← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 55

Sashe 26

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali A'isha ta ɗago kanta ta ce. "Ina kwana?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?" Ta ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah." ƙarasawa inda take ya yi ya kama hannunta ya ce. "Haka kike da gashi Humairah?" Rufe fuskarta ta yi da hannunta tana murmurshi ƙasa ƙasa ba ta ce komai ba. Ya ce. "A ina ake saloon a garin nan mu je a yi miki? Na san idan aka yi gashin naki zai ƙara kyau." A'isha ta ce. "Mene shi ɗin?" Ya ce. "Gyaran gashi mana." Girgiza kai ta yi ta ce. "Babu masu yi a garin nan." Ya ce. "Shikenan, watarana zan kai ki inda ake yi ayi miki." Cikin murna ta ce. "To Yayana na gode." Daga nan suka ɗora karatunsu daga inda suka tsaya. Kafin ya tafi ya yiwa Inna tambayar da ta dad'e tana yawo a cikin zuciyarsa. "Mama matsalar idon A'isha dashi aka haife ta ne?" Inna ta ce. "A'a, daga zazzaɓi kawai Ubangiji ya ɗoro mata, ko shekara biyu ba'a yi ba." Umar ya ce. "To me yasa baku je asibiti an duba idon ba?" Inna ta ce. "Na kai ta nan asibitin Rano suka ce sai dai mu je can Kano a duba ta, su ba su da k'wararrun likitan ido, mun gwada magungunan gida su ma ba'a dace ba." Umar ya ce. "To me yasa ba ku je can ɗin ba?" Shiru Inna ta yi ta rasa me zata ce masa. Numfashi ya sauke ya ce. "Shikenan Mama, Allah ya ba ta lafiya, bari na wuce gida." Sallama ya yi musu ya tafi. Wunin yau gaba-d'aya Umar cikin tunanin yanda zai yiwa A'isha magani ta warke yake yi, tunda ba da ciwon aka haife ta ba da yiyuwar zata warke da yardar Allah. Ya san da zai faɗawa Mahaifinsa ya nemi taimakonsa zai taimaka mata, ko da ƙasar waje ta kama akai A'isha akan ta samu lafiya zai iya kai ta, inda matsalar take baya son mahaifiyarsa ta sani, amma ya san matuƙar ya faɗawa Abbansa to sai Mom ɗinsa ta samu labari, dan Abba idan zai yi abu ba zai b'oye mata ba wai dan gudun ɓacin ranta ba. Idan kuma ya ce shi zai yiwa A'isha magani da kuɗinsa bai zama lallai kuɗaɗen dake cikin account ɗinsa su isa ba, sai dai idan Motarsa zai sayar, idan kuma ya siyar da Motar ina zai cewa Abbansa da Mom ɗinsa ya kai Motar? Haka dai ya kwana yana sak'e_sak'e shi kaɗai da neman mafita, dan babban burinsa a yanzu A'isha ta samu lafiya idanunta su buɗe.

Rayuwa ta cigaba da tafiyarwa su Inna cikin farinciki da kwanciyar hankalin da ba su taɓa riskar kansu a cikin kamar sa ba, sanadiyyar zuwan Umar cikin rayuwarsu. Umar ya zame musu wani bango da yake ba su kariya ta ko'ina a cikin rayuwarsu, dan hatta k'warzabar da mutanen gari da ƴan gidan suke yi musu sun samu sauƙin ta, domin Umar duk ya taka musu birki akan hakan. A gefe guda kuma shak'uwa mai ƙarfi tana ƙara shiga tsakanin Umar da A'isha, kodayaushe suna tare yana koya mata karatu, idan sun gama ya yi mata waƙa ko ya kunna mata kallo a wayarsa tana saurara, wani lokacin kuma ta ce ya kira mata Ma'u su yi hira da Numbern Innar Ma'u da ƙaninta ya tura musu. Da hutunsu na makaranta ya ƙare aka koma shi yake kai ta ya ɗauko ta. Wani irin wasai A'isha take jin zuciyarta a yanzu babu damuwar komai, ta samu abokin hira mai ɗebe mata kewa da nuna mata k'auna. Idan dare ya yi suka rabu da Umar Allah_Allah take gari ya waye su haɗu su ɗora daga inda suka tsaya. Umar ya ɗaukewa Inna komai tun daga kan abinci har komai na buk'atun rayuwa, duk da ita har cikin zuciyarta ba ta so hakan ba, ko dan yawon da ake yi da su a cikin gari ana sun mallake bak'o daga zuwansa garin suna ta tatse shi yana d'awainiya da su. Har nuna masa ɓacin ranta take yi akan siyayyar kayan da yake yiwa A'isha amma bai fasa ba. Bayan watanni ukun da ya ce zai yi a garin sun ƙare sai ya cewa Abbansa shukar da suka yi ba ta yi kyau ba sai sun sake wata, dan haka sai ya ƙara a ƙalla wasu watannin biyu kafin ya koma gida. Cikin rashin damuwa Abban nasa ya amince masa, Mom ɗinsa ce dai ta dinga yi masa masifa kamar zata ari baki, shi kam ya yi hakan ne saboda bai san tafiya ya bar A'isha.

Yau Litinin, da yamma ɗaya daga cikin ƴaƴan Sarki mai suna Haulatu ta dawo daga makaranta ta zauna a ɗaki ba tare da ta nemi abinci ba ta rafka tagumi da hannu bibbiyu, kallo ɗaya mahaifiyarta ta yi mata ta gane tana tattare da damuwa. Cikin kulawa ta dube ta, ta ce. "Ke lafiya kuwa kike?" Kamar Haulatu zata yi kuka ta ce. "Uwa wallahi wani abu ne yake damuna." Da mamaki Uwa ta ce mata. "Mene shi?" Ƙasa ta yi da kanta ta ce. "Uwa Umar ne idan na gaishe shi cikin rashin kulawa yake amsa mun, ba ya sakar mun fuska, ko na je gurinsa da niyyar mu yi hira sai ya haɗe mun rai, kuma ni gaskiya son shi nake yi." Uwa ta ce. "Wanne Umar kenan?" Haulatu ta ce. "Wanda yake zaune a cikin gidan nan ɗan abokin Sarki." Kama hab'a Uwa ta yi ta ce. "Kin san wa kike faɗa kuwa Haulatu? Lallai ba ki da hankali, to bari ki ji in faɗa miki, tun wuri ma ki cire shi daga cikin ranki dan ba'a ajinki ba ne shi, ato." Cikin damuwa Haulatu ta ce. "Saboda me?" Uwa ta ce. "Mahaifiyarsa! Matar nan ba ta kirki ko na sisin kwabo, mun taɓa zuwa gidanta sau ɗaya lokacin da mahaifin shi Mijin nata ya rasu, kakansu Umar ɗin kenan, Sarki ya kwashe mu muka je muka yi masa gaisuwa, yanda Matar nan ta wulaqanta mu abun ba zai faɗu ba, da muka gaishe ta daƙyar ta amsa kamar an yi mata dole, ƙarshe ma tashi ta yi ta bar mu yashe a falo sai masu aiki ne suka yi hidima da mu. Sai dai Mahaifinsa shi mutumin kirki ne, mutumin nan shi idan mutunci yana yin yawa to nasa ya yi, dan shi ba ki ga yanda ya mutunta mu ba wallahi." Haulatu ta ce. "Toh tunda Babansa yana da kirki ba shikenan ba, ni dai gaskiya Uwa ki yiwa Sarki zancen, dan shi kaɗai nake son na aura." Uwa ta ce. "Abun fa da ba zai taɓa yiyu ba ne Haulatu, idan zaki hak'ura ki hak'ura." Kuka Haulatu ta saka ta ce. "Wallahi Uwa zai yiyu, idan ya san ba za'a bar shi ya auri ƴar ƙauye ba me yasa yake kula waccan makauniyar Yarinyar, son ta fa yake yi kuma kowa a cikin garin nan ya sani." Shiru Uwa ta yi na wasu sakanni tana kallon ƴartata, tabbas abun da ta faɗa gaskiya ne, da Umar ya san ba za'a bar shi ya auri ƴar ƙauye ba da ba zai fara soyayya da A'isha ba, idan kuwa har haka ne Ƴarta ce tafi dacewa da auren ɗan gidan mai kuɗi ɗan birni ba ƴar talakawa mara asali ba. Idan Haulatu ta auri Umar za su zamo abun alfahari a garin nan, ko a cikin kishiyoyinta za ta yi musu zarra ƴarta ta auri Mijin da kaf ƴaƴansu babu wadda ta auri ko wanda ya kama ƙafarsa ne a komai da komai, dan yanda take jin Sarki yana faɗar kuɗin mahaifin Umar ba ƙaramin mai kuɗi ba ne. Wani murmushi ta saki tare da miƙewa cikin sauri ta ɗauko kuɗi a cikin jakarta Naira ɗari biyu ta bawa Haulatu ta ce. "Share hawayenki ki kwantar da hankalin ƴata, na samo mana mafita wadda nake da tabbacin zata raba Umar da waccan yarinyar cikin sauƙi, idan hakan ta kasance ke kuma na san yadda zan yi mu janyo hankalinsa gare ki." Haulatu ta ce. "Ta yaya? Me zaki yi?" Uwa ta yi murmurshi ta ce. "Ke dai je ki siyo mun katin MTN da wannan kuɗin, idan kika dawo a gabanki komai zai faru, za ki ga abun da zan yi." Ajiyar zuciya Haulatu ta sauke ta miƙe tana share hawayen fuskartata ta fice daga ɗakin...........✍️

_*Ban yi edit ba, a yi hak'uri da typing errors.*_

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*1️⃣4️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
Chapter 26 · 0% Book details