← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 55

Sashe 11

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana biyu kamar yadda mai magani ya ce Inna ta cigaba da sakawa A'isha maganin, amma idon bai buɗe ba. Hankalin Inna fa ya yi matuƙar tashi, ta saka A'isha a gaba tana kuka mai ban tausayi. Innar Ma'u ta dinga tausar ta tana ce mata, watak'ila ciwon idon A'ishan bana maganin gida ba ne na asibiti ne, idan Allah ya taimaka ana kai ta asibitin sai ta ga an dace, da wannan kalaman zuciyar Inna ta ɗan yi sanyi. A'isha ma ta damu ba kaɗan ba, domin rashin gani ba ƙaramin jarabta ba ce, dan ma wani ikon Allah sai Ubangiji ya ɗoro mata hak'uri akan makantar da ta same ta lokaci ɗaya. Amma duk da haka kodayaushe cikin tambayar Inna take yaushe idonta zai buɗe? Ita dai a kai ta asibiti, wani lokacin har da kuka take yi. Washegari Monday tun sassafe Inna suka shirya suka tafi asibitin Rano ita da A'isha. Tana zuwa suka yanki kati sannan suka yi zaman jiran a kira su dan ganin likita. Sai wajen ƙarfe goma aka kira su, Inna ta kama hannun A'isha suka shiga office ɗin likitan. Bayan sun gaisa Inna ta yi masa sannu da aiki ya tambaye su abun da yake tafe da su. Inna ta yi masa bayanin duk abun da ya samu A'isha, shiru ya yi na wasu ƴan sakanni, da alama jinjina al'amarin yake yi a cikin ransa. Cikin nuna damuwa ya ce. "Ya Subhanallahi, zazzaɓin mai zafi ta yi ne sosai?" Inna ta ce. "Eh gaskiya ta ji jiki." Likitan ya jinjina kai sannan ta taso ya zo inda suke zaune ya dudduba jikin Aisha. Yana yi yana yi mata tambayoyi tana ba shi amsa, sosai yarinyar ta ba shi tausayi, ƴar ƙaramarta da ita a ce ta rasa ganin ta, duk da dai ana haifar waɗanda ba sa ganin ma, amma nata sai ya fi zama abun damuwa tunda ita already ta san daɗin ganin. Bayan ya koma ya zauna ya dubi Inna ya ce. "Baaba a gaskiya wannan matsalar ba za mu iya magance muku ita a wannan asibitin ba, kasancewar ba mu da k'wararrun likitocin ido, ɗan ciwon ido dai haka da ake fama da shi ko jan ido wannan duk mu na iya bayar da maganinsa, amma idan abun ya girmama, ko ciwon idon da dole sai an yi masa aiki to fa sai dai mu tura mutum can Kano ya je a yi masa, dan haka yanzu ke ma sai dai mu tura ki can asibitin Makkah." Da sauri Iya ta ce. "Asibitin Makkah kuma likita?" Likitan ya yi murmushi ganin Yanda Inna ta yi, ya ce. "Ba wai garin Makkah na cikin ƙasar Saudiyya ba, a'a, wani asibiti dake nan cikin jiharmu Kano mai wannan sunan, to insha Allahu matuƙar kun je can za'a dace." Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Amma asibitin na kuɗi ne ko na Gwamnati?" Likita ya ce. "Private hospital ne, na kuɗi." Inna ta jinjina kai cikin damuwa ta ce. "A asibitin gwamnatin shi ba za a iya duba mata idon ba?" Likita ya ce. "Za'a iya, har aikin ma idan ta kama duk za'a iya yi mata, amma maganar gaskiya asibitin Makkah ya fi, idan da hali ku je can ɗin." Inna ta goge wani gumi da yake tsatstsafo mata a goshi ta ce. "To shikenan likita, na gode sosai Allah ya saka da Alkhairi, insha Allahu sai a je can ɗin." Likita ya ce. "To ba damuwa, Allah yasa a dace." Ya kalli A'isha ya ce. "Sannu kin ji, Allah ya ba ki lafiya." Suka amsa da Amin sannan Inna ta yi masa sallama suka fito. Bayan sun fito daga asibitin A'isha ta cewa Inna. "Inna ba zan ƙara gani ba ko? Shikenan na daina ganin ku na daina ganin komai da kowa?" Inna ta shafi kanta ta ce. "Zaki cigaba da gani insha Allahu A'isha, ke dai ki yi ta addu'a, kar ki gaza kin ji?" A'isha ta ce. "Toh."

Hankalin Inna a tashe suka dawo gida, babbar damuwarta rashin kuɗi da rashin hanyar samun sa, domin ta san maganar zuwa asibitin Kano dole sai ta tanadi kuɗi masu kauri, musamman da likitan ya sako maganar aikin ido, ta san kuɗin aiki ba ƙaramin kuɗi ba ne, ita kam zata iya cewa ba ta taɓa riskar kanta a cikin tashin hankali irin wannan ba, wani irin tausayin A'isha ne yake ƙara mamaye mata zuciya game da wannan ƙaddarar da Ubangiji ya ɗoro mata, sai dai ba ta ƙasa a gwiwa gurin kaiwa Ubangiji kukanta a kodayaushe akan ya yayewa A'isha wannan makanta. Bayan ta gama zayyanewa innar Ma'u abun da ya faru a asibitin ta ƙara da cewa. "Babban tashin hankalina inda zan samu kuɗin da zan kai yarinyar nan Kano a duba ta, mu da ko abun da za mu ci ma gagarar mu yake yi." Innar Ma'u ta sauke numfashi ta ce. "Ubangiji shine zai kawo mana mafita Asabe, insha Allahu Allah zai warware." Inna ta ce. "Ni yanzu sana'ar da zan kama nake tunani, na rasa me zan siyar a garin nan wanda zan dinga samun k'wandala da ficika." Innar Ma'u ta ce. "Tun kwanaki nake son na yi miki magana akan aikin abincin sadakar da muke yi a gidan Hajiya Talatu duk ranar juma'a, wannan fargabar ciwon A'ishan da muke ciki ne yasa na sha'afa. Ɗaya daga cikin wanda muke yin aikin tare ce ɗanta ya ɗauke ta ya mayar da ita can Kano gidansa, to kuma har yanzu ba'a samu madadinta ba, zan yiwa Hajiyar magana idan mun je wannan satin, idan Allah ya saka da rabonki sai ki maye gurbin waccan ɗin, aikin 500 ne kullum kuna gamawa za'a sallame ku, sannan kuma za'a baku abinci sosai wanda zai ishe ku, ku ci daga rana har dare." Cikin jin daɗi Inna ta ce. "Amma na gode sosai Ladidi, Allah ya saka da Alkhairi yasa ta ɗauke ni." Innar Ma'u ta ce. "Insha Allahu zata ɗauke ki, dan ba ta da matsala matar, ga ta da ihsani." Inna ta ce, "Allah yasa a dace." Innar Ma'u ta ce, "Amin Amin, ga wata shawara kuma, zan cewa mutane ina yin Nik'an kayan miya namu na gargajiya na dutse da muke yi, idan an kawo mun sai in baki kina yi ki karb'i kuɗin kya rage wasu abubuwan da shi. Tunda idan ke kika ce kina yi ba za'a na kawo miki ba." Inna ta ce. "Na gode, na gode sosai Ladidi, Ubangiji ya taimake ki kamar yadda kike taimako na, ba dan dake ba a cikin gidan nan da ban san yanda zan yi ba." Innar Ma'u ta ce. "Kin wuce haka a gurina Asabe, yanda nake jin ki a cikin zuciyata tamkar ƴar'uwata ta jini, dan haka babu godiya a tsakaninmu, fatanmu kawai Ubangiji ya dafa mana akan dukkan al'amuran rayuwarmu." Inna ta ce. "Amin."

Da yamma Ɗan_juma suna zaune akan wani dakali ɗan nesa da gidansu shi da wasu abokanansa guda biyu suna hira sai ga wani abokin nasu wanda gidansu yake jikin nasu A'isha shi ma ya zo. Bayan sun gaisa ya dubi Ɗan_juma ya ce. "Ɗan_juma ɗan Sarki jikan Sarki kuma Sarkin gobe da yardar Allah, yau ina tafe da wani labari mai daɗin gaske." Ɗan_juma ya yi murmurshin jin daɗin kirakin da Hamza ya yi masa ya ce. "Shaƙa mun cikin gaggawa, ni kuma in shaƙa maka tukuici mai nauyin gaske." Hamza ya ce. "Labari ne akan Yarinyar can daka ƙwallafa rai a kanta, yau kwana huɗu kenan da wayar garin da aka yi ba ta gani, a tak'aice dai ta zama marainiya." Cikin mamaki Ɗan_juma ya ce. "Kar dai ka ce mun A'isha?" Hamza ya ce. "Ita fa." Wani yalwataccen murmushi Ɗan_juma ya saki ya ce. "Kaii, amma na ji daɗin wannan labari Hamzeze, saboda zai samar mun da hanya mafi sauƙi ta cikar burina akan A'isha, ka ga watarana idan uwar ta_ta ta tafi yawon nemo musu na cin ƙanzo sai mu zagaya mu farmata, mu yi mu gama mu ƙara mai ba tare da ta san mu ba ne, tunda ba ta gani balle ta gane su waye. Sakamakon wannan labari da ka kawo mun Hamza, kai ne na biyu a yin wannan harka bayan na gama." Hamza ya fashe da dariya suka tafa shi da Ɗan_juma wanda shi ma yake dariyar, sauran abokan nasa su ma suka taya su, domin sun san da su za'a yi wannan harkar...........✍️

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*0️⃣7️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
Chapter 11 · 0% Book details