe?" Numfashi Mommy ta sauke ta ce. "Wata dama na ga mun samu akan barin yarinyar can daga gidan nan, za su je asibiti ne kuma Alhaji ya ce driver ya kai su, shi ne nake ganin ko mu haɗa baki da drivern ne ya ɓatar da ita?" Khaltum ta ce. "Wannan shawara ce mai kyau gaskiya, abin da za a yi ki fara kiran direban ku yi magana ki ce masa za ki ba shi lada mai tsoka, idan suna tafiya ya bi ta cikin layika ya ce mata saboda go slow, ni kuma zan turo waɗanda za su tare su, su sace yarinyar. Ki ce ya faɗa miki irin motar da za su hau da numbern ta"
Mommy ta ce. "Ta ina su waÉ—anda za ki turo É—in za su san inda suke?" Khaltum ta ce. "Wanne asibitin za su je?" Mommy ta ce. "Na ji da Alhaji ya kira direban ya ce masa asibitin Makka dake b.u.k road." Khaltum ta ce. "Okay, za su jira shi a layin, zan turo miki address É—in inda suka ce mini suke, sai ki faÉ—a masa ya bi ta gurin, zan kira su yanzu, na san ina faÉ—a musu za su tafi." Cikin matsanancin jin daÉ—i Mommy ta ce. "Da kyau khaltum, na rasa ma me zan ce miki saboda farinciki, kin gama mini komai da wannan tunanin naki, yarinyar nan mai siffar mayu ita kaÉ—ai ce damuwata a yanzu." Khaltum ta ce. "Duk abin da zai saka ki farinciki a shirye nake na yi shi, ki kira direban tunda kin san waye, ni ma zan kira su yanzu." Mommy ta ce. "Shikenan sai kin ji ni."
Suna gama wayar Mommy ta aika aka kira mata ɗaya daga cikin direbobin gidan mai suna Buhari wanda Abba ya kira ya ce zai kai su A'isha Asibitin, bayanin aikin da take so ya mata ta faɗa masa tare da alƙawarin 500k cash bayan komai ya kammala. Da murna ya amince, don shi bai ga wahalar aikin ba, don dai bi ta cikin layika kawai ko a 100k zai yi balle 500k. kafin 7:30 su Mommy sun gama tsara komai yadda suke so.
Ummi tana kulle Bedroom ɗinta ta dubi A'isha dake kiciniyar saka hijabi ta ce. "Ki yi abu da jiki mana Nana, mun kusa yin latti fa, har takwas saura quarter fa yanzu. A'isha da take jin duk jikinta a sanyaye ba tare da ta san dalili ba ta ce. "Na rasa fuskar hijab ɗin ne." Ummi ta ce. "Sai fa da na saita miki zirawa kawai za ki yi amma kika tsaya wasa." Ta ƙarashe maganar tare karɓar hijab ɗin ta saka mata tare da kama hannunta suka nufi parking space. Buhari yana hango su ya washe baki tare da zira wayarsa da yake ƙara duba address ɗin inda za su haɗu da wanda za su ɗauke A'isha ya ce. "Sannu da fitowa Hajiya." Da fara'a Mommy ta ce. "Yawwa, an tashi lafiya?"
"Lafiya Æ™alau" ya faÉ—a tare fitowa daga motar da nufin ya buÉ—e musu. Dakatar da shi Ummi ta yi da faÉ—in. "Bar shi Buhari." Risunawa ya yi cikin girmamawa ya ce. "Da kin bari na buÉ—e miki ranki ya daÉ—e." Kafin ya gama rufe baki har Ummi ta buÉ—e motar ta zira A'isha. Har za ta shiga sai kuma tuna ta ce masa. "Yawwa Buhari, idan mun dawo ni zan sauka a matan fada, ita kuma ka zarto da ita ka kai ta gidan Hajiya Zainab, nan maÆ™wabtanmu kusa da gidan da aka yi rasuwa. Ka ce mata in jini" Amsa mata ya yi tare da buÉ—e mazaunin direba ya shiga..........âœï¸
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*3ï¸âƒ£1ï¸âƒ£*
A hankali ya buɗe murfin Motarsa ya fito daga mazaunin direba. Ummi na ƙoƙarin rufe motar da suke ciki ta ji sassanyar muryarsa yana faɗin. "Ummi."
Dakatawa ta yi ganin ya nufo su, da fara'a ta ce. "Safwan, fita za ka yi ne?" A ladabce ya ce. "A'a, na É—an fita ne ban jima da shigowa gidan ba, na zauna a cikin mota ne ina duba abu a waya." A gaggauce Ummi ta ce. "Ayya, mu ma nan asibitin za mu je yanzu, mun ma yi latti sosai." Yana gyara siririn white glass É—in dake fuskarsa ya ce. "Wanne asibiti?"
"Makka."
ÆŠan jim ya yi kamar mai nazari sannan ya ce. "Ki fito kawai na kai ku Ummi."
"A'a Safwan kar ka tashi kanka tsaye, ga Buhari nan zai kai mu, may be kana da wani uzurin kar na tsayar da kai."
"Babu komai Ummi, ku zo kawai mu je." Ya yi maganar tare da juyawa ya koma gurin motarsa.
Buhari dake sauraren su ya ji tamkar ya fasa ihu, addu'a ya shiga yi a ransa Allah ya sa kar Ummi ta amince. A'isha da ta yi lamo a jikin kujera tun lokacin da ta ji muryar Safwan ta sauke numfashi jin Ummi ta kama hannunta ta fito da ita. Cikin rawar baki Buhari ya ce. "Hajiya ku koma mana na kai ku, kar a wahalar da ƙaramin Alhaji, kin san bai fiya san tuƙi da kansa ba." Ummi ta ce. "Mun riga mun fito, kuma ai shi ya ga zai iya." Bin bayansu ya yi da kallo kamar mai shirin fashewa da kuka, takaici da baƙinciki suka hana shi ya ce musu Allah ya kiyaye kamar yadda suka saba kodayaushe idan sun ga wani a gidan zai fita.
Baya Ummi ta buɗe ta saka A'isha ita kuma ta shiga gaba. Buhari yana kallon su suka fice, ji yake kamar ya ruga da gudu ya je ya tsayar da Safwan ya roƙe shi ya bar shi ya kai su A'isha, 500k ɗin da aka masa alƙawari kawai yake tunani. Ya ga samu ya ga rashi. Sai a lokacin tunanin sanar da Mommy ya zo cikin kwanyarsa, cikin sauri ya rufe motar ya juya ya nufi part ɗinta.
Tana zaune a kan lallusar carpet na alfarma da ya kusa mamaye tsakiyar ɗakin tana karyawa Buhari ya fara knocking. Tsaki ta ja tare da faɗin. "Wannan daga ji wani matsiyacin ɗan ƙauyen ne, ai ta buga ƙofa ba jira kamar wanda aka yi wa sata." Ta ƙara jan tsaki sannan ta ɗaga murya ta kira Murja dake kitchen. Da sauri ta fito tana goge hannunta a jikin zaninta.
"Je ki ga waye yake mini wannan bugun haukan da farar safiyar nan." Ta faɗa a lalace. Amsa mata Murja ta yi ta nufi ƙofa. Baby dake saukowa daga kan steps cikin shirin tafiya school ta ja tsaki cikin yamutsa fuska ta ce. "Wai wanne mahaukacin ne a nan? An taho ana buɗewa amma ya ƙi daina cika wa mutune kunne." Rufe bakinta ya yi daidai da faɗowar Buhari parlour'n kamar wanda aka ingizo.
"Malam lafiya za ka shigo mana har cikin parlour ba tare da neman izini ba?" Baby ta faɗa a wulaƙance cikin daka tsawa tana jifan shi da wani shegen kallo. Ƙasa ya yi da kansa a ladabce ya ce. "Gurin Hajiya na zo." Mommy da take masa kallo mai cike da tarin tambayoyi ta ce. "Na san da zuwansa, bar shi ya ƙaraso." Cikin mamakin yadda ta yi magana ba hargagi kamar yadda ta saba yi wa ma'aikatan gidan Baby da Murja ke kallon ta, don hakan baƙon abu ne a gurinsu. Fita Baby ta yi bayan ta mata sallama, a ranta tana tambayar kanta abin da zai haɗa Mommy da Buhari. Murja ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta koma kitchen ta cigaba da abin da take.
"Ina sauraren ka Buhari, me ya dawo da kai?" Mommy ta faÉ—a cikin son jin abin da ke tafe da shi.
Numfashi ya sauke ya ce. "Ranki ya daɗe an samu matsala, don Alhaji ƙarami ne ya tafi ya kai su asibitin." Cikin rashin fahimta ta ce. "Ban fahimci me kake nufi ba, wanne Alhajin ƙaramin?"
"Na ki Hajiya." Buhari ya faÉ—a tare da ba ta labarin yadda aka yi.
A zabure Mommy ta miƙe ta wanka masa mari a kuncinsa dama da hagu. Dafewa ya yi cikin sauri tare da kallon ta, cikin masifa ta ce. "Wanne irin mara lissafi da hankali ne kai? Tun lokacin da ya zo yana musu maganar ba ka kira ni ba ko da a waya ne sai yanzu bayan sun tafi?" Ƙasa ya yi da kansa tare da yin ɗurƙuso kamar mai shirin yi mata sujjada ya ce. "Allah ya huci zuciyarki Hajjaju makkatu, ban yi tunanin za su shiga motar tasa ba ne." Jijjiga kai ta yi tana jin kamar abincin da ta ci zai dawo mata ta kai saboda tashin hankali, baƙicikinta biyu ne, wargazewar da shirinsu ya yi da kuma kai su Ummi asibiti da Safwan ya yafi. Rasa ma abin cewa ta yi saboda tsananin ɓacin rai. Juyawa ta yi ba tare da ta kuma magana ba ta nufi gurin wayarta don kiran Safwan ta sanar masa ya juye su Ummi ko a tsakiyar titi ne ya dawo gida. Ganin haka ya saka Buhari tashi ya fice hannunsa da dafe da kuncisa. A ransa yana Allah wadai da rashin wadatar zuci da kwaɗayi, don su suka janyo masa shan wannan tagwayen marukan a gurin matar da ba ta fi sa'arsa ba. Ga shi ya yi ba wan ba ƙanin.