← Book details Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 55

Sashe 30

Komai Nisan Dare Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sashen Uwa ya fara shiga, tana zaune a falo tana zuba abin kayarwa zata ci Umar ya yi sallama. Cikin mamaki ta ɗago tana kallon sa tare amsa masa sallamar. Barin abun da take yi ta yi cikin faɗaɗa fara'a ta ce. "Áaa Umaru kai ne a gidan namu? Bismillah zauna akan kujera mana, ka tsaya a bakin ƙofa kamar wani baƙo. Bai ce komai ba ya zauna a ƙasa saman tabarma ya gaishe ta. Ta amsa kamar bakinta zai tsage biyu saboda fara'a ta murnar zuwan Uwar. Haulatu tana ɗaki tana shirin makaranta kamar a mafarki ta ji Uwa na ambatar sunan Umar, cikin sauri ta ƙarasa shirinta ta fito. Zuwa lokacin Uwa ta gama cika shi da surutunta da ba fahimta yake ba. Ido a waje Haulatu ta ce. "Ina kwana Umar." D'agowa ya yi ya kalle ta sau ɗaya tare da amsa mata ba yabo ba fallasa. Uwa ta dube ta, ta ce. "Had'o masa abun kari mana, kya tsaya kina kallon sa kuma." Haulatu ta yi murmurshi sannan ta ce. "Toh." Uwa ta tashi tana gyara ɗaurin zanin jikinta, gaba-d'aya ta rud'e sai wani irin murmushi take yi, shi dai kallo kawai yake bin ta da shi. Furewater ta kawo masa guda biyu ta ajiye a gabansa tare da faɗin. "Ka sha ruwa ɗana kafin ta kawo abincin." A hankali ya ce. "Alhamdulillah na gode." Uwa ta ɓata fuska ta ce. "Haba Umar kamar ba gida ba? Nan fa gidanku ne wata alkunya kuma zaka yi? kai da mai iya kawo wani ne ma ka ɗibi abu ka ba shi a gidan nan." Cikin mamakin yanda ya ga tana rawar jiki a kansa ya ce. "Na ƙoshi ne Mama shi yasa." Dai-dai nan Haulatu ta fito da kayan karin da aka ce ta haɗowa Umar a hannunta. Cigaba da magana Umar ya yi ya ce. "Dama yau zan koma gida ne shine na shigo in muku sallama." Haulatu dake tsaye ba ta san lokacin da ta saki kayan hannunta suka zube a ƙasa ba, saurin miƙewa Umar ya yi tare da ja baya yana yatsina fuska. Cikin ɗaga murya Uwa ta ce. "Tafiya kuma Umar? Kana nufin gida zaka koma?" Ya ce. "Eh Insha Allahu." Bai jira cewar su ba ya tsallake kunun gyaɗar da ya mamale a ƙasa da k'osai ya fice daga ɗakin. Haulatu da ta yi mutuwar tsaye cikin damuwa ta ce. "Na shiga uku, Uwa kina ji fa wai tafiya zai yi, to a ina zan ƙara ganin sa balle har a yi maganar Aurenmu?" Cikin karaya Uwa ta ce. "Na rasa ma bakin magana Haulatu, wannan shine ga bikin zuwa amma babu zanin d'aurawa." Zama Haulatu ta yi dab'as a ƙasa, ba ta sani ba ashe ta miƙe ƙafarta akan kunun gyaɗan dake zuba uban tiriri, da sauri ta janye ƙafarta tare da sakin ƙarar azaba, a rud'e Uwa ta yi kanta tana tambayar ta abun da ya faru.

Inna ce zaune a gaban A'isha tana kallon ta cikin takaici da kufula ta ce mata. "Wallahi A'isha zan saɓar miki, dan iskanci tunda kika tashi yau kike mun kukan banza, na tambaye ki me yake damunki kin ce ba komai, yanzu kuma na kawo miki abinci tun ɗazu kin ƙi ci." Aisha ta goge idonta ta ce. "Ki yi hak'uri zan ci." Sallamar Umar ta katsewa Inna maganar da take son yi. Cikin fara'a ta amsa masa tare da yi masa maraba sannan ta bashi gurin zama. Bayan sun gaisa ta shige ɗaki ta bar su tare da A'isha. Idanunsa a kanta ya ce. "Humairah!" Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin wani abu da ya cika mata zuciya mara daɗi yana gushewa. Kanta a ƙasa ta ce. "Na'am." Matsowa ya yi kusa da ita so closely, cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce. "Me yasa kike kuka?" Kansa ta nuna masa da hannunta ba ta ce komai ba. Ya ce. "Me na yi?" Cikin sanyin murya ta ce. "Ba jiya ne ka ƙi dawowa ba." Numfashi ya sauke cikin damuwa ya ce. "I'm sorry, wani abu ne ya tsayar da ni." Gyaɗa masa kai ta yi a hankali. Cikin rarrashi ya ce. "To ki daina kukan tunda na zo yanzu, ki ci abinci kuma ko in tashi in tafi." Da sauri ta ce. "Zan ci, amma dan Allah Ya Umar karka ƙara ƙin dawowa, ka ga bani da abokin hira sai kai, ita Inna sai dai tay ta mun faɗa." Kasa magana ya yi saboda wani irin tausayinta da ya kanainaye masa zuciya, iya jiya kaɗai da bai dawo ba ta shiga cikin damuwa ina ga ya tafi gaba-d'aya? Yaya zata ji idan ya ce mata yau zai tafi baza ta ƙara ganin shi ba? Ta ina zai fara faɗa mata wannan maganar? Cikin nutsuwa ta fara cin abincin duk da ba wani daɗinsa take ji ba, dan dai ba ta son Umar ya ƙara tafiya ya bar ta ne. Kaɗan ta ci ta ce ta ƙoshi, bai matsa mata ba akan sai ta ƙara ci ba ya ƙyale ta. Inna ta fito za ta cigaba da ayyukanta Umar ya dube ta ya ce. "Mama yau da safen nan fa zan tafi gida." Shi kansa da ya yi maganar sai da ya ji wani iri, balle kuma Inna da ta sandare a guri ɗaya cikin mamaki. A'isha kuwa ji ta yi zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske. Cikin al'ajabi Inna ta ce. "Wanne gidan? Ba dai can garinku ba?" Cikin ƙoƙarin ganin ya b'oye damuwarsa ya ce. "Can Mama." Inna ta ce. "Ikon Allah, kuma shine Umar saboda Allah sai yau ɗin zaka faɗa mana?" Ya ce. "Mama tafiyar ce ta kama ni babu shiri, kiran gaggawa aka mun a gida." Inna ta ce. "Too, in ce dai lafiya?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, akan harkar karatuna ne." Inna ta ce. "Allah Sarki, in ka tafi sai yaushe kuma?" Murmurshin yaƙe ya yi wanda ya fi kuka ciwo ya ce. "Zan dawo nan kusa Insha Allahu." Inna ta jinjina kai cikin tsananin mamakin abun ta juya ta koma ɗaki. A'isha da ta kame kamar status ta sauke numfashi ta ce. "Yaya Umar ina zaka tafi? Tafiya zaka yi ka barni?" Hannunta ya kamo ya ce. "Wa ya faɗa miki zan iya barin ki Humairah? Ina tare dake a kodayaushe." Ta k'wace hannunta cikin damuwa ta ce. "Gashi nan kacewa Inna zaka tafi gida yau." Ta fara hawaye ta ce. "Dan Allah Yaya Umar karka tafi ka barni, ka ga kai kaɗai ne abokina, idan ka tafi da wa zan dinga hira da karatu?" Runtse idonsa ya yi yana jin yanda zuciyarsa ke yi masa suya, ba zai iya jurarar ganin ta cikin damuwa ba, dan haka ya ce. "Shikenan na fasa tafiyar." Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta shiga share hawayen fuskarta, baiwar Allah, har cikin zuciyarta ta yarda ya fasa tafiyar. Haɗe_haɗen su Daddawa da kuka da lalle Inna ta haɗawa Umar cikin wani ƙaramin buhu a matsayin tsaraba ta fito masa dashi tsakar gida. Yana zaune suna hira da A'isha har 11 ta wuce, kasantuwar su tare sai ya sanyaya masa zuciya ya mantar da shi damuwar da yake ciki. Suna cikin hirar aka kira shi a waya, d'agawa ya yi ya ji muryar Ado driver, bayan sun gaisa ya sanar masa ya ƙaraso cikin garin Kumurya yana ƙofar gidan Sarki. Wata irin bugawa ya ji zuciyarsa ta yi, lokaci ɗaya ya ji mood ɗinsa ya sauya, shikenan dagaske dai tafiya zai yi ya bar A'ishansa. Ba tare da ya bari ta gane halin da yake ciki ba ya miƙe ya fita bayan ya ce mata yana zuwa zai je ya dawo...........✍️

_*Ku yi hak'uri da wannan ina cikin sha'anin biki ne, ko editing ban yi ba*_

*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*

_By_
_Zeey Kumurya_

*ELEGANT ONLINE WRITER'S*

*1️⃣6️⃣*

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
Chapter 30 · 0% Book details